Chapter 16

220 27 1
                                    

Wacece Ni?

Part 3/16

**************************

Rayuwa kenan, Rayuwa tafiya takeyi kaman kiftawar idanu,

Rayuwata ya canja sosai,Na koma
Nihila Othman Abdulrahim Amma wasu har yanzu da Boddo ake kirana,komai nawa na makaranta ne ya koma Nihila.

Ni da Yayana Nabil muna zaune lafiya ba' ajin kanmu,
Sosai muke nuna wa juna kulawa
Dukda cewa watan mu biyar da aure Amma babu abinda ya taba shiga tsakanin mu Amatsayin mu na ma'aurata, Nikam hakan dama bai dame ni ba, Yaya Nabil ya soma nema min Admission abroad zan cigaba da karatu a Manilla, Amma tare zamu tafi saboda yana so yaje yayi wani course awajan.

Yaya Nabil ya mikawa Baffah aikin Hospital dinshi da ake ta famanyi tsahon shekarunnan wanda sosai ake kawata hospital din,. Idan kaga asibitin zaka dauka akasar waje ne saboda tsahon lokacin da aka dauka ana ginawa Kuma wainda aka bawa contract din daga China suke, gashi dukkan abinda ake zubawa daga China akeyo order su,machine masu kyau irin Wanda babu su a Nigerian....Hospital din dai so MashaAllah.

************

Alhamdulillah na samu Admission...shiri kawai muka somayi mukayi wa su Hayatee bankwana dasu Dije da Goggo...har tsokanr dije nakeyi taki aure kowa yazo bata sauraranshi saboda ayanzu karatu takeyi itama Baffah ya saman Mata nursing school Kuma tana maida hankali sosai, idan kaganta ayanzu bazaka taba cewa ta taba aure ba ko tana da yara  saboda we are age mate Kuma babu abinda jikinta yayi illah hips da fari data kara tazama wata cikakkiyar mace itama.

Tafiya mukayi muka barsu Hayatee na rada min akunne cewa na tabbatar na dawo mata da great grandson.....Nikam nayi dariya abina, na bi bayan miji na muka shige jirgi.

****************

Bayan tafiyan mu Baffah yasa aka kama Abuddarr aka dawo dashi Nigeria,Baffah yaji zafin abinda Abuddar yayi baiyi nadama ba sai dayaga halin da mahaifiyar shi ta Shiga kafin ya soma nadama, amma sai da Baffah yayiwa Nabil magana, Nabil yasa aka kulle shi a guardroom na tsahon wata daya kafin aka fito dashi.

Maganar azaba kuwa Abuddarr yasha  azaba mara misaltuwa Koda ya dawo, tuni ya fara ganin kowa da mutunci ya dena shaye shayen dayakeyi, ya dawo mutum shiryayye, daga karshe Hayatee tasashi ya kawo mata ai masa aure amma ya ce baida ita su zaba Masa kawai.

Aiki da cikawa ai sai Baffah tuni ya nemo masa yarinyar abokinsa wacce akaso Nabil ya aura,haka aka daura masu aure ya siya mashi gida suka zauna lafiya abinsu.

****************
Too Short

DielaIbrahim ✍️

WACECE NI ✔Where stories live. Discover now