Chapter 5

229 28 8
                                    

Wacece Ni?

Part 3/5

_______________________________

Kai tsaye Maitama na nufa
Ina Shiga ban je ko Ina ba ,bangaren Nabil  nayi Amma ban kai ga Shiga ba, naji an janyo ni da hannu daga kan dazanyi naga Lailah.

Lailah tace Boddo ke wacce irin yarinya ce mara aji mara zuciya.....wato dole sai kin Shiga gona ta ko....na Miki kashedi tun ba yau ba amma kin kasa ganewa, Ina mai umartarki da karki saki auran nan ya tabbata akanki domin Zaki fuskanci kalubale babba acikin sa.......  Last warning din dazan baki kenan......ta sake min hannu gami da tura ni na kusan faduwa, haka ta tafi ko a jikin ta.

Na tsura mata ido har saida ta kure wa gani na,na kauda kaina na Shiga dakin.....bansamu kowa a falon ba ina ta sallama Shuru babu kowa, direct dakin baccinsa na nufa nanma dai Shuru babu kowa har ban daki na duba babu kowa na zauna saman gadon sa Ina share zufa.....Ina tunanin Lailah,...... hannuna na kai zan dauki pillow sai naji na bige wani abu.

*Na waiga don ganin me na bige, wani  ring box ne mai kyau, na dauka zan bude kenan idona yakai ga wani hardcover mai masifar kyau da tsari na ajiye ring din na dauki hardcover danaga an rubuta Dairy.......
Na fara budewa nidai kwalliyar diary din ya tafi da imani na....haka nake ta budewa Kaman wani karamin jaka na Mata, harda wajan sakala pen da wajan sa IDcard da sauransu.

Ina budewa asaman dairy din naga an rubuta date,sai naji Ina son karanta littafin, Ina son Jin meya faru a rayuwar Yaya Nabil.

*************************

Nikam kingani mummy wlhy na gaji....na gaji tun yaushe kike cewa zaki kwato min abinda zuciyata take so amma me haryanzu mummy kin kasa yin komai akai tsahon kwanakinnan, ki duba fah kigani mummy har bikin ya matso.......

OMG Lailah meyasa kike da naci ne, tunda nace maki ki kwantar da hankalinki ai sai kiyi Shuru kiga abinda zai faru Koh.......Haba my Lailah kinsan farin cikin ki shine nawa...don haka dole ne na miki abinda zai faranta maki rai.......so ki Kara hakuri kinji daughter, tana magana tana bubbuga mata baya alamar lallashi.

Okay mummy I trust you, nasan zakiyi komai saboda farin ciki na.I love you mummy.

I love you too darling....oyaaa yanzu ki tashi kije ki kwanta ki huta and ki cire damuwa aranki kinji daughter.

Toh mummy bye.

Bye.

Bayan tafiyan Lailah.....mummy ta kira kawar ta awaya take zayyana mata yanda sukayi da Lailah.....azahiri mummy bata son Lailah da Hamid saboda bashida wani kudin azo agani.....burinta yar'ta ta auri dan shugaban kasa ko wani hamshakin, Amma Lailah ta kafe akan wani Hamid.......Mummy tace da kawarta kina jina Ina so kisa ai min aiki mai sunan aiki wanda zaisa Lailah ta dena son Yaronnan......so nake ayi auran nan da wannan matsiyaciyar yarinyar don ta tafi tabar mana zu'ri'ar mu .......yarinya kwata kwata ta sanya babu wanda yake ganin yara na da mutunci ayanzu, komai aka samu ita.....dama cen Ina neman yanda zanyi da ita, yanzu kam Kinga dama ta zo min don haka dole auran nan ya tabbata akanta. Ita Kuma Lailah kimin yadda nace maki kawai....yauwa toh sai naji kiranki.

Ta kashe wayar tana karkada kafa ta daura daya kan daya......don bazata cimma burinta agidan ba sai Boddo tabar family din.

**************

Baffah ne da Abokinsa da Kuma Nabil suke magana akan auran Nabil, Wanda Nabil ya bukaci dasu dakata har sai an gama bikin Boddo tukunna......Baffah yaso ahada bikin ne amma abikinsa baban yarinyar yace ayi  wa Nabil uzuri.

Nabil yaji dadi sosai dasuka amince da bukatar shi, yana sa ran kafin lokacin ya samo abar kaunar shi, yai wa su Baffah sallama ya tafi wajan Hamid, Hamid ne keta faman kiranshi awaya da akwai wani shirye shirye dasukeyi basu karasa ba, yanzu basu cika wuni a gida ba sai tsakar dare suke dawowa.

***************

Page na farko naga an rubuta
Unknown, sannan date ya biyo baya akasa kafin naga an rubuta "Ranar da na fara ganin ta."

