Chapter 7

271 27 4
                                    

Wacece Ni?

Part 2/7

_____________________ Present Time
7:00am

Bude idanuwa yayi ya sauke su a Hoton dake manne jikin bangon dakin nashi
Ummie ya furta Yana matukar ji da Ummie yayi kewanta na kwana dayan nan dayayi
Gashi tana ta mashi text Wai ya dawo ba'aga Boddo ba tun jiya da ta tafi sch...........................

Tunanin koma gida ko ya cigaba da neman yarinyar nee
Har dai ya yanke shawara
Ya tashi ya Shiga wanka minti kadan ya shirya ya fito
Asibitin ya koma Yana neman mutumin dayayi masa bayani jiya..........Nan take ake sanar Masa da cewa jiya mutumin a hanyan sa ta komawa gida yayi hatsari Kuma atake Allah ya dau ransa.......sosai yaji mutuwar mutumin ya nemi da akaisa gidan mutumin
Ko da yaje yayi ta'aziya wa iyalan mutumin sannan ya masu kyauta Mai tsoka ya musu sallama ya tafi............................sai da yayi kwananki bakwai a garin kd
Yana cigiyar yarinyar........
Wannan kenan

______________________
Makera,rigasa kaduna.......8:00pm

Goggo don Allah ki sanar Dani komai hakika Ina cikin duhu, tun ranar da naxo garinnan kunnuwa na suke jiye mini maganganu dayawa akaina da Kuma baba Wanda na kasa fahimtar ko Daya daga ciki........ke sheda ce goggo yau kwanana Shida Amma kullin sai Inna ta Aiko ko taxo da kanta da maganganu Wanda kunnuwa na suka kasa dauka har yanxu
Maman Rabi da maman Safiya sunce Baba yabar maki wasiya cewa kisanar Dani wani abinda ban sani ba
Da alamu wasiyar tana da muhimmanci acikin rayuwata.....ta share hawayen da suka Dan sauko Mata tace goggo
Ki Fadi min don Allah

Dije da ke gefe tace bason ran mu bane sanar dake komai awannan lokacin Boddo.....Amma ganin Baba bayanan shiyasa suke ta fallasa sirrin da ya dade a birne
Dukda cewa babu Wanda Bai sani ba a gidan ku.......Amma shakkar baba yasa kowa yai Shuru da bakinsa.......nida goggo kullin muna addu'a Allah kada ya kawo ranar da xaki ji magana makamanciyar wannan, to sai dai kaddara a rubuce take..........tayi Shuru tsahon dakika goma babu Wanda ya sake cewa uffan a cikin su...........

Gyaran murya goggo tayi ta kalli yaran nata, ta ruko hannun Boddo tace........labarin wasiyar da Baba yabari kike son ji?

Na gyada Kai Alamar eh da sauri

Goggo tayi murmushi sannan ta dora da cewa.....................xan Baki labarin WACECE KE Boddo Amma ki bar wannan a matsayin sirri kada ki sanar da kowa......Kuma har gobe Ina so ki Sanya aranki Baki da mahaifi sai Baba.............tayi Shuru sannan ta cigaba .................

Labari

Shekara Ashirin Baya

Baba alokacin ana kiransa da malam buba Wanda har yanxu bawai sunan ya bata bane mu na gida mu nee muka koma ce mashi Baba kamar yadda yar Daya tsinta take kiransa dashi
Wanda ita tafara kiransa da Baba kafin sauran yayansa Suma suka kirasa da hakan..........ita wannan yar.....yanda akayi ya sameta shine

Malam buba kowa yasan shi mafataucin kifi ne sukan je rafi suyi kwanaki suna Kama kifi
Idan suka Kama sai sunkai an siye kafin suke dawowa gida
Shiyasa yake Dade wa wani zubin Bai dawo ba

Kamar yadda Abban Dije yabamu labari kafin Baba ya bamu nashi labarin

Ranar sun tafi Kama kifi da yamma harda Abban Dije kasancewar shi sabo a harkar
Sai malam buba ya ce yaxo suje don yaga yanda sukeyin sana'arsu

Sun Isa wajan da yamma sosai
Suka fara aikin shirya komai yanda sukeyi suka barshi a ruwa
Sannan suka tafi su kwanta sai da safe zasu cigaba da komai

