Chapter 15

272 29 1
                                    

Wacece Ni?

Part 2/15

_________________________________
General hospital ,Suleja

Back to where I stop....am so sorry for not posting 2days....... Please bear with me.

Nabil ya kai dubanshi ga Boddo wacce gaba daya hankalinta baya wajan.....dafa goshinsa yayi,tuni dabara ta fado masa....sa kafa yayi ya tokari kafarta.......a razane ta dago kai tana kallonshi, Nabil ya daure fuska kaman bai taba dariya ba hade da kuma juya kai gefe batareda kallon inda take ba,
ya ce ga Kaya nan kiyi anfani dasu kafin ayi discharging dinki.

Gyada kai nayi kaman wata doluwa baki bude Ina mamakin wai ya siya min kaya......kaman kuwa yasan ina bukatar kayan don danayi wanka ma ban iya maimaita inner wear na ba saboda tsabar wari danaji sunayi
Kwanansu takwas a jiki na......Rigar Jikina kawai na Sanya babu hijab sai wani mayafi 
Don dama  ranar da abin ya faru mutanen sun kwace min hijab dina sai ya rage gyalen Shima don na daura akaina ne na tsira dashi......daga kaina na Kuma yi Naga Yana niyan tafiya....nai saurin cewa Thank you  da karfi
"Tsayawa yayi  yadan jiyo kadan yana kallon ta, so tari Nabil yakanji muryar Boddo tai mashi kama dana yarinyar dayake nema.......ya kan tuna ranan da taimasa kwatancen bank a kaduna da Kuma randa ya ganta a appartment din Ummie idan tana magana yakanji kaman muryar yarinyar amma...shi ya kasa tunano yanayin fuskar yarinyar yadai san chocolate color ce ita .....Juyawa yai yayi tafiyarsa.

Tashi nayi na kewaye dan karfe mai cotton da yake jikin gado na na bude ledar don daukar kayan dukda nasan babu inners hakannan zan sanya kayan ai ba wanda zai gane....Ina wannan tunanin ina ta faman ciro kaya wanda to my surprise nazo kan pant da bra mamaki ya hanani karasa ciro sauran kayan na tashi na waiga da sauri ko akwai mai kallo na, Naga babu kowa, na juya Ina kallon kayan, taya Nabil zai fara tunanin siya min wannan kayan,ko kunya na ma baiji ba.....ohhh na tsura ma bra din ido  tabe baki nayi na dau daya na sanya cib yamin what how comes yasan size dina.....cikin sauri na gama shirin na maida sauran kayan na kulle na tura kasan gado..na koma na kwanta Ina tunanin wani Hali Aamir yake ciki.

Two Days later
8:30am

Ina zaune na gama shiryawa nurse  ta shigo ta mika min leda tana cewa patient dina gashi inji oga nabil kici kafin na baki injections Koh

Na ansa Ina murmushi nace toh nagode.
Bayan na gama ne nurse ta dawo yimin allura.......har ta fara hada kayan alluran na kalleta Ina tunanin dabarar dazanyi yau, kullin haka nake bata mata lokaci sai tayi dagaske take iya min allura
Nace Mata:
amma pls da anbar injections dinnan naji sauki fah baki gani ba...Kuma doctor dayazo dazu ma yace naji sauqi an kusa discharging dina, na karashe fada ina motsa eye brows dina

Kallo na tayi ta gefen Ido tayi smiling sannan ta maimaita abinda nace cikin keta, Boddo kenan inda sabo ai na saba.......alluran nan da kike gani tun da muka fara sai mun gama bi'iznillah kaman yadda doctor ya rubuta, don haka daurewa zakiyi ki juya nai maki pls karki bata min lokaci yau.....

Hakanan na juya Ina rufe Ido Ina matse wa, Ina turo baki  har ta gama min na gyara zama Ina tura baki, daga kaina dazanyi na hango Nabil nesa damu kadan yana nufo inda muke rungume yake da hannun sa........thank goodness angama min alluran tana cemin sai anjima nayi banza da ita ko kallan ta banyi ba....

Nabil na kalla wanda ya tsareni da kyawawan idanuwansa Ina kwana na furta Ina mai tura baki

Baka isa ka sheda cewa ya amsa min ba sai dai bakinsa daya dan motsa kadan... tissue ya mika min sannan ya ce hawaye a idanunki.,....Aikuwa Ina taba wa naji hawayen ba shiri kunya ta kamani yanzu zaice da girmana Ina kukan allura na ansa na sunkuyar dakai Ina gogewa ahankali........
tsahon minti goma yana tsaye bazan iya cewa danna waya yake ba Kuma bazan iya cewa kallo na yakeyi ba, daga bisani yace dani......    Aamir ya farfado, and gobe za'a kaishi gida, idan kina son ganinsa ki biyo ni yanzu.....Yana kaiwa Nan  yayi hanyar fita.

WACECE NI ✔Where stories live. Discover now