Atsanake nafara karatun Diary din wanda tunda ga page din farko nafara Jin zuciyata tana bugawa domin kuwa labarin sosai yaimin kaman dani ake, gani nake kaman agabana abubuwan duk suka faru....Amma na kasa tantance ko Ni din ce, ko ba ni bace,.....haka na cigaba da karantawa ban sare ba sai da nazo inda nayi accident wanda Yaya Nabil Ashe shi yaimin treatment na farfado, Amma washegari kawai nabar asibitin batareda ya kuma gani na ba, still Naga inda wasu samari suka so suyi min fyade tabbas na tuna dukkan abinda ya faru dani ashe Yaya Nabil shi yake taimako na......kaina ya gama kullewa......tausayin Yaya Nabil naji da irin wahalan dayasha na neman yarinyar.........na dakata da karatun na juya na dauki gidan ring dinnan budewa nayi.....take nayi tozali da zobe na, zoben da Baba ya siya min tun Ina karama.......na tuna lokacin da Baba yace min Boddo Ina zoben ki.....namashi karya nace nakai inda ake wanke zobe ne su wanke min, da haka dahaka har ya manta bai sake tambayana ba.

Sannan kuma na tuna inda naga same zoben ahannun Yaya Nabil sanda ya dawo daga karatun soja, tabbas ko alokacin naso nayi bincike akan zoben Amma sai na hakura.,......na share hawayen daya zubomin na cigaba da karanta Diary din....wanda har up to date bai samu wani feedback akan yarinyar ba, Kuma baisan sunanta ba...........araina nace Yaya Nabil baisan Ni bace....Shi ya taimake ni ahannun kidnappers, bazan manta randa nai masa kwatancen bank ba a kaduna, amma shikam bai rubuta ba saboda baisan Ni bace.......Shin wannan wata kalan soyayyah ce, shi baya Jin komai game dani, na dauka tunda yana sona tun Ina karama, zai iya gane ni ko Kuma yaji sign azuciyar shi akaina.

Rufe Diary nayi naji kaman na dau zoben na tafi dashi amma wata zuciyan tace na bar masa kawai, miye anfanin dauka bayan har yanzu baisan nice masoyiyar tashi ba...Kuma Ni ayanzu aure zanyi,na dauki pen zanyi rubutu a wani pagr, Ina son na sanar dashi nice yarinyar dayake nema....amma tuni zuciyata ta gargade Ni,   babu anfanin sanar dashi komai tunda aure zanyi.....Ina hawaye nabar dakin Koh cikin gida ban Shiga ba na wuce na koma gida Kai tsaye dakina na nufa na kwanta don wani zugi da zuciyata takeyi....kodai nima na fara son Yaya Nabil ne, nake tambayan zuciyata

Haka naita tunani barkatai azuciyata har Mamie ta shigo tana ta min hira kadan kadan....Bata gane na fita ba.

********************

Ranar Alhamis itace ranar Kamu
Anyi min kwalliya kaman ba ni ba....haka muka nufi wajan event din wanda ba karamin kashe kudi Akayi awajan ba... Duk aikin Daddy ne.

Ina zaune a katafaren kujeran da aka tanadar domin ni da ango nayi kasa dakaina dake an rufemin da net, Ango Hamid na gefe na, naji muryar sa ciki ciki yana magana da abokanansu, daga kai nayi da sauri na fara kai idanuwana gare shi, sai dai ya bada baya.....haka na kura wa shigar tashi ido araina nace shidai Yaya Nabil komai nashi daban ne....dalili kuwa zaka iya rantsewa shine Ango a wajan, dukda shima angon dai bawai baiyi kyau bane. Amma zuciyata tafi hasko min Yaya na Nabil.

Karfe Tara na dare aka tashi, kowa ya koma gida, agajiye muka koma gida, Ni da Dije da mufida kasancewar su kadai ne kawaye na.

************************

The Next Day
Friday
8:00am
Dinner za'ayi yau.

Matar dake min dilka sai faman dirzan Jikina takeyi Awannan lokacin...  Ina Jin su dije da mufida suna ta hira abinsu amma nikam damuwace fal acikin raina.....Yaya Nabil kawai nake tunani ji nayi kaman na dau wayata na Kira shi sai Kuma na tuna bani da number sa don haka na hakura nabar wa Allah komai.

*************

Sauri yake ta faman yi ya kammala wa Hamid komai kafin ya tafi....sai da ya tabbatar ya hada masa dukkan abinda ango ke bukata ranar dinner kafin yasa kai ya fice.

Gudu yake ta falfalawa a babban titin.....tunawa yayi da ranar dasukayi hatsari da Boddo, Allah cikin ikon sa kuma take Nabil ya fara tunano moment dinsu da Boddo Yana jin strong feelings game da ita.,...shikam ji yakeyi kaman ita ce yarinyar da yake mutuwar so da kauna,......   Murmushi yayi lokacin daya tuna wani behavior din Boddo sai Kuma ya daure fuska....acewar shi taya zai rinka tunanin matar wani, wanin ma babban Amininsa Hamid....take ya kawar da zancen gefe yamaida hankali ga driving din dayakeyi......Yana Allah Allah ya Isa kaduna ya samu information akan Love dinshi.

***************************

Vote!Vote!!Vote!!!
Please and also comment are always welcome.

WACECE NI ✔Where stories live. Discover now