Page 24

289 29 4
                                    

KOWA YA GA ZABUWA...
(DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

*PAGE 24*

*FREE BOOK*

**Readers! Wai kuwa kun san magic ɗin dake cikin comment? Bari in baku wani takaitaccen labari, na tashi yau da ciwon kunne wadda rabona da in taɓa wayana ma tun 8am, se da karfe bakwai na dare ya buga nace bari in ɗan leka online tunda kunnena yayi sauƙi wallahi ban da niyyar typing yau, but to my biggest surprise se in na shiga nan in ga doguwar muhawara, in na shiga chan in kalli ruwan comments nace kai I cannot disappoint u guys dole in daure in baku page...! Wannan page ɗin naku ne masoya littafin kowa ya ga zabuwa😍🥰 one love**

Shanyayyun idanunsa masu cike da kwarjini irin na cikakkun maza ya zuba mata na ƴan sakanni.
Se a sannan kuma ta fahimci irin katoɓarar da ta zabga sede Hausawa na cewa Magana zarar bunu... Kasa Kallonshi tayi tana jin yadda idanunshi ke ladabtar da ita yadda ya kamata.

A maimakon karatun Tsam ya miƙe ya fice daga wurin cikin salon takunshi, da kallo ta bi bayanshi har ya maida kofar ɗakin shi ya rufe..

A zabure ta mike tsaye ta koma tsakar parlorn tana zirga zirga, damuwa ta hango shimfiɗe a fuskanshi wadda ita a nata Tunanin damuwar ya ta'allaka ne da barin rayuwarsu da zata yi bayan sun fara sabawa da ita especially yaranshi, gabaɗaya ta rasa Tunanin da zata yi, da gaske tana jin hamza a zuciyarta kuma tana jin zata iya aurenshi.. Tana kuma son auren nashi ne ko ze samu natsuwa wurin fuskantar rayuwa guda ya dena raba hankalinshi saboda soyayyar ta.

Sede ita kanta in ta ɗaura Tunanin ya su Norah zasu yi se taji wani tashin hankali ya lallaɓo ya rufeta, kenan abunda ta fara ze zama a banza?
Alkawarinta da Daadida ze zama ta karya shi kenan?

Shi kuwa a nashi ɓangaren yana shiga ya zube bisa gado rigingine, da sauri sauri yake fitar da numfashi, ambaton Allah yayi tayi har ya soma jin zafin da zuciyarsa ke masa na raguwa,gabaɗaya iharin jikinsa ya mutu murus... Har abada baza'a taɓa jifan shi da kalamin da ya mishi zafi irin wannan ba kuma wadda ya rasa dalilin jin zafinta haka.

A iya tunaninshi bashi da wani businesses da ita banda kula da yaranshi se a yanzu da ta zaɓi gyara rayuwarsu da taimakon ubangiji zuwa hanya madaidaiciya, amma Sam be gane ba kuma girma da matsayin da wani sashe na zuciyarshi kuma ya bata ba.

Har lokacin magrib yana nan kwance a wurin kaman wadda aka sassara mishi gaɓoɓi, da sunan Allah ya miqe ya shiga toilet yayi alwala ya fito fuskanshi a dinke tsab, parlorn ya fita cikin I don't care manner ɗinshi na asali, duk sun yi alwala suna shirin sallah, ba tare da ya kalleta ba yayi gaba ya tada musu sallar.

Itama sau ɗaya ta kalli fuskanshi da ya koma mata sak na ranar da suka fara haɗuwa, bayan sun idar da sallah ya buɗe Alqur'ani ya cigaba da muraja'ar na baya.

Toh fah tun tana ɗaukan abun wasa se taga ya ɗau zafi sossai da ita kaman wacce aka ce ta zage shi ko wani abu, se kuma hakan ya sakata a damuwa rayuwarshi bata gama saituwar da tayi alkawari ba, har Hamza ya koma be sake gane mata ba.

Ranar da ya koma ba karamin daru suka kwasa da zainab ba wadda har ta kaisu gaban mahaifiyarshi dake goggo a gareta.

"Hamza Abunda zainab ta faɗa haka ne?" Ta faɗa tana Kallonshi.

"Eh hajiya, amma don Allah ki fahimce ni ba wai don cutar da zainab nake son shigo da Hidayat rayuwata ba, son ta ya samo asali ne daga tausayinta in bazaki manta ba a shekaru da dama su Abba ƙarami sun je nema min aurenta har sau uku a wurin marikinta.." Ya faɗa yana kallon Hajiyar cikin son tunatar da ita hidayat.

KOWA YA GA ZABUWA...Where stories live. Discover now