Chapter 13

260 30 0
                                    

Wacece Ni?
Story written by
DielaIbrahim ✍️

Part 1/13

_____________________________Abuja
________ Maitama


Muna Nan zaune muna zaman jiran Hajiya kamar yadda naji Yar Aiken nan ta fada

Tsahon dakika Goma Sha biyar
Sai ga wata dattijuwar tsohuwa
Sanye cikin Shiga ta Alfarma
A kiyatsance xaka kiyasta shekarunta bisa hamsin da dori
Amma a zahiri takai saba'in
Kyan jikinta, hutun da take samu kadai ya wadatar

Aka katse min tunani na da cewa
Ina yini Hajiya
Talatu ke gaishe da matar
Nan muma muka gaishe ta

Ba shakka ta amsa ba yabo ba fallasa dauke da fara'a a fuskanta

Adaidai lokacin Kuma Wata Mata ta fito
Baxaka sata a fannin farare ba Kuma baxaka azata a fannin bakake ba
Tana da kyanta MashaAllah
Wacce ta xo Aika ita ce a bayanta
Da alamu itace mummy qarama
Ta nemi waje ta zauna nesa da ita Hajiyar
Cen ta numfasa dacewa Hajiya
Kin ce akawo maki Mai Taya ki Hira da wasu kana Nan aikace aikace
Yanxu karo na Hudu kenan Ina kawowa kina cewa basuyi maki ba.....to ga wannan sabbin ki zaba acikinsu

Hajiya ta yamutsa fuska
Ta kallo mu
Nidai Boddo kaina na qasa Ina wasa da yatsun hannuna
Cen muka ji tace
Waccen ta tsakiyan

Abinda ta iya furtawa kenan sai Kuma tayi Shuru
Kallo ya koma kaina wacce Ni nama manta da cewa Ni Boddo Nina zauna a tsakiyansu
Talatu dake gefe na tayi Hamdala
Lallai Boddo kin Taki sa'a xaki kwashi gara a gidannan ki godewa Allah cewar Daya daga cikin Yan matan da muka xo dasu
Nikam ban gane me suke nufi ba
Sai ji nayi Mummy qarama nacewa
Talatu mine sunan ta

Boddo ta Bata amsa
To yaudai Hajiya ta xabi Yar aiki
Yanxu xaki barta anan
Bari naje na dauko maki kudinki
Inyaso karshen wata Kya dawo ki amshi wani
Toh toh Hajiya godiya nake

Tashi tayi ta fita
Jim kadan ta Aiko aka kawo wa Talatu kudin

Tashi nayi na bisu abaya  Basu Ankara ba sai jin takun tafiya na sukayi dayar yarinyar tace lah ji Wai ta biyo mu Kuma

Talatu ta saki wani salati tare da tafa hannuwa ai Boddo shikenan nan Zaki ta zama Kuma kina musu bauta ana turawa Inna kudin aikinki sai dai kiyi hakuri ki koma kinji

Kuka na saki Ina cewa yanxu Bari na xasuyi awannan gidan Yan yankan Kan
Haka sukai ta lallashin na na koma na zauna a inda muka zauna da farko
Shuru falon babu kowa saboda ita Hajiya ta Dade da barin parlon

Ina Nan zaune dai tsahon minti Talatin can Naga fitowar wata Mata xatakai shekaru Daya da dayar matan da mummy qarama ta Aiko daxu

Tace min Yar Nan tun daxo Hajiya ke nemanki Ashe kina Nan taho kinjiko
Innuna maki dakin da Zaki zauna
Ba musu ma tashi nabi bayanta
Ta cikin parlon muka kutsa muka dinga tafiya muna zuwa wani babban corridor inda Naga kofofi ta kowani bangare
Kafin muka Shiga want kofa cen ta karshen ginin part din
Daki ne madaidaici
Akwai gado wardrobe,bedside Kai harda dressing mirror da abin saka takalmi ga carpet a tsakiyan dakin da Kuma dust bin da abin say kayan wanki

Nace dakin Hajiya nee ?gyara wa za'ayi Koh? Na tambaya

Dariya matar tayi tace zauna yarinya
Na zauna
Tace naso ace sai gobe xan fara maki bayanin komai na part din Hajiya kafin muxo ga gidan gabadaya
Amma yau xan fara don na cire ki a duhu
Ta karasa tana murmushi

Yarinya mine sunan ki

Nace Boddo
Tace asali fah
Nace Boddo
Tohhh Boddo barkanki da shigowa wannan gida Ina fatan zakiyi aiki tsakaninki da Allah

Ahankali nace Mata inshallah xanyi Mama

Kallo na tayi Jin na kirata da Mama
Tace shekara na goma Sha Takwas a gidan Amma babu yaran da ya taba kirana da Mama
Koda masu aiki aka kawo part dinnan Haka xasu gama har su tafi Basu mutuntani
Sai mutun Daya
Shine da na Uku Kuma Babba yanxu a Duk cikin fadin gidannan
Shi kadai yake kirana da Mama
Sauran yayan kuwa sai dai su kirani da sunana gatsau Duk da Suma suna da tarbiya daidai gwargwado
Hakan yasa Yan aiki Basu gani na da mutun ci Hajiya kadai ke tsawatar masu idan taga suna ci mun fuska

Nidai Ina jinta bance Mata komai ba

Ta cigaba da cewa
Boddo Nan shine part din Hajiya
Hajiya mahaifiyar Mai gidan nanne wato mijin Hajiya qarama
Tace
Boddo idan kina so zaman gidannan yai maki dadi to karki kula kowa, na haneki da gulma
Kiyi harkarki
Babu ruwanki da Shiga harkan wani
sannan Aikinki a gidannan ko ince part din Nan kadai
Shine Zaki gyarawa Hajiya daki kullin ki share ki wanke bayi
Sannan ki xama Mai tsabta don Hajiya nason mace Mai tsabta

Idan kika gama wannan
Akwai wasu lokuta da take xuwa garden shakatawa xaki rakata Kuma ki dinga yimata Hira Mai dadi
Xaki kasance a kusa da itane ko da yaushe saboda idan tana bukatar wani Abu ki Mata cikin gaggawa don Bata son nawa
Yanxu xaku Bata idan taga kina nawa ko kina wasa
Babu ruwanki da Shiga kitchen you wanke wanke akwai masu Ni nake dafawa Hajiya abince sanann akwai masu wanke wanke da sharan falon waje
Ina fatan kin gane

Na gyada Kai Alamar eh

Sannan nan dakin ba dakin Hajiya bane Nan shine hurumin ki nida ke a Duk fadin gidannan
Anan xaki rinka kwana
Nima anan nake kwana

Bakomai yasa aka bamu wannan dakin ba sai don munfi kusa da Hajiya babu wani Mai aiki da ake Bari ya shigo Nan ciki inda kika bi sai Ni sai Kuma ke yanxu
Don Haka ki kula sosai

Gyada Kai na kumayi kamar wata kadangaruwa

Sannan ta fita tabar Ni nikadai
Ina tunani.

😃😃😃
Love y'all

...............

DielaIbrahim ✍️
Vote/Share please

WACECE NI ✔Where stories live. Discover now