Chapter 9

226 25 10
                                    

Wacece Ni?

Part 3/9

_________________________Sudan___

Sir zai iya yuwuwa abinda Nabil ya fada gaskiya ne, mu duba mugani amma we should be very careful cewar Hamid Yana tallabe da kafadar Nabil wanda daka gansa kasan Yana bukatar kulawan doctor.

Hamid ya zaunar da Nabil a wajan inuwa yace ka huta aboki bari mu duba wajan Koh

Nabil cikin jarumtaka yace okay Dan uwa be careful idan kin samu wajan sai kazo ka tafi dani

Okay

Haka suka bazama suna duba inda yakama ta su Shiga wajan.....Allah cikin ikon sa Hamid yayi nasaran samo whole din babban whole haka suka fara shiga Daya Bayan daya , Hamid ya koma ya dauko Nabil Suma  suka fara Shiga zuwa wannan lokacin Nabil Yana iya tafiya dakanshi saboda shi sadauki ne.😜don haka Hamid ya sake shi suka fara aiki.

Ahankali suke dira cikin ramin wanda zaka yi mamaki idan akace maka gida ne aka gina acikin kasa Kuma mutane suke rayuwa aciki.....wato wasu mutane ne daga America da mugun yawan su, suka yada zango a wannan rami, lokaci zuwa lokaci suke Shiga kauyukan Sudan sukai masu farmaki, sukan kwashe dukkan dukiyoyin mutane want zubin kuma sukanyi kidnapping mutanen.
****

Basu ankara ba sukaji karar tashin bomb wajan sai da ya girgiza sojoji sama da goma suka kara shekewa, yawu Hamid ya hadiye Yana mai Jin zafin yan uwansu dasuka rasa...mutanen suka fara fitowa Daya Bayan Daya da wata irin bindiga mara Kara sosai sai dai kawai kaji saukanta ajikin ka, lokaci daya Suma suka soma harbin...jibkake kawai ana kashe kashe
Nabil da Hamid sun matukar kwarewa a aikin su don haka suka dage suna ta harbi sai da ya zamana ba a Kara kashe masu mutune ba.

Successfully suka kawar da gaba Daya mutanen wajan sannan suka Shiga ciki nanma dai wani bomb dinne ya tashi wanda da kyar su Nabil suka sha sunyi sa'a babu wanda ya mutu,  suka soma harbin Suma har saida suka kawar da Duk wani makiyin su, daga karshe suka firfito da mutanen waje suna fita 1 after the other, sai da suka gama fitar da mutanen sannan sauran sojojin Suma suka soma fita Amma me zai faru sai jin girgiza kasan wajan  ya fara sauko masu yana rufesu...Nabil nee yake ta kokari Yana taimakon sojojin suna fita, sai da aka zo kansu ne kasar wajan ta burma sai wani hanya da suka samu....abin tausayi Ogan su ya mika hannun kenan Yana cewa Nabil ya fito Amma hankalin Nabil Yana wajan Hamid Wanda dutse ya danne rigan shi ga kasa tana ta saukowa tana rufeshi, Nabil yayi namijin kokari ya sauko ya cire Masa maballin rigan kakin soja ya janyota ahankali ya rike ahannunsa,.....Hamid ya mika masa wani takarda fara Wanda ya ciro acikin aljihun wandan sa yace ungo aboki kawai kada ka damu kaje, Ni Ina ganin nawa yazo karshe, yana hawaye Yana cewa Aboki idan ka koma gida ka kula da Boddo, kamin Alkawarin zaka sata farin ciki har iya tsayin rayuwarta...Aboki Allah ya sada mu a waje mafi Alkhairi wato Aljannah.........Yana kaiwa nan wata kasa mai yawa ta rufe wajan daya kamata ya biyo,
Nabil ya zare idanu yana Kiran sunan Hamid da karfi Amma Shuru Hamid bai ansa ba, mamakin faruwar wannan ala'amari Nabil yake shi fa har yanzu bai yadda ya rabu da Aboki Kuma Dan uwansa ba, Idanuwansa sun kafe waje guda ya dena jin maganin kowa,da taimakon Ogansu ne da wani soja suka janyo shi ya fito daga wajan, baya motsi ko kadan Shidai kawai ya zuba wa kasar ido Yana tunani barkatai acikin zuciyar shi.

Suna zaune awajan tsahon minti goma ana bawa kowa ruwa Yana sha, kawai sukaji Nabil ya kurma ihu gami da dafe kanshi.......Duk da yaso hawaye su fito a idanuwanshi don ya samu saukin ciwon dayakeji amma Ina idanunwanan sun kafe babu ko digon ruwa atare dasu, Ogansu nee yake ta faman lallashinsa yana bashi hakuri sun jima awajan Amma Basu ga alamar Hamid nada rai ba, sun so su duba amma babu hanyar da zasu shiga sai suka hakura suka tafi Nabil kam ya koma kaman wanda cutar barin jiki ya sameshi baya  magana baya komai, janshi kawai akeyi, ya rike rigan Hamid gam da hannu daya, dayan hannun kuma takardar da Hamid ya bashi ita ya rike gam.

