Chapter 3

472 31 0
                                    

Story written by
DielaIbrahim ✍️

Part 1/3

****************
Dedicated this page to mi lovely sister
Bilkisu Ibrahim❤️

*************

Bismillah ✍️

Tsahon Dakika 20 suka dauka sannan suka fito daga gidan tare da anso sakon goggo....sukayi hanyan gida abinsu,

Kasancewarta magriba ta gabato kai yasa sukai ta zabga uban sauri har suka kawo kofar gidan su Dije....

Dije nikam Bari na shiga gida kinsan Kamar yadda na Fadi maki Inna inta ñeme Ni Bata ganni ba can gane kurena......ki Bari anjima kadan can shigo sai insha furar.

To shikenan tunda kince Haka Boddo lafiyarki tafi min komai a rayuwa...kije Allah ya tsare
Ameen sai na shigo.

*******
Cen cikin makoshinta ta furta sallamarta don tasan babu mai amsawa sai mala'iku

Tasamu nasaran shiga dakin Inna....Wanda tana shiga ta nemi guri ta zauna daga bakin kofa kaman yanda tayi dazu...yanxu Kam ta hango Innar zaune saman wat tsohuwar kujera wacce Duk ta yayyage sbd jumawarta

*Ina kikaje don ubanki?

Kasa dago innocent face dinta tayi amma tuni idanuwanta suka kawo ruwa don ta San laifi ta rigada ta aikata shi.

Wata irin tsawa hade da zagi Inna ta Kuma surfafa Mata, sannan ta xabga Mata doguwar bulaliyar dake rike a hannunta
Hade da fadin Shegiya Mai halin mayu.....Zaki fadin min gidan ubanwa kikaje bayan dawowarki

Bata iya bude Baki Tai magana ba sbd azabar dukan da ake mata gashi tasani duk gidan babu Wanda ya Isa ya kawo Mata dauki, dama Baba ne
Kuma bayanan😢

Kimanin mintuna goma ta dauka tana zabga Mata sai datayi Mata tas sannan ta tura ta waje kofar daki ta rufe kofar ta ta barta Nan kwance

Hakika kuka take yi Amma babu Wanda zai gane hakan sbd ahankali takeyinshi.....

Ita kam takasa gane meke faruwa ne acikin rayuwata.....tasan ba Inna bace ta haife ta sbd so tari Inna na zaginta tare Dace wa
Shegiya wacce Bata asali.....Kuma Baba ya ki ya fadi Mata Ina mahaifiyar ta suke da dangin mahaifiyarta .....Shiyasa ta ke tsananin son baba sbd Duk yafi sonta cikin yayan da Allah ya bashi, shine ya zame Mata uba Kuma uwa acikin rayuwarta

Shiyasa Bata so daga want Abu ya same shi sbd gatan ta daya Allah Kuma gatan ta daya Babanta.... ..kuka ta cigaba dayi anan kwance......mutanen gidan sun fito waje don hada hadan sallan magrib
Al'adan gidan ne fito wa waje bayan sallan magrib anan xasu xauna har karfe tara Uwa goma suna Hira  yara kuma na wasa

Ko kallon ta basuyi ba sai harkan gabansu suke da yayansu

Da kyar ta iya tashi tayi alwala ta dawo Nan kofar dakin, kullin kayanta ta dauko Wanda dama nanne ma'ajiyarsu don Inna taje ba dakinta Kuma ba dakin mahaifiyar ta bace da zata na ajiye Mata simmokaran kayan ta....Hawayan ta ta share sannan ta kunce kullin kayan ta dauko wani wankakakken bakin cukurkuddadden hijab tare da Dan kwali ta shinfida sannan ta fuskanci alkibla

Bayan ta idar ne ta xauna it dakai tana kallon yaran gidan sa'o'inta suna ta hira suna shewa tare da uwayensu....kauda kanta tayi gefe guda tana kallon farin wata want ya haska ko Ina na gidan.....tsahon dakika Biyar kafin ta kalli hanyar waje
Dije ce ta shigo ta nufo inda Boddo take

Da murnar ta ta karaso wajen Boddo tare da mikamata kwanon fura tana Mata murmushi

Kauda kanta Boddo tayi

Dije abin ya Bata mamaki don Haka ta nemi gu ta zauna sanna ta Ciro karamar  touch light dinta ta haska fuskan Boddo

Subhanallah Boddo meya sameki haka kike zubda hawaye

Boddo ta cije lebe sannan ta ce bbu komai Dije

Ahah ki Fadi min indai ba so kike Nima na fara kuka ba

To kiyi kukan mana seme munafuka ai duk ke da muna fukar uwarki kuke zuga ta, takeyi iskancin da takeyi....to wlhy xanyi maganin abin Yan iska kawai, tashi ki fita ai ba gidan ubanki bane

Dije Tai Shuru tana kallon Boddo....Hakika dije na son mayar Mata da magana Amma kallon da Tai wa Boddo yasa tagane tana Mata àlama da tayi Shuru kada ta tanka

Tashi tayi ta niyan fita harta kusa Kai baking kofa In a ta kula kwanon furar da aka kawo was Boddo ,Dauka tayi ta zubar akasa sanna ta kwalawa Dine Kira

Zoki tafi da kwanon Furar ki

Tana dawowa ta tarar zubar da furan tayi Hawayen da take son boyewa Kar su fito sune suka fito ta kalli inna sannan ta karkada kai ta zugunna ta dauki kwanon tayi hanyan waje abinta .

Inna ta koma ga kallon ta ga Boddo tace......Wai ke Boddo ko Kyakkyawa to wlhy sai na lalata kyannan naki da kike dashi sai na nakasaki inga idan wani xai Kara Kiran ki Boddo agidan Nan.



**************



DielaIbrahim ✍️
Vote nd Share
Pls🙏





WACECE NI ✔Where stories live. Discover now