Page 47

467 21 4
                                    

KOWA YA GA ZABUWA...
   (DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

FOLLOW ME ON Wattpad @Gureenjoh6763

AND ON AREWA BOOKS @gureenjo

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

                      *PAGE 47*
LAST PAGE

*FREE BOOK*

"yarinyar nan wai har tayi girman fooling ɗina, ce min fa tayi zata get together ta kuma fita da decent dressing amma yanzu ji dress dake jikinta? Ya Subhanallah"

A sanyaye yace
"calm down die hard baki gani gabaɗaya hankalinta ya tashi? She's just a teenager for goodness sake"

Norah ɗin ya riƙe yana goge mata bakin nata, duk fuskanshi ya bayyana damuwa, Kallonsu ta tsaya yi kerere lallai Raed be ɗauko hanyar tarbiyatar da yaranshi ba, Juyawa kawai tayi ta koma mota ta zauna da kallo ya bita har ta rufo kofar kan ya kamo hannun Norah ya sanyata bayan mota shima ya shiga ya ja suka bar wurin.

Har suka yi nisa babu wadda ya iya magana, chan ya dube ta ganin yadda take fushi ita kaɗai..

"Baby gurl please you need to calm down, ba wani abu me muni kika samu yarinyar nan tana yi ba..."

Katse shi tayi
"ba abu me muni ba ka ce? OK shikenan! Nunamin kawai zaka yi ƴar ka ce baka so in hukunta ta bayan ka san laifin da ta aikata babba ne, taya zata yi irin wannan rayuwa tana ƴar musulma?"

"Ya Subhanallah! Hidayah me ya kawo wannan magana?"

Shiru tayi bata ce komai ba har suka isa gida, duk ta riga su fita ta haura ta shige ɗakinta, ko da suka hauro da Norah kuka take yi

"am sorry dad na Haɗa ku faɗa da mommy I had no idea night club zasu ja ni naje, wlh I dressed like this saboda zuginsu ban taɓa ba, ka tayani ba mommy hakuri duk su suka faɗa min abunda zan faɗa mata ta barni na fita ba zan ƙara ba"

Zaunar da ita yayi shima ya zauna yace
"kin san mommynku is my first cousin sis ko?"
Kai ta gyaɗa ya ce
"yau ko bani da rai she have all the right da zata zauna daku ta hukuntaku idan kun yi ba dae dae ba, sannan karya bashi da kyau kin yi ƙarya saboda ki aikata saɓo in kin mutu me zaki cewa Allah?"

Kuka take yi ta sake cewa
"am sorry"

Yace
"Yafiyar Allah zaki nema sannan ki ba mommynku hakuri idan ta huce, Thank God we are leaving France 2morrow, je ki cire kayan nan ki kwanta ok?"

Kai ta gyaɗa ta miƙe ta nufi ɗakinta, ɗakin hidayat ya kurawa idanu yana nazarin ɓacin ranta a saninshi tana da sanyin hali da ko laifi aka mata cikin natsuwa take hukunci, amma kuma kwarai be ji daaɗin kalmarta na wai ze nuna mata Norah ba ƴarta bace, mikewa shima yayi ya nufi ɗakin shi, tun da ta tare gidanshi basu taɓa raba wurin kwanciya ba se ranar.

Babu wadda yayi baccin kirki a ranar asuba farko ta fita ta fara Haɗa musu break, bayan ta gama ta bi su ta tashesu suka fara yin sallah kan suka yi wanka suka hau shiri, Farrah ta aika ta tada Norah ta dawo, har gari ya ɗan yi shaa kan suka fito suka karya, ko da ya zauna a dining ma
"Good morning"
Kawai tace tare da saka mishi abinci ta tura mishi, kaɗan ya ci ya koma parlor da suka bar komai an dae rufe da Fararen kyalle, suna gamawa suma Paul ya gama fitar da akwatunasu suka bar gidan zuwa Airport anan suka samu Rashida suka yi sallama, har suka sauka Riyadh Motoci kusan biyar suka taryesu babu wadda ya cewa wani komai se yaran ke ta hayaniyar su.

KOWA YA GA ZABUWA...Where stories live. Discover now