Chapter 16

242 26 1
                                    

Wacece Ni?

Part 2/16

The Next Morning
11:00am

Zaune nake Ina ta faman kallon kofa ko zanga Nabil ya shigo tun 5am dana tashi nake dokin barin asibitin nan na kosa inga Hayatee don bazan iya boyewa ba awannan lokacin ni karan kai nasan nayi kewan su gaba dayansu......wata na nawa bangan su ba.....ga kuma su goggo da Inna Wanda bansan awani hali suke ba barin ma Inna da ko digon tsananta babu acikin zuciyata nasan bata kauna ta Amma ta rike ni tayi dawai niya dani tun Ina jaririya....to mezai sa na juya mata baya aduk halin dana tsinci kaina....har yanzu Ina da alwashin taimakon ta aduk sanda Allah ya horemin .........na tsunduma sosai cikin tunani bansan lokacin da mutane zuka zagaye gado na ba....daga Kai kawai nayi na hada Ido da Nabil, uhmm babu abinda ya canja game da bugun zuciyata, ahankali na fara kallon sauran mutanen, doctor ne da nurse sai wani soja kusa da Nabil
Wanda ya kafe Ni da ido kaman ace dashi chas shi Kuma ya cinye ni,
Doctor na kalla na fadada murmushi na nace yaune Koh doctor..,. .

Doctor wanda sosai magana ta yabashi dariya yace wato nasha ganin patient da Basu son asibiti da injections but yours is different ace patient wanda baida lafiya Kuma yasan da haka Amma yake son assalame shi,you are impossible Boddo Abubakar....kekam wani irin tsana kikaiwa asibiti ne ?
Nurse tace tambaye ta dai doctor
Har kuka fa takeyi duk sanda zan bata injections.

Sojan da yake kusa da Nabil ya ce
Uhmm toh kunga laifinta tunda bata so basai abarta ba....ya karashe maganar Yana kallon Nabil da Ido daya.

Uhmm haka sukai ta maganganunsu Nabil kuwa ko kala bai ce ba....shi da surutun ma ya ishe shi sai ce ma sojan yayi Hamid kindly meet me outside along side with her when she is done ..........Okay kawai Hamid ya bishi dashi.

Ni Kuma nabi Nabil da kallo har ya kure ma ganina hakika Nabil daban ne acikin maza tafiyarsa da komai nasa daban ne dana sauran maza, ahankali na janye idanuwa na daga inda nake kallo
Saboda jin wani sabon abu wanda ya tokari zuciyata, besides bansan dalilin impressing dinshi dànake ba, "Huh🙄 I can't say,"  tashi nayi na hada kayana.......black leda na dauka bayan na Sanya hijab da wani cover......ban Ankara ba naji an rike ledar hannun nawa......daga Kai nayi da sauri ina mamakin abin sai naga Hamid ne kaman yadda naji Nabil ya fadi sunan.

Yace " Madam ban isa na barki ki dauki nauyi haka ba,kawo kigani"

Ban musa mashi ba na sakar mashi ledar Ina mai kallon doctor Ina cewa toh doctor na gode sai wani lokacin.....yace min toh adai kula da shawarwarin da muka baki, nace inshallah zan kula har mun fara tafiya Nurse tace Ni baza'aimin sallama ba Boddo?
Nawaiga da sauri nace lah aunty kiyi hakuri wlhy duk cikin zakwadin komawa gida ne.

Nurse tai murmushi tace it's okay safe journey koh......nace Mata Thank you sannan muka tafi.

Har muka isa inda sauran sojojin suke bamuyi magana da Hamid ba yasamin kayana a motan da Nabil ke ciki ya cemin kishiga koh.....Shi Kuma ya shiga driver seat.

Na Shiga na zauna ta hannun da Nabil yake shi Yana gaban seat dina, Ta mirror na hango shi wanda tuni muka hada ido zare idan nawa nayi kaman naga abin mamaki acikin mirror din daga bisani Kuma na matsa da sauri don na dena kallon shi....

Sosai abinda Boddo tayi yabashi dariya amma  dariyan bata fito fili ba cikin zuciya yayi ta... Sincerely speaking this girl is really really funny ya rasa mai yasa take sashi dariya atimes he really enjoyed her attitude towards him, kawar da tunaninta yayi a zuciyarshi sannan ya fara danna wayar shi, Hamid yasan Nabil baya hira a mota don haka bai matsa mashi ba kasancewar duk halinsu daya na miskilanci amma gwara Hamid akan Nabil.........ahaka muka fara tafiya babu hira sai zallan kida dayake ta faman tashi ahankali na wakokin India masu sanyaya zuciya, kamar ko da yaushe yauma baccin nayi a mota..........cikin ikon Allah Kuma ban farka ba sai da naji mutuwar  mota alamar an kashe mota....bude idanu nayi.....damamaki na ganni acikin gidan danayi akalla wata biyar bana cikinsa.....uhmmmm yanzu da wani ido zan kalli mutanen gidan.....mutanen da suka min hallaci ni kuma na butulce masu....wayyooo Allah ni Boddo kunyansu ma nakeji taya zan fara hada ido da Hayatee......Kara dukun kune wa nayi a cikin motan bayan fitar su.........tsahon minti biyu sukaji Shuru yarinya bata fito ba, Hamid yace lafiya kuwa

Nabil ya tabe Baki yasan shirmen  da ta saba yi shi take niyan yi yanzu.....is better ya wuce ya barsu idan ta gaji ta fito.har ya fara tafiya Hamid yace Nabil mana wait and talk to her nasan Kai tana Jin magananka.

