Chapter 17

258 25 0
                                    

Wacece Ni?
Story written by
DielaIbrahim ✍️

Part 1/17

__________6month later_________

It's her new life
So anything can happen's to her
😉😉😉

Yau kimanin wata Shida (6)month kenan
Ina aiki a cikin gidan da ban taba ganin Mai gidan ba
Amma na Saba da komai na gidan Kuma nasan ko wani bangare na gidan
Ba shakka Ina Jin dadin kasancewa dasu Hajiya da Mama
Amma Kuma nakanyi kewan Baba Allah sarki Baba yau wata Shida Bai sani a idanuwansa ba
Allah yasa Yana lafiya
Duk wata Talatu takan xo amsan kudi Amma boye min takeyi batasan mu hadu ko kadan so daya na taba ganinta  naje gareta Ina kuka ta maida Ni gida inga Baba inyaso saita dawo Dani

Hakuri taita bani Wai in Bari taje ta dawo inshallah xata kaini
To ganin da ban Mata ba kenan har yau.

Abuldarr yaran mummy ya gwada yana Sona sosai don Haka nayi wani tunani
Kuma na bashi hadinkai
Dukda nasan ba auransa xanyi ba don Ni a tsari na bani son Mai kudi ko kadan
Nafi son talaka Irina
Yakan min Duk wani Abu da saurayi ke yima budurwa
...
Mama batasan Yana Sona ba
Sai wata Rana  kwatsam da tagan mu muna hira cikin wasa da dariya

Mama ta kirani ixuwa daki hankalinta a tashe
Taso ta sanar Dani wani Abu Amma ganin kaman na fada sonshi dayawa yasa Tai Shuru
Amma ta gargadeni da nabi ahankali
Allah sarki Mama kenan

Ana Haka nee wata Rana Abuldarr ya kirani misalin karfe goma na dare
Yacemin inxo dakinshi baya da lafiya inxo inyi jinyarsa
Sosai abin yaban mamaki
Inyi jinyarsa kuma
Nace mashi yayi hakuri dare yayi
Magiya ya fara yimin ahankali
Ina turjewa akan baxan samu Daman xuwa ba.....sauri ma nakeyi na koma daki don Ina waje na boye inda Mama baxata ganni ba
Dana gaji da magiyar da yakeyi min nace mashi saida safe na kashe wayar da shi ya siya min

Na koma daki na kwanta
A Raina Ina mamakin shi Wai inje inyi jinyarsa

..........

Washegari da safe bansa shi a idanuwa na ba Haka har dare yayi wasa wasa sai da mukayi kwana uku ba muga juna ba
A kwana na Hudu nee nayi niyar xuwa flat dinshi donjin ko lafiya

Knocking nayi ahankali
Amma Shuru ba'ai magana ba
Sai na gwada Murda kofar
Da ikon Allah naganta abude kuwa nishiga
Parlo nee Mai kyau Amma babu kowa a ciki
Sai kofar bayi na falo sai dinning ciki akwai kofar da nake tunanin nanne dakin shi
Sai na nufi kofar
Ina Shirin murdawa naji magana kaman na mace
Sai na saurara kadan
Amma gaskia bana iya Jin komai

Zuciyata na tunzurani na bude kofar aikuwa sai gashi ta budu

Banga kowa ba dayake gadon Yana cen ciki nee kamar yadda dakin Hajiya yake
Sai na nutsu na cigaba da tafiya na sauka ta step na Mike sampal inda nake iya hango gadon

Sai dai Kash zuciyata ce ta daskare sakamakon ganin wata mace da Kuma Abuldarr kwance
Cikin bargo
Kawar da fuska ta nayi
Cen Kuma
na sake Kai duba na ga fuskan yarinyar
Inna lillahi wa'inna illaihi raji'un
Babu shakka basira ce
Sai na fara tunano gani na da yarinyar Bai wuce so uku xuwa Hudu ba
Basira tana Daya daga cikin Yar aikin gidan ita ma Amma tana bangaren masu wanke wanke ta wajan Mummy qarama
Yarinya ce Kyakkyawa yar fulani
Nima bamu taba magana da ita ba nasanta nee sanadin Mama
Randa muke xagaye gida
Mama take Fadi min sunayen Yan aikin da muka gani masu mugun yawa Kuma ciki harda ita basira

