Chapter 1(New part)

268 25 0
                                    

Wacece Ni?
Part 2/1

Bisimillah
Time pass
4years later
__________________________Nigeria
Abuja_______maitama
At 4:10pm

Misalin karfe Hudu
Wata mota kirar Matrix fara dal
Ta danno Kai gidan Alhaji Yusuf Bello......Kai tsaye motor park motar tayi sannan akayi cooling dinta ahankali........ sannan aka bude kofar alokaci Daya Kuma aka ziro kafa waje
Baka iya ganin komai a kafar
Saboda black socks da Kuma Ash flat cover dayai ma kafar kyau sosai ,sai black jeans da ya Dan nuna sign dukda dogon Ash colorn hijab din ya rufe wandon ana iya ganin shatin shi......
Tsahon mintina biyar ta dauka acikin motar da àlama littatafai take kwasowa
Tuni ta fito sannan ta Kuma dukawa ta janyo wata Ash handbag ta rataye sannan ta kulle motar tasa key

Ta Kama hanyar Shiga ciki
Lailah diyar mummy ta fito xata wuce ta hadu da ita tace
Gida bana uban mutunba Amma sai cin arziki akeyi andai ji haushi.......ta qarasa maganar tana tura baki.

Bata tsaya kula taba Tai gaba abinta Kai tsaye flat din Hayatee ta nufa sannan tashiga da sallamarta dakin ta Shiga ta sameta zaune tana aikin karatun jarida......Dane wa cinyarta tayi tace mi granny kintsufa amma sai kin karanta labari

Uhmm jimin 'ya ke idan aka ganni aka ganki basai a dauke niba abarki ............kece ai kikai Kama da tsoffaffin Kinga Ni dagani karki karasa min cinyar

Dariya nayi nace toh basai ki rinka hutawa ba

Tace aa banni kawai nakaranta  nasan Miye duniya take ciki
Ke indan nasaki ki karanta min sai kiyita sauri da turancinku irin na turawa ni ba gane wani abin nake ba..........

Dariya nayi tayi
Sannan nace Hayatee nah na dawo daga sch

To sannu da dawowa BODDO
__________________________________
_________________________
__________________
Tuni ni Mai rubutu Alkalamina ya kusan fadi kasa zabagen mamaki dajin cewa Wai Boddo ce ta dawo Haka
Boddo dai wacce take Talla a kaduna ko wacce ranar Allah
Wacce Bata da gata ko kadan
Na kuma kallonta lallai shekara Hudu bawasa bane yanxu Boddo tana neman shekara Ashirin da Daya (21 years) jindadi ya nuna sosai a chocolate color din fatar ta
Wani abin mamaki shine  Familyn Alhaji Yusuf Bello sun dauke ta amatsayin diyan da suka haifa babu wani Jin dadi da Boddo ta nema ta rasa a gidan ....bugu da kari Boddo har motar Hajiya (Hayatee) take fita da ita Wanda Hayatee ita ta Mata izini dahakan Amma da kyar Boddo ta yadda don saida yazama ta Dena ma Hayatee magana sai da Adda tasa Baki  kafin ta yadda har ta koyi tuka mota.....Acewar Hayatee Wai yanxu Boddo ita xata dinka kaita anguwa da Duk inda xata.............
Adda Kuma babu abinda batayiwa Boddo ita dai tana son yarinyar tana Mata kallon yarta ....hmmmmm Rayuwa kenan da alamu Boddo dai ta zama Yar gida......to Bari muji yanda za'a Kaya............
__________________________________

Boddo ta tashi ta nufi dakinsu, ta gaishe da Mama....sai wasu Yara dasuka rungumeta suna murnar dawowarta
Da alamu jikokin Mama nee

Mama tace kunga ku sake ta ta huta ko......

Ta nufi toilet tayi wanka
Tafito ta shirya tsab cikin wata doguwar Riga na material dinkin yai mata kyau ta yafa gyale
Kwalli kawai ta Sanya sannan tace Mama na tafi wajan Ummie
To sai kin dawo

Kai tsaye flat din Ummie tanufa
Da sallama ta Shiga ta iske ta xaune saman kujera da àlama waya tagama yi
nace barka dai da warhaka Ummie nah

Ummie tace ahah harkin dawo daga makarantar eh Ummie
Ummie tace yanxu nagama waya da yayanki

Nai murmushi nace Ummie kullin sai kince yayana Kuma Baki taba bani shi muka gaisa ba
Shin shi yayan nawa yasan da kanwar tasa na fada a salon shagwaba

Da mamaki Ummie takalli Boddo tace Ina xuwa
Kiranshi ta Kuma yi
Bugudaya ya dauka yace Ummie
Na nikadai cen Kuma yace oppssss Ummieyn mu mu biyu nayi tafiya wata taxo ta kwace min soyayyar Ummie
Idan na dawo sai na sata kuka

Ummie Tai dariya ta kalli Boddo
Boddo tana sauraran shi itama murmushi takeyi

Ummie tace bata kwace  maka niba kawai dai ta maye gurbi na ne?

Kai Ummie dama akwai wacce ta isa ta maye gurbi na?

AA Amma kanwarka ta wuce misali wajan yabo,,,,na Bata ne ku gaisa nee

Yadanyi Shuru kadan na tsahon minti biyar kafin yace Bata

Koda Boddo ta amsa Shuru tayi
Shima Kuma Shuru yayi
Cen tace Ina yini
Jiyayi gabansa ya Fadi dum
Kaman muryar ta yaji
Uhmm kawar da zancen yayi yace shi ba dama yaji muryan mace sai yace muryarta nee

Ahankali yace lafiya
Ya kike

Tace Alhamdulillah
Yace to kicigaba da kula min da Ummie na kinji idan na dawo Naga ta canja xan Miki kyauta

Nace to in Allah ya yarda nagode
Na Mika wa Ummie wayar na samu waje na xauna
Bayan tagama nee nace
Ummie kina da aikin da za'ai maki
Ummie ta girgiza Kai

Nakara  cewa ko wanki babu

Ta girgiza Kai tace Boddo bakya gajiya da aiki nee jiya fa kikamin wanki Kuma yanxu kina tambayan wani to babu
Shikenan ke baxaki huta a rayuwarki ba
Nace Agafarceni Ummie amma zaman aiki nakeyi a gidannan Kuma Kuna kyautatamin shiyasa Nima nakeson kyautata maku
Mahaifina Yana yawan fada min cewa Duk Wanda ya kyautata maka to kaima kasaka Masa da Alkhairi

Ummie Tai murmushi Masha Allah angaishe da Baba nikam Ina son ganin mahaifin ki Boddo
Kodan jinjina Masa irin tarbiyar Daya Baki .......Allah yai maki Albarka 🙏 🙏 Kuma Allah ya baki miji na gari Wanda zai kula dake

Boddo ta sunkuyar dakai ta Kama gefen gyalenta tana was dashi.....ahankali ta rinka ja da baya har ta gudu ta bar dakin

Babu abinda Ummie take inbanda dariya tace auuuu addu'ar ce baxaki amsaba shine Kika gudu Allah ya shiryaki Boddo
.......................

________________
DielaIbrahim ✍️
Vote pls 🙏

WACECE NI ✔Where stories live. Discover now