Wannan kenan.

**********************

Ina zaune akan sallaya tsakar dare Ina nafilfili Ina ta Addu'o'i....naji gaba na ya fadi lokaci daya Hamid da Yaya nah suka fado min araina....Na fara karanta
Hasbunallahu wa ni'imal wakil, Lahaula wala kuwata illah billahil aliyul-azeem.

Haka naita Addu'o'i kala kala har wayewar asubahi.

Da sassafe kuwa naga Kiran Mamie Adda na daga, tana tambayana Ina lafiya nace mata eh lafiya lau nake, me ta gani ne......Hamdala tayi sannan tace min tayi mummunan mafarki ne game dani Amma yanzu jin muryata hankalinta ya kwanta.

Nace Mamie kina sa damuwa aranki dayawa shiyasa, Mamie ki rinka taya ni da addu'a kawai da Kuma Allah ya dawo dasu lafiya, kinji Mamie nah

Tace toh Boddo sai anjima zamuyi waya Koh.

Nace toh Mamie ki gaidamin da Daddynah

Okay zaiji.

*******************

Bayan faruwar haka da wata daya.
Wata rana su Mamie suka kawo mana ziyara Adamawa, nayi matukar farinciki da na gansu kwanansu biyu a Adamawa sanna suka fara shirye shiryen komawa Abuja, har Dada nacewa ko zasu tafi dani Amma Ina sam Hayatee ta hana Wai Mijina bai bani izini ba. Ina ji Ina gani suka koma abinsu.

********

Abuja

Bayan su Hayatee sun koma ne da sati daya sai ga Nabil ya dawo,
Baya cikin hayyacinsa don ko magana bayayi da kowa..daka ganshi kasan yana cikin damuwa...wato abinda yayi taking dinshi so long kafin ya dawo acen Sudan shine.

Bayan sunyi nasarar barin sahara din suka taimaka wa mutanen dasuka ceto da kuma masu laifi duka suka  mikasu zuwa ga gwamnatin qasar Sudan, an sara masu Nabil matuka tare da kyauta mai tsoka,.....shi Kam ma bai da lafiya hakan ba damun shi yayi ba, sai mutanen da aka ceto aka basu kudi dakuma wajan zama don ahalin da suke ciki suna bukatar taimako.

Sauran Sojojin gaba daya suka dawo Nigeria amma banda Nabil acewar shi zai kara jira yaga ko zai samu Hamid don bazai iya komawa gida batareda Dan uwansa ba....sai da ya koma  sahara shi kadai ya bincika sosai Amma bai ci karo da konai na Hamid ba....Baisan dalilin dayasa mind dinshi yake bashi cewa Hamid ba mutuwa yayi ba, dukda kowa yasan yadda kasan wajan tayi rugu rugu dole ne mutum ya mutu idan yana ciki.

Haka dai saida Nabil yayi wata Daya da sati Daya kafin ya koma gida.

Baffah babu yanda baiyi dashi ya fada masa damuwarshi amma ya ki fada sai faman nuna masu Riga da takarda yakeyi.

Daga karshe dai Baffah ya amshi takardar ya bude yana karantawa......sosai abin cikin takardar ya bashi mamaki ya kalli Nabil yace
Nabil kayi magana Ina Hamid Kuma miye dalilin sa na rubuta wannan bakar takardar,

Nabil da shidai tunda aka bashi takardar bai iya budewa ba, sai dai yaita kallon ta kawai, ya girgiza kai sannan ya furta Baffah miye acikin takardar..... cikin muryar tausayi.

Hayatee da Ummie hankalinsu yayi matukar tashi suka ce Baffah mecece acikin takardar Wai?

Baffah ya mika masu Yana cewa bazan iya fada maku da Baki ba ku ansa ku karanta.

Suka amsa suna karantawa sun girgiza Suma sosai suka kalli Nabil suna kara tambayan shi abinda ya samu Hamid har ya rubuta wannan takardar.

Nabil dai yakasa furta Koda kalma daya haka suka sallameshi ya tafi dakin shi washegari kuwa saiga su Daddy da Adda hankali atashe haka ranar aka yini ana tambayan Nabil Amma babu amsa ko kallon su bayayi.

Me zai faru ai sai Ummie takama kuka tanacewa , mutun ya dawo kaman gawa, ita kawai akaishi asibiti a duba mata lafiyar danta.

Haka kuwa akayi Koda aka kaishi asibitin likitan ma cewa yayi wani abu nee ya tsorata shi,Shiyasa ya dawo haka, Amma zai daura shi akan magunguna da sannu zai samu sauki Inshallah.

*********************

Vote!Vote!!Vote!!!
Please

WACECE NI ✔Where stories live. Discover now