Ina Nan tsaye naqasa gaba naqasa baya zunzurutun ina cikin fargaba
Nawani tsaya kaman wacce jijiyoyin jinkinta suka Dena aiki

Basu lura daniba illa harkan gabansu kawai sukeyi
Wanda tuni na rufe idanuwa na na juya don Bai kamata Naga tsiraici irin Haka ba

Da kyar na samu kwarin gwiwar daga kafa na guda Daya
Na fara takawa ahankali
Har na fita batareda sanin su ba
Kaitsaye flat dinmu na wuce
Har na gitta Mama wacce sai faman magana takemin Amma Ina hankali na yayi gaba
Bana Jin komai a wannan lokacin

Daki na nufa na xauna Jim kadan Mama ta biyo ni ta dafa Ni
Lafiya Boddo meya sameki ne Haka
Kuka na fara yi na rungumeta
Ina Mai Jin dadin kin xuwa Dakin Abuldarr awancen Daren Daya kirani
Mama tayi tayi na Fadi Mata
Amma na qasa sai tayi fushi ta tashi xata fita

Hakika tunda na fara rayuwa da Mama ta kasance tamkar uwa agareni Bata qaunar ganina cikin damuwa don Haka Banga dalilin boye Mata abinnan ba tunda ta rigani xuwa gidannan so ta fini sanin komai game da halayen Yan gidan

Ahankali nace Mama na
Kiyi hakuri ki dawo na Fadi maki abinda ke damuna

Mama ta dawo ta zauna

Na kalle ta kadan sanann na fara Bata labarin Duk yadda abin ya faru tsakanina da Abuldar

Murmushi Mama tayi
Tace meyasa wancen ranar nace maki kibi ahankali
Saboda nasan komai akan Abuldarr ya Bata rayuwar Yan Mata agidan nan  wa'inda suka xo aiki  gidan nidai Wanda na sani kenan
Ko wacce takan yadda dashi nee saboda yace Mata zai aureta daga karshe idan ya Gama anfani dasu yakan kala masu sharri yasa akore su

Naso na Fadi maki tun ranar Amma sai na bar was Raina saboda Naga yanda kika tsunduma cikin soyayyar sa
Gashi Allah ya taimake ki tun ba'ayi nisa ba kin gane gaskiya
Yanxu dai matsalar guda Daya ce
Ya nemi ki xo kinki xuwa
Idan ya kasa cin galaba akanki
Zai San yadda yayi yasa akore ki
Kicigaba da addu'a kinji
Inshallah Allah zai taimake ki

Na riqe hannun Mama
Nace Mama ban taba yadda da Abuldarr ba na bashi hadin Kaine saboda nasan mene nemanufarsa akaina, Mama ban taba sawa araina xan auri mai kudi ba
Kuma ki dubi matsayin fah Ni Yar aiki bugu da kari Yar talaka
Wacce ko Mummy qarama baxata taba bari ta hada jini da talaka Irina ba.......... baisan daga Ina nake ba kwasam yace Yana Sona
Kuma lokaci Daya Wai zai aure Ni Kinga kuwa dole a dasaa ayar tambaya a wannan labarin son nasa
Shiyasa nayanke cewa xan bishi da sannu xan gane abinda yake nufi Kuma gashi na gane
Ayanxu baxan ta ba barin yasan nasan komai akan halaiyarsa ba
Kuma xanyi yadda kikace Mama nagode

Babu komai Boddo tashi muje wajan Hajiya daxu tana ta bidar ki

Toh Mama

Suka nufi dakin Hajiya

................

DielaIbrahim ✍️
Vote/Share please

WACECE NI ✔Where stories live. Discover now