Chapter 23

300 27 7
                                    

Wacece Ni?

Part 2/23

_________________________Maitama,

Falon Baffah

Nabil zaune a qasa ya durkusar da kanshi yana sauraran Baffah
Sosai Baffah ke masa fada wanda
Fada dabi'ar Baffah ce Amma ba kasafai ya cika yiwa Nabil fada ba.

"Haba Nabil tun yaushe na Fadi maka kaje jaga yarinyar nan.....nida mahaifinta muna so mu tsaida rana, Amma kayi shuru kai bakaje ba Kuma kai baka ce komai ba, Toh ka tabbatar kaje ka same ta yau kafin raina ya baci."

"Toh Baffah ayi hakuri zanje inshallah, daga wannan maganan yayi Shuru baisake cewa komai ba tsahon minti biyar kafin yayiea Baffah sallama ya nufi part dinsa.

Mummy qarama ta labe a kofar baya tana Jin duk abinda suke tattaunawa sosai abin yayi mata dadi don dama ita take zuga Baffah da zancen auran Nabil, komawa daki tayi tana murna Baffah yayi wa Nabil tsawa abinda take fata kenan, uhmmm murmushi tayi sannan tace muje zuwa I'll show you my true color when am done with you all.

Yar'ta dake tsaye bakin kofar dakin ta, tana jiyo maganganun mummy, ta girgiza kai ......ita kam abu guda ta tsana wato Boddo wacce ake neman a shigo da ita gidan karfi da yaji bayan bawani relation dake tsaknin su, gashi kowa yafi sonta da ita, Wanda a da ita kadai take rausayawar ta a family saboda ita kadai ce mace.........ta Sanya hannu a harshe zamu gani.....ko they will succeed.

Abuddar baya qasan duk tsahon kwana kinnan, Baffah ya tura shi qasar sudan don ya kula masa da wani company dinsa, dukda baya da natsuwa, Amma mummy ta matsa akan Baffah  ya sakar wa  Abuddar Daya daga cikin company dinsa ko zai shiryu ya dena wasu abubuwa dayake yi........ .  Toh sai dai bamusan plan din Baffah ba akan haka yadai bashi ragamar company dake sudan Kuma ya zuba Masa Ido.

*************

Nabil ne ke ta faman shiri zai je gidan su yarinyar daaka matsa Masa  sai ya aura.......sai faman kumbura yake Hamid Kuma na ta mashi tsiya......

Bayan Nabil ya gama ya dauki car keys yace da Hamid idan ka gama dariyar sai kazo muje....Kuma wlhy inkayi wasa bazan baka kanwar tawa ba.

What...what Nabil No No Nooooooooo too it can't be possible......kasan yadda nake sonta ai kaman raina.....Nabil kasan matukar ban koma da Mata ba wlhy Ina komawa aure zasu min kafin na dawo.....,..just like you, shiyasa nake so mu daidaita....

Uhmmmmm kaji dashi, nidai sai ka lallabe ni tukunna

Wlhy zanyi koma miye kake so,

Nabil ya wurga Masa harara....muje kana Bata min lokaci.

Okay sorry my oga yafada Yana dafa bayan Nabil, dariya sukayi sannan suka fita gaba dayansu.

****************

Hayatee kuyi hakuri, al'amarin ne ya rikidar dani kwana biyu
Amma Ina bukatar explanation
Hakika tunda mahaifina ya rasu,
Nagano bani da Asali, kuma hakan bakaramin matsala zai janyo min ba wajan aurena, hakan yasa na fara binciken iyayena...(shine dalilin dayasa naje Niger State tsahon watannin nan dasuka wuce kafin ayi kidnapping dinmu......na yi bincike sosai Amma babu feedback, sai wata rana kwatsam
Matar Dana sauka agidanta take sheda min cewa tasan iyayena sakamakon Jin asalin sunana
Nihila Othman, daga nan ta hadamu da danta tace yakaini Amma ya tabbatar da cewa babu Wanda yagansa ko yasan daga inda yazo.shine a hanyar mu akayi kidnapping dinmu....Nabil da mutanensa su suka cece mu....Amma shi an komar dashi gida. Nayi shuru ban cigaba ba.

Adda tace wata matace wannan
Kinsan sunan ta.

Aa Mamie bansan sunan ta ba
Amma danta Mama yake ce mata"

WACECE NI ✔Where stories live. Discover now