Chapter 24

256 26 0
                                    

Wacece Ni?
Story written by
DielaIbrahim ✍️


Part 1/24

_________________________
Bangaren Mama kuwa tunda muka fita tace Bari ta gyara min kayana tunda naki gyarawa tunjiya........zama tayi ta fara fidda kayan ahankali tana gogewa bata Dade ba ta gama don basuda wahalar guga
Ta shirya su tsab a wardrobe
Sannan ta dauki kullin kayan Boddo tace wannan Kam Ina xan kaimata Bari muga ko always abinda take so........

Mama ta kunce kaya sannan ta fara fiddasu a hanakali
Kwatsam hannunta yakai Kan towel din Boddo
Gabanta nee ya yanke ya Fadi
Ta bude towel din turaren Almiski nee ya fado
Tace wannan ai towel din......... sai Kuma tayi Shuru takasa karasawa.............
To me Boddo takeyi da wannan towel din
Uhmm koma miye Bari ta dawo xan tambaye ta
Mama ta zunduma cikin tunani
Saboda haryanxu towel na kanshin Almiski Wanda sai an diga a ruwa dashi akeyiwa diyar wanka Kuma akan shafa a towel din Duk sanda aka wanke gudun karni...........

Mama ta tashi ta Sanya towel din da Almiskin a saman kayan Boddo a wardrobe sannan ta kulle sauran kayan ta ajiye agefe
Tana jiran dawowan Boddo.

________________________
Yamma likis Ummie ta dawo batareda Boddo ba
Hayatee Bata ji Dadi ba Amma ta tausayawa yarta ayanda Ummie ta Bata labari cewa Adda yanxu tana yawan sa kanta cikin damuwar rashin yarta
Mama na gefe tace Allah sarki
Wanda Duk laifi na da sakaci irin nawa shiya jawo hakan taa faru

Hayatee tace aa Mama karki fada Haka Ina bayanki haka Allah ya tsara kudena sabo wa ubangiji
Duk abinda zaiyi to yakanyi shi dabdalili
Kuma da sannu xakuga sakamako......yaushe tace xata xo
Jibi tace
To Allah yakaimu itama xan mata fada akan ta Dena damuwa

................

Ina zaune a wani daki tamkar dakin sarauniya saboda kyan da dakin ke ciki....nace ohhhhhh Wai ni Boddo nice yau xan kwana a wannan dakin.....ahankali nace gaskiya nidai imanina xaiyi rauni Bari na je wajan Adda nace ta maida Ni gida baxan iya kwana a wannan dakinba

Na fita nayi kwanar dakin Adda
Na sameta a falonta na zuguna mace don Allah ranki shi Dade ki gafarceni baxan it's kwana a dakin cen ba

Tashi tayi da mamaki tace lafiya Boddo meya faru
Shuru nayi sai Kuma nafara kula nace wlhy tunda uwa ta ta haifeni nayi imani ban taba ganin daula irin na gidannan ba
Hajiya imani na zaiyi rauni don Allah ki maida ni wajan Hayatee
Dukda suma din suna cikin daular Amma cen xan iya kwana
Nan Kam na tsora gaskiya

Babu abinda Adda takeyi inbanda dariya wanna yarinyar lallai tana da abin dariya

Ahankali tabjanyo Boddo tabzaunar da ita tace Boddo
Wannan Yana Daya daga cikin ni'imar da Allah yai was rayuwarki, wata kila kinsha wahala nee a baya Amma yanxu
Allah Yana Kore maki duk wata damuwa Taki don haka ki gode Masa kinji
Nace toh nagode Amma xan iya kwana a falon Nan

Adda ta girgiza Kai tace dakin da kika baro shi xaki koma
Oyaaaaa bye bye sai da safe
Adda na fada tana min dariya

Nikam a tsorace nake haka na koma na kwana Ni kadai
Amma fah a kasan carpet na kwanta saboda saman gadon laushi gareshi sosai.....ga bedsheets Mai laushi da aka shimfida............kwanan kasa nidai yai min Dadi don ban taba kwana a irin wannan gadon ba tunda nake a rayuwata.........

.........................

Bayan kwana biyu Zan iya cewa naji dadin gidan sosai don azahiri ba matsayin Yar aiki Adda ta dauke Ni ba
Ita ta dauke Ni amatsayin Diya

Wanda har tamin Alkawarin xàn cigaba da karatu
A Rana ta Hudu muka fita da ita mukaje aka fito min da results dina na waec Alhamdulillah jarabawar tayi kyau sosai

Daga wajan muka je wajan tela ya gwada Ni ta bashi Kaya akalla sunkai Ashirin

Taganan Kuma mukayi cikin gari
Bamu tsaya a ko Ina ba sai kofar makarantar
Nile University of Nigeria

Kallo na tayi tamin murmushi
Sannan ta cigaba da tukinta
Duk inda mukabi sai Naga ana gaishe ta har muka Isa want office
Anan Naga tabada kudi masu yawan gaske
Atake akai mata printing admission letter akabata da suna data gani a saman waec form din
Sannan yace madam gobe xanje na biya kudin a bank sannan naje academic planning
Sai na karasa maku komai

Yace thank you sai ka Kira miji na ka sanar dashi idan ka Gama komai.....ohk inshallah

Muna tafiya naji wasu suna cewa
Lah matar Othman Abdulrahim
Nan ana ta gaishe ta tana amsawa cikin fara'arta

Har muka karasa mota
Sai da muka Isa gida nee take cemin Boddo Baki sha'awan canja suna nee
Nace aa ranki shi Dade Ina matukar son sunana saboda mahaifina nee yasanya min

Adda tai murmushi tace to shikenan ga papers dinki
Cikin week dinnan xa'a gama maki komai na registration
Course din da kika Fadi min shi na cika maki (pharmacy)

Hope Baki da wani matsala Koh
Nace AA nagode sosai babu abinda xance da ku sai godiya

Karki damu na daukeki amatsayin yata ne......Ni duk inda Naga Diya mace nakan ji Ina son taimaka Mata saboda yata Dana rasa don Haka wannan ba damuwa bane kinji
Gobe xamu gidan Hajiya nasan tana kewanki

Nai smiling nace Allah sarki Hayatee Nima Ina kewarta

Adda ta kalle Ni tace ke Kika sama ta wannan sunan

Nace eh ta nemi nabcanja Mata suna sai nace to tana son Hayatee
Tace min eh

Adda tace sunan da jikanta ke kiranta dashi kenan Amma ya'akai sunan yaxo mind dinki

Nai Shuru cen Kuma nace
Hakika Hajiya ta Shiga raina tun Randa na fara ganinta Inayi Mata aiki tsakani da Allah batareda na anshi ko sisi acikin kudin da ake bayar wa na aiki na ba..........
Inayi mata kallon uwa Kuma kaka agareni.....,tun Ina karama nake son Kiran wani da Hayatee sai Naga ita ce ta Dace da wannan sunan .....da mahaifiya ta nanan to da shakka babu itace rayuwata......nadan you Shuru

Adda tace Ina mahaifiyar ki nace ta rasu tun ina jaririya

Allah sarki Allah yai Mata rahama......ameen na Amsa

Nai Mata sallama ma wuce daki

Abangaren Adda kuwa tana Jin wani Abu game da Boddo
Jita keyi inama itace yarta
Hakanan tayi ta tunani har bacci Mai nauyi ya dauketa...

___________________Boddo__________

DielaIbrahim ✍️
Vote pls 🙏

WACECE NI ✔Where stories live. Discover now