Page 12

244 20 0
                                    

KOWA YA GA ZABUWA...
   (DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

                      *PAGE 12*

*FREE BOOK*

*Afuwan Na ji na shiru da kuka yi jiya🙏*

Cikin tsananin tsoro da fargaban abunda ze iya faruwa da su ta fara ambaton Allah..
"Allah gani gareka ya Allah, da kai na dogara Allah kuma a gareka kaɗai nake bukatar taimako, ya Allah ka karemu da zuri'a ta ya Allah....."

Kaman daga sama suka hango mota na zuwa da mugun speed, gabanshi ta shiga ba tare ma da ta sani ba, wani wawan birki aka taka a daidai lokacin mutanen suka iso su.

Zaune yake yana ƙarewa situation ɗin kallo cikin son fahimtan abunda ke faruwa, abu irin haka baya gaggawa sbd yanayin shi na famous mutum celebrity, ana iya tricking ɗinshi cikin sauƙi Dukda babu mahalukin da ya san ma yana Nigeria banda yaranshi se wanchan tsohuwar da ta sashi zuwa, tuna haka kaɗai ƙona mai rai yake.

"Dan Allah karku cutar damu babu abunda muka muku!"

Hidayat ta faɗi tana Haɗa hannunta wuri guda cikin roko.

"Muma don Allah kiyi hakuri babu yadda kika iya hanyar samun mu kenan!"
Ɗayan ya faɗa.

Kara kankame Aisha hidayat tayi a hannunta tana girgiza kai tana cewa..
"Ba zan taɓa Bari ku taɓamin yarinya ba, ba zan bari ba sede in kasheni Zaku yi ku ɗauke ta.."

"Hakan ma se ayi ai! Abunda muka sani yau se mun ɗauki yarinyar nan!"

Buɗe kofar motan akayi wadda duk ya saka su maida hankali kai, Seda ya shafe seconds kan ya sako kafafunshi ƙasa ya sauko cikin wani salo na burgewa.

Sanye yake da track suit riga da wando na Fendi me tsananin taushi da tsada, dark Ash ya saka hulan a kanshi yadda ya rufe giranshi da rabin idanunshi hancinshi sanye da facemask as usual cikin dakakkiyar muryarnan tashi yace

"Says who?"

Duk Kallonshi suke kan na farko yace
"kaman ya says who? Mu muka ce haka kuma dole mu ɗauke ta malam ka kama gabanka ba ruwanka... Baba kamo ta mu wuce.."

Hannu wadda aka kira da baban ya miƙa da nufin kamota se Charab yaji an riƙe hannun, wani wawan juyi yayi ya murɗe hannun tare da sauke mishi naushi da kafa ɗaya a fuska, ihu ya kwala yana zubewa sauran suka yo kanshi laga laga yayi musu su huɗu kan suka mike suka gudu.

Duk wannan dukan da ya musu ko hulan kanshi be faɗi ba bare Hidayat da ta kara rukunkume Aisha ta ga fuskanshi, hakanan yana dukan ne kaman irin wadda baya so hannunshi yayi datti ɗinnan.

Hannaye yasa a aljihu ya tsaya yana Kallonsu, so yake yayi magana sede ranshi a ɓace yake da abubuwa dayawa, tsaki me karfi ya ja ganin Hidayat ta fara jan Aisha zasu tafi a tsakar daren nan.

"Shiga mota!"
Ya faɗi maganan cikin dakakkiyar muryar salon bada umarni.

Chakk hidayat ta tsaya gabanta na dukan tara tara muryarshi kaɗai ya haifar mata da wani kalar faɗuwar gaba bare umarnin da ya Bayar, shi kuma da wanne ya zo?

Watsar dashi tayi ta sake jan Aisha tana jijjiga Junior da yake ta kuka.
"I said enter the damn fucking carrr!!"

Kawai se ta fashe da kuka me karfi saboda tsoratar da tayi hakan yasa Aisha ma fara sabon kuka.

KOWA YA GA ZABUWA...Where stories live. Discover now