Chapter 23

253 27 0
                                    

Wacece Ni?
Story written by
DielaIbrahim ✍️


Part 1/23

__________________________2days later Abuja______Maitama

Da marice likis....... weather garin yayi dadi kasancewar Ansha ruwan sama tun safe sai karfe biyu ya tsagaita.......
Irin wannan lokacinne masu kudi suke so saboda mafi yawanci idan gari yayi haka turawa naso  a iya bincikensu sun tabbatar da cewa kallon waje mai dauke da shukoki daban daban da flowers masu kyau da Kuma ruwa Wanda yake gudu da ainihin wato kukan tsuntsaye
Hmm Yana wanke brain kaji Duk want damuwanka takau.....awannan lolacin Hayatee ma tana garden hutawa takeyi saboda rahamar dake dauke da weather yau........awannan lokacinne take cemin Auuuuu na mance Ummie ta ce fah na kiraki ki Mata Hira kwana biyu Ummie tana jin dadin hirar ki......da alamu kaman xata kwace min ke

Nai murmushi nace aa Hayatee ke kaka ce Ummie Kuma ai uwa ce........Dagaske?

Mukaji maganan kwatsam daga Bayan mu______ Ummie ce da kanta tana sanye cikin Shiga na Alfarma dauke take da leda guda uku manya manya ahannunta

Nai sauri na nufeta na amsa incewa Ummie ce dakanta dauke da Kaya masu nauyi..........na amshi kayan nayi wajan Hayatee na ajiye inacewa gaskiya Fah kayan da nauyi.... sannan na maida kallo na ga Ummie nace
Ummie ki Dena daukan Kaya masu nauyi Haka
Ki ringa kirana Ina daukan maki saboda anfani na kenan agidannan nafada cike da kwazo
....... 

Mama wacce take doso inda muke tace ke dince Zaki iya ragguwa dake mAh ta fada tana min hararar wasa

Hayatee tayi dariya aa diyata ba ragguwa bace ko Boddo na

Nikam Ido na xuba ma kowannansu....dubi yanda kowa ke haba haba dani sun dauke ni kamar Daya daga cikin danginsu
Lallai soyayyah anan take...........na zurfafa cikin tunani 

Ummie tace Hajiyata takaina Hutawa kike

Eh Ummie Ina zuwa ne naganki da ledoji haka

Lahhh Ummie kayan da kika bani ne nabawa tela na...........

Ohhhhhh badai harya gama kayan ba ........Yagama wlhy

To nawa yace sai na tura Masa anjima..........Ummie Tai murmushi tace Hajiya ta ba saikin biya ba........ Hayatee ta dafa goshinta wlhy Nasan dole kibiya Ummie ke Kam Duk inda aikin lada yake sai kin aikata shi

Ummie tace babu komai Hajiyata
Yauwa gobe Ina son xuwa gidan
Adda and idan ba damuwa Ina so  Boddo ta raka ni saboda ta tayani Hira

Ohk tohhh badamuwa kice wa Adda nikam nayi fushi tunda yanxu mantawa takeyi dani yau sati biyu bansa Yar autata a Ido ba Kinga ko ta yada Ni

Ummie Tai dariya aa nasan Adda da dalilin ta.......saboda Adda indai wajan zumuci nee to xa'a Bata award....

To Allah ya kaimu goben.....   Mama ga kayanan na Boddo ne don Allah a xubar da wancen kayan nata...sannan Duk abinda take bukata karta ji kunya asanar dani......Mama tace angode Hajiya Allah ya saka da Alkhairi, Allah yaja nisan kwana

Hayatee dai murmushi Mai sauti

Na durkusa har kasa Ina mamakin mutane masu karamci
Hawayen da ke son zuba ne suka fara ambaliyan fito wa...........nace bansan dame xan gode maku ba amma kunmin abinda bazan taba butulce maku arayuwa ba
Nagode nagode Allah yasaka da Alkhairi natashi na gudu daki
Saboda kukan Daya kwace wa zuciyata da idanuwa na
..........

_______________________washegari
Misalin karfe 12 na Rana
Mungama shiri xamu tafi wajan Adda  ( Legislative Quarters) kamar yadda Ummie ta fada muna cikin mota

WACECE NI ✔Where stories live. Discover now