Chapter 22

261 27 0
                                    

Wacece Ni
Story written by
DielaIbrahim ✍️

Part 1/22

________________________
5:30pm

Na dawo daga gidan dije Ina cikin mota......motar Dana hau Kuma ta tsaya a daidai first bank
Wai motar ta samu matsala
Ana gyarawa
Nikam na sauqa na biyashi kudinshi na koma gefen titi Ina jiran wata  motar don hankali na yayi gida saboda Hadarin Dana ga ya hadu
Ruwa ake Shirin tsugewa dashi

Ina Nan tsaye ruwannan ya sauko ruwa sosai Wanda tuni na fara jikiwa
Saurin samum runfa nayi inda na bige wani mutun batareda na kalli fuskan Shiba na bashi hakuri na koma gefe Ina rawar sanyi

Tabangarenshi kuwa gani yake Kaman yasan yarinyar
Fuskanta ya sake kalla ta gefen Ido shikam ji yake Kaman itace yarinyar Nan Daya ke nema tsahon shekarunnan Kuma itace sanadin xuwan shi yau garin kaduna gashi yasamu bad luck
Tunda yaxo yake nemanta Amma Shuru kwatancen da akai mashi kwata kwata is wrong .......har an fara ruwan sama ,shikam  bayaso ya jike ne
Shiyasa yadan fake da gudu kawai xaiyi ya Shiga cikin mota
.............   

Tsahon minti Arba'in aka dauka ana tsuga ruwan sama
Tun muna mu biyu a runfar har muka xama mu biyar Mata biyu ne sauran Kuma maza.........

Ruwan ya tsagaita don Haka na Kama hanya xan wuce
Naji wani mutun nace wa
Don Allah baiwar Allah kudi nake so na cire shin kinsan wani bank ta cen gaba ban da wannan banking

Na waiga sainaga fa Dani yakeyi
Sai nace mashi Anya bana tunani sai dai ta bayanmu akwai GT Bank tacen gaba Kuma akwai Polaris bank kusa dashi Kuma akwai UBA Bank............

Ya tsira Mata Ido Jin yanda take furta ko wacce kalma da hausa Amma harshen Fulani gare ta Kuma Kai tsaye tamai kwatance........muryar ta tamai Kama da ita yarinyar don baxai manta taimakon dayai Mata ba
Wanda Sentence din da ta Fadi mashi kawai ya riqe  tundaga ranar ya riqe voice din.......baiyi tunanin yarinya Yar talla Kuma daga gani Basu da Hali Amma har ta iya wannan turancin
Tace masa Thank you you've done a such Favor you save mi life thank you so much tana kuka tabar wajan .....Bai samu ya tambaye ta Ina xata ba................

Malam Ina fatan ka gane Koh don sauri nakeyi xan wuce ta katse mashi tunanin shi

Uhmmmm to don Allah ta wajan xakiyi nee inba damuwa saina na rage maki hanya sai ki nuna min

Nai saurin cewa kayi hakuri bana Hawa lift na juya Ina tura baki

Kasaitacciyar murmushi yayi  yace ai ba lift bane  malama tunda  ba gida nace xan kaiki ba
Xaki nuna min nee saboda ban San wajan ba......kimin don Allah badan niba  ya had a hannuwansa biyu

Nace naji

Tunda nashiga motar bance mashi uffan ba shima Kuma Bai Kara magana ba sai dai na lura Duk Bayan minti biyu yakan juyo ya kalle Ni
.......... Muna isowa nace mashi yauwa nan ga Polaris ga Kuma  UBA
Mun wuce GT Bank cen baya kadan abinda yasa bance mu tsaya ba saboda Naga layi yayi yawa,,,Kuma ga dukkan alamu kaman sauri kakeyi , Amma Nan zaka iya samu  sai anjima
Na fada Ina bude motar nayi tafiyata ban jira yace min komai ba........
Tuni na tari taxi ya karasa Dani

.......................

Next day

Ranar da xan koma Abuja
11:30am
Driver yaxo muna ta bankwana da Baba da goggo
Ina rike da towel din da Baba yabani tare da turaren Almiski saboda har yau kanshi yakeyi baba yace kanshin Almiski nee tunda yaji towel din Yana wannan kamshin ya Tara kudi naira Dubu bakwai ya siya irin turaren  kwalbar turaren miski
Kullin yakan Sha fa turaren a towel din  shiyasa kamshin ya Tsaya

Mun Kama hanya kamar ko da yaushe yauma Bacci nee ya dauke ni Mai nauyi a mota
Wanda bani na farka ba saida naji horn sannan na farka......

Kut na Kama salati nace yanxunan Ina bacci har mun iso

Dariya driver yakeyi Yana cemin
Ai kinsha bacci............ya fada adaidai lokacin Yana ketare gate na uku muna Shiga ainihin gidan
Ina sauka ban tsaya kwashe kayana ba na ruga aguje nai ciki
Da gudu na Shiga flat din  a tsakiyan corridor din na tsaya Ina kwala masu Kira
Cikin minti biyu Naga Mama ta leko daga bisani kuma Hayatee ma ta leko.............ai acikinsu narasa wa xanje na rungume
Ina Nan tsaye Naga sunyo kaina suna murna

Hayatee tace Boddo Ashe xaki dawo dagaske gaskiya kin kyauta sosai......mama tace MashaAllah
Diyata ta dawo sannu da xuwa

Na nufesu da murna nace Hayatee, Mama nayi kewarku wlhy Baba Yana gaishe ku suka

Muna amsawa Yanxu diyar Mama taje tayi wanka ta huta ko
Nai murmushi Mai qayatar wa nace Toh Hayatee idan na Gama xan shigo

Tace toh Boddo sannan ta juya ta koma daki mu Kuma muka Shiga ciki nida Mama tana min sannu

Bayan na huta ne......Mama take cemin kije ki gaishe da Ummie yanxu sai kije wajan Hajiya
Nace toh Mama

Dan ta ma ya dawo ranar da kika fita yau Kuma ya koma da safe
Da kina nan da Kinga soyayyah a wajan Hajiya da jikanta......jiya ma Kam da kyar ta barshi ya tafi kaduna Wai zaije wani aiki wlhy Hajiya har kuka tayi Wai xata bishi......Mama ta karasa tana dariya sannan tace ba'ama zo wajan Ummie ba indai nuna soyayyah ce ga Dan nasu...............

Murmushi nayi Nace Allah Mai iko to shi Mama Ina yake xuwa ne?..........Yana kasar waje yaje karatun soja burinshi kenan tun yana karami shiyasa Daya gama karatu sai mahaifinshi ya Samar Masa sojan kasa ya tafi
Yanxu Yana cen....sai yanzu Allah ya bashi ikon zama soja...........

Nace Allah ya bashi sa'a
Ameen Mama ta amsa

...........,......

DielaIbrahim ✍️
Vote please

WACECE NI ✔Where stories live. Discover now