Chapter 8

304 27 0
                                    

Wacece Ni?
Story written by
DielaIbrahim ✍️

Part 1/8

******************

Misalin karfe Bakwai ya fito cikin shirinshi ya nufi part din Ummie
A dining ya same ta tana jera abinci
Tabaya ya lallabo ya rungumeta
Best Mama in the whole world
Good morning Ummie

Morning  Nabil ka tashi lafia ?
Lafia Lau Ummie
Hope kin tashi lafia
Alhamdulillah

Yanaga yau ka shirya da wuri Ina komai lafiya dai Koh
Eh Ummie akwai wata Mara lafiya ce da xan duba ta

Ohk toh zauna Koh

Aa Ummie hada min komai idan naje nadan huta sai nayi break din......
Baffan ka ya kirani yake tambaya na ko ka kusan gama attachment Dinka
Nace mashi eh Amma kana so ka canja hospital
Shine yace to ba damuwa
Ko xaka koma cen nee ka cigaba dayi
Sai nace mashi sainayi shawara dakai shine yace
duksanda ka gama in sanar dashi
Oh toh Ummie
Ina ganin Baffa Yana so mu koma gida ne
Ni Kuma Ummie bani son zamanki a cikin gidan Baffah wlhy Duk da Nan ne yakamata mu zauna saboda nafison kwanciyar hankalinki
Amma matsalolin gidan  sunyi yawa wlhy Ummie

Toh yaxanyi idan yace na dawo
Kasan Baffa yayi hakuri  kusan shekara na
Biyar fa anan daga Ni sai Kuma  Kai
Sai Baffah idan ya kawo Mana ziyara

Bari naje Ummie idan na dawo sai mu larasa mgn Koh
To Nabil Allah ya tsare
Allah ya kiyaye hanya

Ameen Ummie nah

Minti 30 ya dauka ahanya kafin ya Isa asibitin
Kaitsaye ward din datake Nan ya nufa
Abakin kofar ya tarar da mutane suna ta hayaniya harda likitocin

Yace Dr. Nas me ya ke faruwa ne

Good morning Dr. Nabil dama patient dinnan nee ta gudu
What!!!

Yes  Kuma ga dukkan alamu Bata gama samun sauki ba
Sir. Gashi bamu samu address dinta ba cewar wata nurse

Ranshi ya baci sosai yace masu to shikenan
Office dinshi kawai ya wuce Yana ta huci

Wannan wata irin yarinya ce wacce Bata damu da kanta ba ballantana Kuma na mutane
Shi Yama rasa meyasa ya damu da kulawarta
Wata zuciyar ta kawar mashi da xanjanta.

Ya cigaba da aikin shi Amma Ina yakasa Yana tunano irin haduwan su da ita dole shine yake taimaka Mata
Kusan haduwa uku kenan acikin shekara daya
Amma ita ga dukkan alamu Bata sanshi ba,,shikuma yagane tane ta fuskanta.
Yace good da karfi gwanda ma karta sanni don bana son Shiga matsala
Haka yaita tunani shikadan shi Yana bawa kansa answer

.....................

5 months later

Kamar yadda kuka sani babu abinda ya canja game da rayuwar Boddo
Saima Kara lalacewa da tayi
Allah sarki Boddo

Ku biyo ni ku Sha labarin Boddo

Dije Aminiyar Boddo ta samu miji su Rabi ma sun samu inda za'ayi bikin su Rabi da wata daya kafin ayi na Dije

Shirye shiryen bikin su Rabi da Safiyah ya kankama
Sai haibaice habaice suke yi da Boddo

Boddo Bata da mashinshini an samata Boddo Amma daga gani sunan baiyi tasiri ba

Idan suna abinsu basuyi a gaban idon Inna sai idan Boddo na zaune ita kadai
.

.....


Da akwai wata Mata da take kawo wa Inna ziyara
Idan suka Shiga daki babu abinda suke sai kulle kulle
Wani zubin Kuma Inna ta sako Hijab dinta su fita tare Basu  dawowa  sai gab da sallan magrib

Kaman kullin yauma ta kawo Mata ziyara
Suna daka suna ta xance
Adaidai lokacin Boddo ta shigo gidan tayi sallamarta Duk da babu Mai amsawa
Tanufi dakin Inna zata Shiga kenan kunnuwanta suka jiyo Mata abinda ya gigita kwakwalwanta
Tokarewa tayi abayan kofa ta kasa motsi sannan ta cigaba da sauraransu

Kamar yanda nake fada maki kawata Malam yace yarinyar zata zama baiwarki har ranar da zata bar duniya idan kika yi an fani da maganin nan
Yanda ya dace
Sannan shi Kuma Baba kince wancen asirin da akayi ya karye Koh
To ga wani kullin magani a ruwan wanka kawai xaki sa mashi maddin yayi wanka dawanna ruwan to xai Dena ganin mutuncin Boddo sannan Duk abinda yake Mata xai Dena bugu da kari Ba xai Kara tsallake maganarki ba
Kuma bazai sake  maganar Boddo ba agidannan
Ni na Gaya maki Haka

Masha Allah shiyasa nake sonki Sa'a sa'ar Mata Allah ya bar Mana ke

Aakwai wani Abu daya sa'a
Bana son ganin cigaban Boddo
Shiyasa ma tuntuni na Shiga na fita naganin babu saurayin da yake xuwa wajanta
Yarinya Duk tabi ta kanainaye Min miji ko kula da  dansa idi bayayi
Shiyasa nadau alwashin sai na rabasu sai na sanya Masa kiyayyanta a xuciyarshi

To mexai Hana a tura ta aikatau kawai Asabe (sunan Inna kenan)

Aa ai idan na turata aikatau Bata kusa Dani wata kila cin dadi xata rinka yi
To in Banda abinki Asabe kudin aikatau din ke xa'a rinka kawo mawa kina facaka dasu
Kuma yanda take dinnen gida Mai maikoh xamu samu inda Koh Dubu talatinne xa'arinka bamu awata ki duba shawarata
Kinsan kaskancine mutun ya ringa aikatau Kuma irinsu da wuya su samu mijin aure Kinga shikenan mun nakasata
Ba mashinshini ballantana tayi tunanin Aure

Uhmmmm da gaskiyar ki sa'a to Bari na gama da malam tukunna sai mu Kara sa xancen da aikatawa Koh!

Boddo batasan sanda hawaye suka fara xuba a idanuwan ba
Ta fita daga gidan da gudu tayi gidan goggo tana kuka

Goggo tayi tayi Boddo ta Fadi Mata meke damunta Amma Ina Taki Fadi Mata

............
*****************

DielaIbrahim ✍️
Vote and Share
Pls 🙏

WACECE NI ✔Where stories live. Discover now