Nabil ya katse shi da cewa kasan i don't take shit..... So I can't control my anger...what's the essence of staying inside the car....afterall she is awake ai and she knows that we've arrived... please you talk to her as for me am going in.

Hamid ya girgiza kai yasan halin abokin nasa juyawa yayi ya bude motar yace madam please come out.

Banyi niyan fita ba amma ayanda yai min magana  yasa na sanyo kafafuwana masu kumari da haske waje.......daga kai nayi naga ya tsira ma kafafun idanu.........bansan lokacin danai saurin sauko da hijab dina ya rufemin duka kafan ba. Nakan tuna Mufida friend dina a Nile University takan ce kafa na yana burgeta mostly maza sukan so masu irin kafan.........sai dije duk sanda akaimin kunshi dukda kafan ba fari bane haka kunshin zai amshi kafan yayi kyau sosai...dije kwana take tana kallon kafana atimes takan sa kanta wajan kafan nawa sai ta kwanta tayanda data farka zata ganshi....... murmushi kawai nayi

Nan yafara kame kame.........leda na na janyo ban rufe kofar ba na dallah masa harara sannan nai shige wata cikin gida Kai tsaye part din Ummie na nufa don agaskiya bazan iya tunkarar Hayatee awannan yanayin ba Ina matukar Jin kunyan abinda na aikata na barin gida batareda sanin su ba amatsayinsu na iyaye kaman yadda na dauke su.

Ina shiga kuwa adai dai kofan kitchen don ta baya na bi....naci karo dashi kayan hannuna suka zube kaina Kuma yayi masauki a kirjinsa......Ya Salam !!!! Ya fada Yana Mai kallon nonon kindirmo Daya zube masa a riga farar T Shirt dinsa..........

Daga Kai nayi da sauri Ina duba hijab dina dana ga Alamar Kindirmo ya zuba na jah da baya da sauri ina zare idanu ganin shima na bata masa riga, ganin  irin kallon daya ke bina dashi yasa nayi qasa dakaina ......... rufe baki nayi cikin tsoro na fara furta am so sorry please wlhy ban lura bane....don Allah kayi hakuri.......Muryar Ummie naji tana fadin Nabil ya nakeji kaman muryar Boddo, adaidai lokacin da take fitowa daga kitchen din.

Mamaki ya hana Ummie cigaba da magana tace Boddo............

Murmushi nayi na cire hijab din Jikina  na yar awajan sannan na kutsa ta gefen Nabil da gudu na rungume Ummie..........

Nabil yana tsaye zuciyanshi ya kawo sama kaman ya sameta yakeji ya wanke ta da mari amma wata zuciyan ta taushe shi ya wuce bai ko kula su ba.....Kai tsaye daki ya nufa yayi toilet direct Hamid na mashi magana Amma Ina ko sauraranshi baiyi ba.
Sai da ya kimtsa kanshi sosai yayi wanka kafin ya fito ya sauya wasu Kaya sannan ya nufi falo yasamu Hamid na kallo......yace ka tashi kaje kitchen din Ummie ka diba abinci malam don kai ba bako bane agidan.....tabbas Hamid ba  bako bane agidan su Nabil an mashi farin sani har kwana yakan zo yayi bayan sun gama force saboda duk inda akayi posting din Nabil to Hamid na gefen sa.

Hamid yace kwantar da hankalinka friend yanzu zanje nakai gaisuwa wajan Ummie da Hayatee..... Nabil yayi murmushi Jin sunan Hayatee

Yace to ni zan Shiga wajan Hayatee ne yanzu sai ka iso Koh.........Okay kawai Hamid yace ya cigaba da kallonsa.

*********

Na Kama Ummie na kankame ta na ki sakin ta.......Ummie tace Boddo Ina Kika Shiga babu irin nemanki da bamuyi ba.

Murmushi na Kuma yi nace babu Ummie Ina gida.....Ummie tace ban yadda ba Boddo kije yanzu ki huta ki gaida Hayatee anjima kyazo ki fada min abinda ya sameki....na gyada kai sannan na ce Ummie Ina Jin kunyan Hayatee don Allah ki raka ni kinji na kama hannunta ina rokonta
Cute smile Ummie tayi tace Boddo kenan muje toh.
Na kwashi kayan nawa mukayi part din Hayatee.

************

Vote!Vote!Vote!!!!!
Please

WACECE NI ✔Where stories live. Discover now