Chapter 10

324 24 2
                                    

Wacece Ni?
Story written by
DielaIbrahim ✍️

Part 1/10

*******************

Tundaga wannan rana Boddo ta rasa farin ciki
Domin kuwa Al'ameen ya janye
Neman da yakeyi da ita

Ya baiwa baba hakuri tareda cewa iyayen sa ne suka Masa kashedin auran Boddo
Wai saboda Yan anguwa duk sun San da maganan fyadan da akai wa Boddo, dama za'a hadata dasu Rabi ne
To yanxu ba maganan auren  Boddo

Haka lokacin auran yaxo akai ta shagalin biki
Innah Bata bar Boddo ta zauna ba ko da yaushe tana cikin aiki da aike da Kuma Talla
Har aka gama bikin

Ace warta hakan shi zai Hana Boddo Tai saurayi

Bayan bikin da  sati uku ana  saura sati daya bikin Dije

Boddo na zaune saman gadon Goggo tayi tagumi
Dije tace kiyi hakuri Boddo Haka Allah yaso Amma Ni bani so kina damuwa
Don Allah ki Bari

Dije bazaki gane ba Ni ba saboda Al'ameen yaki aure na bane nake tagumi illah saboda sunana da aka batamin a anguwa wasu tausayi na zasuji wasu Koh...ko a gefen zanin su
Dije ni tawa kaddaran Haka tazo min sai dai in cigaba da imani da ita gudun kada na sabawa ubangiji na

Dije Nan da sati daya kacal zakiyi aure zan koma nikadai babu wacce xan dinga gani inajin farinciki acikin Raina sai goggo
Makaranta, Talla, Aika, yawo Duk Ni kadai xan rinka zuwa
Mexaisa kice baxan damu ba
Ta dan goge hawayen dasuka xubo Mata sannan ta cigaba

Dije kune kuke debe min kewar mahaifiya ta
Baba Bai cika zama ba ballantana yai Hira Dani
Gashi yanxu tunda abinnan yasame Ni da farko kullin ya ganni sai ya zubda hawaye
Amma daga baya Dana fadi Masa ya gane gaskia ba'aimin komai ba
Sai dai yai ta tausayi na Kuma dukda haka Inna tafi karfinshi
Sannan Yana so ya cika kudirinshi na ganin na gama sec sch nasan Kinsan da hakan
Shiyasa so da dama yake yi kamar Bai damu Dani ba gudun kada Inna tagane Ina makaranta
Gashi harna kusa karasawa
Tai murmushi
Kindan meye Dije
Idan natuna Ina da ilimin addini Dana Boko nakan just dadi sosai
Kuma son Baba azuciyata karuwa yake
Tun Ina karaama bani da buri da wuce inganni a makaranta inga nayi karatu
Gashi Baba yayi iyakar kokarinsa
Nikam inshallah  ko baji ma ko ba dade wlhy Dije sai na cigaba da karatu sai nayi University

Dije datai Shuru tana sauraranta
Tai murmushi tace kindade kina fada min cewa da yardar Allah sai kin cigaba da karatu
Shiyasa kullin nai sallah nake tayaki da addu'a
Allah ya cika maki burinki

Ameen summa Ameen Ni wlhy saboda na taimakawa Baba nakeson yin karatu

Dije ta dafa ta tace Kiyi hakuri Boddo ai anan saman layin zan zauna idan kikaji kadaici basai ki xo ba Kuma makaranta ma ai tare xamu rinka xuwa
Karki damu kinji ko
Kiyi murmushi don Allah

Boddo Tai murmushi tace to shikenan naji
Yanxu ki tashi muje wajan Mai dilkanan ko tagama hadawa Koh
Ta bamu

Eh hakane fa na tuna muje

...............

