Chapter 6

311 28 0
                                    

Wacece Ni?
Story written by
DielaIbrahim ✍️

Part 1/6

***********

Tabbas Boddo makarantar Boko takeyi batareda sanin Inna ba

Tun Bayan data gama primary Inna tace Bokon ya Isa Haka
Sai ta dawo Talla

Boddo nason karatu tun primary sch dinta na daya take xuwa a jinsu har Karin class akai Mata saboda kokarinta yayi yawa

Baba yana son ta cigaba Amma Inna tahana
Baba Kuma yadau alwashin ko duka  yayansa basuyi karatu ba Boddo sai tayi
Hakan yasa yai Mata registration batareda sanin kowa ba suke xuwa ita da Dije
Tun jss 1 gashi yanxu suna SS 1
Kuma Baba yace data Kai SS2 zata rubuta waec inshallah

Ko su Rabi da Safiya Yan bin diddigi basusan da makarantar Boddo ba  saboda su iyayensu ba makarantar ce a gabansu ba neman kudi nee
Suyi ta daura was yaro Talla
Har auran sa

Abin da yake birge Boddo a gidan shine matan gidan Basu taba kawo ma Inna zigi akanta ba.....Kuma yayan ma Haka

wannan kenan

***********

Few months later

Boddo na zaune tana sharban kuka ta tasa bokitin tallan ta a gaba tana ta rusa kuka

Wata Mata ce tazo wuce wa ta Ankara da ita tace yarinya kekoh meyasa meki kike ta rusa kuka Haka
Ahankali ta daga Kai ta kalli matar tace ban saida kayan Talla na bane....to kekuwa basai ki tafi gida ba

Ai cewa sukai wai abincin yayi tsami Kuma Ina mamakin Taya shinkafa da wake zaiyi tsami

Danacisai na just tsamin tabbas Amma bansan daga inda yake ba
Kuma ahalin yanxu idan na koma gida bugu zansha
Ta karashe mgr tana shashekar kuka

To Kinga yarinya dare na karayi gwara ki tashi ki tafi gida kada wani abu ya same ki Koh
Kinji kiyi hakuri idan kinje ki bawa mamanki hakuri

Boddo tace toh nagode
Ta tashi tana hada kayanta
Tana kewan Dije Bata da lafia shiyasa Bata Zo ba

Tana cikin wannan tunanin ne
Mai mashin ya taho da gudu ya banketa arashin sani

Nan ta Fadi kasa warwas
Tuni mutane sukayi cha akanta
Ai da sauri aka sureta sai cikin asibitin tare da bokitan tallan ta

Mutane nata tofa albarkacin bakinsu.....

Bayan an shigar da ita ne likitoci suka nemi Jin Karin bayani kafin a amsheta suna Nan tsaye an gama masu bayani tare da yarjejeniya Mai mashin ne zai biya kudin
Suna ta kasafi batareda sun duba taba

Ahankali yake tafiya cikin natsuwa ya gota su kenan yaji hayaniya yayi yawa
Baya son hayaniya ko kadan
Kamar ya wuce sai Kuma ya dawo ya tambayesu meke faruwa ne???

Daya daga cikin likitan ne ya fara mashi bayani Bai ma Kai karahe ba  yaji yace
Maza a Shiga da ita A & E

Ba tareda Bata lokaci ba suka Shiga da ita
Shiyayi aikin Bata wani ji rauni ba goshinta ne ya bugu har jini ke fitowa sai hannunta data ji ciwuka har waje uku
Successfully suka gama Bata farfado ba Yaba da sallahu cewa a Nemo iyayenta xuwa Nan da washe gari
Sukace to

Acikin motar sa yake ta sake sake
Wannan wace irin yarinya ce da ko dayau she Bata damu da kanta ba.....Sarai ya gane yarinyar
Amma ya rasa meyasa Duk taimakon da za'ai Mata sai ya xama mutun na farko Mai taimaka ma rayuwarta

Uhmmmm yayi sansanyar ajiyar zuciya sannan ya ce Ina son ganin iyayenta don nasan dalilin dayasa suke son jefata cikin matsala Haka.

........
Boddo Bata farka ba sai karfe  Takwas na dare tana farkawa taganta saman gadon asibiti
Tayi yunkurin tashi Amma Ina jiri ya hanata tafiya
So take ta tafi gida
Amma ta aiyana anranta washe gari da sassafe xata bar asibitin

................

Yarasa meyasa ya damu da yarinyar tun dawowanshi gida yake ta tunaninta aranshi
Baya son rayuwar ya mace ta kasance cikin wahala
Yana matukar tausayin ya mace
Baisan dalili ba

Jiyayi an dafa shi daga baya
Yasan Ummin sace

Yadago Kai yace Ummi
Na dawo kina bacci sai na shigo daki ..........
Shhishhhhii 🤫. Baka shigo dakina ba nasan shigowanka
Kaitsaye part Dinka ka wuce

(Nabil)
meke damun kane yau ka dawo cikin damuwa

Babu komai Ummi gajiya ce taimin yawa Ummi kada ki damu kinji

Uhm uhm Nabil kasan bana son ganinka cikin damuwa Koh
Yai murmushi yace nasani Ummi shiyasa nace maki babu komai ai

To mi son bakaci abinci ba kazo
Let have our dinner ko

Oh Sweet Ummi
Ummi tai murmushi sannan ta tasa keyarshi gaba suka wuce part dinta

Akan dining table zuba masu abinci plate Daya suke ci tare
Har suka koshi

Ya Dade a part din suna hira xuwa karfe Goma ya koma part dinsa

..................
****************

DielaIbrahim ✍️
Vote and Share
Please

WACECE NI ✔Where stories live. Discover now