Bayan sun gabatar da sallan  magrib suka hada wuta na Kara
Malam buba ya zagaya wajan rafin don dubawa ko tarkonsu ya yi..............ya dago katakon net din sai yaji nauyi
A tunanin shi kifayen nee suka hau sosai.......sai ya kirawo Abban dije dayaxo ya taimaka Masa su Kama kada suyi asarar na yanxu

Sunyi nasaran janyo net din suka ainihin xuba ababban bahon dasuke xubawa
Haskawan da malam buba da
yayi da tochi
shi yasanya gabanshi Fadi warwas........Abban dine yace Inna lillahi wa'inna illaihi raji'un
Malam Buba Dan mutum nee fah jaririne Amma da alama baya numfashi

Sukayi saurin daukan jaririn
Suka yanke shawaran kaishi asibiti ko da ma bashi da Rai

Sunyi nasaran Kai jaririn asibiti mafi kusa da wajan
Cikin ikon Allah aka du ba jaririn
Likitocin sunyi matukar mamakin dukda ruwan da jaririyar data Amma bata mutu ba tana so ta rayu
Hakan yasa sukai Mata tainakon gaggawa kafin washe gari da safe suyi transferring dinta ixuwa babban asibiti don duba lafiyar jikinta sosai

Successfully suka dawo da numfashinki
Anna da Tai makon oxygen

Da safe akayi gaggawar kaiki babban asibiti
Aranar Malam buba suka dawo Mana da labarin ki alokacin malam buba yabaiwa Inna kudi ta siya kayan jarirai
Amma Inna Taki siya ta kashe kudin

Kina asibitin mukaje muka ganki lokacin na haifi Dije da wata biyu

Kina da kyau matuka
Idan aka ganki baxa'a ce kice aka Ciro daga cikin ruwa ba

Satin ki Daya aka sallame ku
Malam buba ya baiwa Inna ke riko
Hakika kinsha wuya a hannun Inna har Kona ki da wuta tayi
Babu irin azabar da Inna batai Miki ba idan malam buba ya dawo sai tace ai kece ba kyaji tana cikin aiki Kika mirgina

Kullin dai haka xanjen yake
Malam buba ya rada maki suna Boddo sannan ya tara iyalan shi yai masu kashedin
Kada Wanda ya kuskura ya sanar dake cewa bashi ya haifeki ba
Duk Wanda yayi gigin fada maki to wlhy abakin auranta

Sannan Kuma ya fifita ki acikin yayansa Yana matukar sonki sosai.....wani lokacin yakan dauke ki ya tafi dake Rafi
Har Kika fara girma
Daga Nan nee Inna tace karya Kara tafiya dake xaki tsaya ki rinka Taya ta aiki
Malam buba baisan ana daura maki Talla ba
Sai daga baya yasan hakan
Kuma alokacin Inna da alama rufe Masa Baki tayi saboda ranar Daya fara fada yace baxaki Kara xuwa talle ba
Washe gari Kuma dayaga an daura maki sai ya wuce babu abinda ya ce tun daga lokacin in a ta samu damar daura maki talle safe da yamma

Goggo ta kalli Boddo da take ta faman sharban hawaye

Goggo tace hakuri xakiyi Boddo
Haka Taki kaddaran take
Ki rungumeta gudun kada ki tsaba wa ubangijinmu

Boddo tace Goggo
Yanxu bansan Wacece Ni ba
Taaya hankali na zai kwanta
Dole na nemi Asali na goggo
Ina son nason ko Wacece Ni

Goggo tace yanxu tashi kuje ki kwanta gobe sai mu karasa maganar Amma don Allah Boddo kada kiss damuwa aranki kinji

Boddo ta gyada kai
Ta atashi tayi alwalan bacci
Taxo ta kwanta kusa da dije tayi addu'a ta rufe Ido
Anna Ina baccin ta nema ta rasa

Cikin ranta tana tsara yanda xata
Nemo Asalinta nee shin ta Ina xata fara
Rafin xata je ko Ina?

Wacece Ni Ina bukatar sanin dangi na Ina son ganin mahaifiyata sannan Ina son sanin dalilin bacewata

Amma ta Ina xan fara.............
Tashi tayi tana binciken hanyoyin da rafin kaduna ya bi ya fitaxuwa wani gari

Atunaninta ta hakan xata bi ta gano garinsu..........

...............

DielaIbrahim ✍️
Vote pls




WACECE NI ✔Where stories live. Discover now