Nabil Baffah ya Kira fah daxu Wai suna hanya gobe inshallah

MashaAllah
Dagaske Ummie

Eh Kuma yace da akwai maganar dake tafe dashi sannan buguda Kari yayi kewanmu

Nabil yai murmushi duka duka wata uku nee fa rabon mu da Baffah...... uhmm Baffah kenan
Naso na rigashi zuwa ganin shi Amma tunda zaizo Kam shikenan

Ya dauka wayanshi ya Kira private number Baffah
Bugu daya aka daga cikin sallama

Ya amsa cike da doki
Yace Ina yini your highness

Cikin wayar akace
Uhmmmm Mi Son kaifa idan kasan kayi laifi
Babu sunan da baka kirana dashi domin neman yafiya

Nabil yai murmushin Daya fito mashi da dimple guda daya daga kasan kumatunsa Wanda ya lotsa sosai ma'ana dimple din shi ya karamasa kyau zallah

Yace Baffah nah bana kowa ba

Wanda aka Kira da Baffah yace
Nima Nabil dina bana kowa ba

Baffah karfe nawa zaku iso gobe

Huhhh 😲jimin yaro ko tasowa bamuyi ba kana tambayan what time xamu iso
Uhmm to dai flight din karfe 9 zamu bi Kuma dai kasan babu nisa ko

Eh Baffah Ina Nan Ina jiranku
Daga yanxu xuwa karfe Shida
Na rufe schedule din fita
Nida fita sai Inka koma

Baffah yai dariya
Dadi na dakai akwai iya karrama bako
B

affah ai ka fi bako
Muhimmanci

Uhmm Baffah nah zai zo Kam Ina Ni Ina fita salan na ja wa kaina wani laifin

Hmmm ai Kai baka laifi mi son Allah dai yai maka Albarka
Ameen Baffah

Gobe xamu yi mgn Koh
Toh Baffah a huta lafia

Ya ajiye wayar ya kalli Ummie

Murmushi takeyi yace
Lahhhh Ummie

Ummie Tai saurin kallon shi cike da son Jin mexai fada

Rabon da Naga wannan murmushin naki harna manta
Ko dai Duk saboda Baffah xaixo gobe nee😉

Ummie ta hade Rai

Wayyoohhh Ummie da wannan fushin nata
Allah yai saurin kawar dashi .....
Ya karashe yana kokarin sabulewa ya gudu

Ummie tayi kaman xata kamashi Amma Ina tuni ya tsere Mata
Tai dariya ta wuce dakinta

................

Ayau ake daura auran Dije Aminiya ga Boddo

Innah Bata son ganin Boddo ta halacci bikinan don Haka ta cika Mata kayan Talla
Kuma ahakan Boddo Tai saurin saidowa ta dawo ta Mika Mata kudin
Sanin cewa Inna na iya cemata ta xo ta zauna agabanta yasa ta gudu da sauri Innar na kiranta Amma Ina tayi waje cikin sauri tashiga gidan da Yan Mata suke

Yan matan qawayensu na makaranta nee su biyu suke ta kokarin kwashe abinci suna xubawa a bokitin fenti
Babba

Boddo tace sannunku Sabira
Kunsha aiki
Wlhy Koh bakomi ai harkin dawo ne

Eh Ina Amaryar take nee?
Tana ciki takiyin wanka Wai sai kin dawo

Boddo ta Shiga dakin tana sababi
Toh na dawo sai ki tashi ki Shiga wanka ga Alawiyya Nan ita xatai maki makeup Kuma normal ba Wanda ake cika foundation ba
Y

auwa don banson Wanda ake cika foundation

Nima na tsani irin kwalliyar Nan irinta akai wa su Rabi
Kaman aljanu
Amma na yadda da alawiya Dan ta iya sosai

To naji muje nayi wankan

MashaAllah dukda bikin bana masu kudi bane Amma anyi komai a wadace Amarya tayi kyaau sosai
!!!!!!

******************

DielaIbrahim ✍️
Vote and Share
Pls 🙏


WACECE NI ✔Where stories live. Discover now