(New Part) Chapter 1

274 25 2
                                    

Wacece Ni?

Assalamualaikum
Am so sorry dudes, Na so na gama tun a part 2 but da alama hakan bazai yuba, so please kuyi hakuri ku cigaba da bibiyata a Wacece Ni? don jin karashan labarin.

Part 3/1

____________________Saudi_Arabia

Misalin karfe Tara muka Isa kasa Mai tsarki 9:00am
Alhamdulillah mun iso kasa mai tsarki cikin garin  Madina muka sauka muka kai gaisuwa ga kabarin Annabin Rahama Manzon Allah (SAW) kaman yadda sauran masu zuwa Hajji sukeyi ...muna nan zaune cikin masallacin Annabin Rahama bayan Hayatee ta gama waya Jim kadan akayo Kiran Hayatee awaya , driver ya fito yasanya kayanmu amota
Sannan muka Shiga Kai tsaye wani  gidan sama mai hawa akalla goma koma fiye da haka don ban tsaya girgawa ba agaskiya gidan ya hadu don ta lifter muka shiga ya sada mu da dakin namu,

Kwana mukayi a cikin garin madina washe gari Kuma muka dau hanya izuwa Makkah,
Anan ma appartment din mu ba karamin kyau yaimin ba, kowa ya zuba kayansa a wardrobe sannan na Shiga toilet MashaAllah na furta Lallai na shigo qasa mai tsarki saboda shi kanshi haduwan toilet din is different.

Da yamma misalin karfe uku da rabi muka nufi babban massallaci anan mukayi La'asar muka dan kewaya cikin massalacin muna yi muna hutawa har magrib yayi mukayi magrib mukayi isha'i sannan zuwa karfe Tara saura minti goma muka koma gida.

Munyi waya dasu Mamie Adda, Daddy, Ummie da Baffah Wanda sosai Baffah yayi Hira da Hayatee
Azuciyata nace lallai Baffah na ji da mahaifiyarshi, nace ya Allah kabamu Ya'ya masu Jin kan mu akowani hali muka tsinci kanmu.

Sannan muka kwanta, cikin dare misalin karfe uku da rabi ña farka nayi nafilfili Wanda har gabanin sallan asubahi, nayi sallah kafin zuwa shidda bacci ya kwacemin haka na tashi naje na kwanta.

***********

Sati biyu muka diba acikin garin Makkah, muna kai ziyara ko dayaushe Babban masallaci mai tsarki, sosai nake bata lokaci wajan rokon ubangiji damuwata, Ina yiwa Baba addu'a sosai sannan sai personal addu'ar da kodayaushe saina yita, Allah yaba ni miji nagari wanda zai kula dani har abada kuma wanda zuciyata take so, sai dai ni nasani cewa tafiya nakeyi acikin duhu batareda sanin inda na dosa ba, bansan wa zuciyar tawa take so ba, addu'a kawai dai nakeyi hade da barwa mahallici na komai.

Awannan sati biyun muka kara zuwa Madina kafin ranar Arfah,anan ma bakaramin godewa ubangiji nayi ba dayasa na kara taka kafa na izuwa garin madina Kuma naga kabarin manzon Allah (SAW), nayi addu'a sosai Kuma munyi duk abinda mahajjata ke yi, kasancewar mahajjata sun fara yawa sabanin lokacin da muka zo,Kuma su Goggo da Dije sun iso suma sai dai ba waje Daya muke dasu ba yanzu mukan je masallaci da wurwuri domin samun lokacin yin ibada kafin mutane su fara yawa aita cunkoso, haka dai mukaita zagaye ka'aba wanda tun tasowata ban taba tunanin zanga ka'aba ido da ido ba ballema har na taba Kuma na zagaye ta....Babu abinda zan iya cewa ko zan iya yi sai dai naita godewa mahallici na dayai min rahama acikin rayuwata.

***********
Ranar Arfah, muna garin Madina muna ibada ga jama'a dayawa,Bayan mun gama da daddare mun koma ne Ina zaune kusa da Hayatee Ina matsa Mata kafa , Mama Kuma tana gyara Mana wajan kwanciya Ummie ta kira wayan Hayatee, mun sha hira sosai Hayatee kuwa tace abata jikanta su gaisa, Haka na koma kallon ta naji kaman nace tabani saboda jin sautin muryarsa ta cikin phone din, har Hayatee ta gama Ina kallonta, ta kalle ni tace Boddo lafiya kuwa tunanin me kikeyi haka?

Saurin girgiza Kai nayi Ina cewa Babu komai Hayatee Ina kallon yadda kike magana ne, Abin Yana bani sha'awa na Kara sa maganar Ina kwakulo dariya, itama dai Hayatee dariya tayi tace ja'irah.

Jim kadan nace mata zanje na kwanta, tace min toh sai da safe don tasan na gaji sosai.....sai dai nagama Shirin bacci kenan naji
ringing din wayata, Koda na duba number Nigerian nagani Kuma bansan number ba, nidai tun zuwan mu daga Mamie, Daddy,Ummie da Hamid suke kirana bandasu nasan babu Mai number na Kuma babu mai kirana, Ina nazarin mai kirana har Kiran yayi cutting, na kwanta kenan aka kuma kira, saurin dagawa nayi nace
Assalamualaikum sannan nayi shuru,

WACECE NI ✔Where stories live. Discover now