Wacece Ni?

1.4K 62 4
                                    

Wacece Ni
Part 1/01

Bissimallah

Gudu kawai take zabgawa bata ko waiwayen bayanta rike take da wata jaririya a hannunta wacce baxata wuce kwana daya ba da haihuwanta saboda babu Kaya ajikinta sai dai lullube take da wani towel...Bata tsaya da gudun ba har sai da tayi gudun kimanin kilometer tari da hamsin-kusan awa biyu da dori tayi tana gudu a cikin dajin da baxata iya cewa ga garin da take ba ko ga kyauyan da take...kallo daya xakai Mata ka hango gajiyan da tayi.

A wani katon kogi ta tsaya Wanda ruwa ne ke tafiya ba tsayawa, ayayin da ta ijiye jaririyar gefe guda wacce sai faman raftaka ihu take yi..Alamar gajiya da Kuma yunwa........Tsaki matar tayi tare da kallon jaririyar hade da daure fuska

Tace kwanan ki ya kare ja'irah....bayan matar ta wanke kafarta ta dau mayafinta ta yafa, sannan ta dau jaririyar da niyan jefata cikin kogin nan Mai tafiya
Ta durkusa ta ijiye jaririyar acikin ruwan Nan da Nan ruwa ya fara Jan jaririyar ahankali tana tsala ihu ruwa yana ta tafiya da ita wacce tuni har ta fara lumewa.......But unfortunately matar ta xo tashi kenan bayan ta gama Dariyar mugunta taji kafar ta, ta xame Ina ai Bata Ankara ba tuni ta fada cikin kogin tana ihu tana neman dauki.....da ikon Allah itama ta lume a cikin ruwan ba jiririya ba matar......
Haka ruwa ya tafi dasu.

....................

15years later

Yara ne yan mata kana na wanda akalla ba akasri ba zasu Kai ahekaru goma da dori, zaune a gaban Yusuf Dan tsoho Memorial hospital Wanda aka fi sani da Asibitin Dutse babban asibiti ne Wanda yayi fice acikin jahar kaduna.....

Da alamu talla sukeyi ko wacce da robarta a kusa da ita...wasu suna hira, wasu suna wasa agefe, wasu sun natsu, wasu Kuma sun bar kayan tallan sun tafi yawon iskan cinsu, sai subar kana nan su tsare masu har su dawo......

Wata mota ce kirar Prado fara gal sabuwa ta fito daga cikin asibitin kaitsaye yasha kwana zai wuce, kaman ance ya waiga
Yana waigawa ya hango wata yarinya akalla xatayi ahekara goma tsaye gaban wani saurayi tana kuka, duban shi yakai ga bokitin tallan ta yaga ya xube a kasa komai na ciki ya xube.....
Tsaki yayi ya fada aransa.....haka iyayenku suke sa yaruwarku ta kaskanta a banxa da wofi.....ya wuce abinshi batare da tsayawa ba.

Yarinyar Kam kuka take tana cewa ka yi hakuri ka biyani kudina...ai da gangan ka barar min da kayana..yanxu me kake so nace wa Inna....nashiga uku wlhy yau nasan Mai raba Ni da ita sai Allah

Hararata yayi sannan yace kasa kasa idan kina so na baki kudin ki to ki biyoni yanxu muje .....babu Wanda xai San inda xamu

Allah ya tsare ni..Ni in bika Tab Wlhy na gwammace na koma Inna ta kashe ni dako in bika

Tsayawa yayi Yana kallon yarinyar Mai wayon tsiya kullun yakan so yai Mata wayau tun Bata Kai Haka girma ba.......Samari da yawa awajan suna shakkar ta saboda halinta ba daya yake da sauran yan matan wajan ba , yayi yayi ta biyo shi Amma sbd wayonta ya kasa cimma burinshi....

Yace yarinya arxiki na kiranki kina gudu ko

Eh din na gudu din....Kuma Allah ya tsare ni da fadawa tarkon irinku.

Ke ni kike ce ma haka?

Eh din na fada...Tai mashi tsiwa hade da murguda Masa baki

Bige bakin yayi yace ki saurari sakamako yarinya

Babu abinda ka Isa kamin eheeee...ta fada tana kwashe kayanta...tace ma sauran Yan matan ta tafi gida

****Boddo *****
Haka xaki wajan Inna batareda samun cikon kudinta ba cewar Dije yar makwabciyar su Boddo.

Yaxanyi Dije kinsan babu kyau xubar da mutunci....mu mata ne Kuma rayuwar mu tana da rauni Dije tun bamu da wayo muke talle....Munsan halayen mazan wajannan dayawansu Almajirai ne wasu Kuma kani kawa ne masu saida man fetur da sauransu ......dole muyi taka tsantsan da rayuwar mu......Dije gaskia na gwammace inje wajn Inna ahaka sai dai in kashe ni xatayi ta kashe Ni ..
Murmushi Dije tayi tace Nasan goggo idan nace Mata kudi na sun bata, batayi min komai...don Haka ga kudina ki Kai wa Inna kawai...muje ma in raka ki nima na tashi tallar.

Bude Baki Boddo tayi hawaye na xuba a idanuwanta tace Dije kullun ke kike Tai makona....agurin Inna ta hanyar bani kudin ki....ta Sha majina Alamar shasshekar kuka tace Nima Allah yasa watarana in saka maki da taimakon da kike min.

Kada ki damu Boddo Ni dake ai mun xama daya babu mejin kanmu yi Shuru kinji tana lallashinta.

Wata katuwar mota suka tsayar wacce Yan kaduna ko ince masu hawanta a kaduna sukan ce mata Ganjal ko transporter.....baya suka hau abinsu..... mostly Idan motar ta taho daga bakin dogo hayin-rigasa ta nufa haka xalika daga hayi Kuma bakin dogo ta nufa.

Hira suke suna dariya cen Dije tace akwai Makera

Tsaya wa akayi daidai kan layin makera suka biya kudinsu sannan suka wuce....Basu dade da fara tafiya ba Suka ji an Kira Boddo
Waigawa tayi taga Babanta ne yana tsaye rike da kekenshi...yaki
Ya kirawo su

Murmushi tayi tace lah Baba suka ruga a guje suka ce baba Ina yini

Lafia Lau Boddo, Dije har kun dawo
Eh Baba

Yace ga wannan maxa kije gida nasan Bata aje maki abinci ba...idan kinje karki Bari ta gani sai kici kinji ko Yar Babanta

To baba nagode Allah ya tsare,Allah ya dawo dakai lafia

Ameen Ameen Boddo
Maxa ku tafi gida
Toh suka wuce abinsu.

To be continue
✍️
Inshallah
🙏

*************

Keep calm fans 😊 the journey just begin ✍️😜

Comment are always welcome

DielaIbrahim
Pls 🙏 share .

WACECE NI ✔Where stories live. Discover now