Chapter 19

223 26 1
                                    

Wacece Ni

Part 3/19

The next morning

Muna zaune muna breakfast nake cewa Nabil zansa a dauko twins saboda junior, shikadai anan bazai sake yanda yakamata ba.

Nabil yace to adauko su amma ba Dade wa zasuyi ba kinsan itama Mamie itakaidaice ce Kuma yanzu ta Saba dasu sosai.

Nace alright ba damuwa.

Muna gama cin abinci kuwa na tura driver ya dauko su amma saida na fara Kiran Mamie  na shaida mata komai kafin ta yadda.

Aikuwa dawowansu yasa Junior kara sabawa anan naji Yana m zuba turanci kaman an aikosa nace da Nabil you see jiya kuwa ko surutun shi ba'aji sosai, kaga yanzu dole ya sake dasu kuma ya Kara sabawa damu.

Nabil yace yes you are right.

*********

Hamid kuwa kullin sai ya kawo mana ziyara wani zubin su fita shida Nabil suje yawan shakatawa har yaran suke diba, nikam sai abarni Ni kadai agida.

Wani ranar Sunday weekend suna gida suna hutawa,Yara na falona suna wasa, nikam Ina kitchen Ina hada snacks (meat pie,cake and pizza) with fruit salad.

Naji sallama waigawan dazanyi Naga Dije wanda ayanzu ta mayar da sunan nata Deeja...Wai ita Yan Mata.

Rungumeta nayi Ina cewa nifa da nayi fushi dake ne, ace tun dawowar mu ko kizo kiga Yar uwarki, nasan dai goggo bazata hanaki ba.

Dije tayi dariya tace haba sister,wlhy nima Inata son zuwa
Kinga abubuwa sun min yawa ne a Yan kwanakinnan, kin san Ina business Kuma daga China nakeyo order kaya, toh shine fah kikaga duk na zama busy dayawa, am so sorry dear.

Uhmm ba komai na gode ma da Kika Zo dama Ina son ganinki,amma Taya Ni aikin nan idan mun karasa sai muyi magana Koh.

Okay Ni wlhy Nihila kina bani mamaki ace duk girman gidan nan Baki da mai maki abinci sai dai wanki da wanke dishes, ke Wai baki son wata taiwa mijin ki abinci, uhmm ko dayake hakan ma yayi kina da gaskiya

Kema kin sani dije darajar mace shine iya girki da tsabta a gidan mijin ta.....Taya zanyi sake da wannan damar, saboda kudi bazan iya sakin ragamar gidana wa yan aiki ba wlhy.

Yayi Mrs Nihila Oth........

Aa karki Kuma wannan a waje ne Amma cikin gida kuwa Mrs Nihila Nabil Yusuf nake.

Ah AhAhAh.....yayi Yar gidan Nabil, Allah yaja zamaninki, Allah ya barku tare

Ameen Summa Ameen

Haka mukai ta hira har muka karasa aikin muka jera komai a dinning, sannan muka same su a falo.

Nace dasu toh sai a aje hirar hakanan azo aci abinci Koh.

Nabil yayi murmushi, Hamid Kuma yar yace toh madam gamunan zuwa.

Bayan duk mun zauna a dinning da yara sai faman surutu, tsawa na daka masu nace suyi Shuru kowa yaci abinci....shine fa muka samu sa'ida.

Bayan mun gama cin abinci ne, muka kebe nida Dije nake shaida Mata Asibitin Nabil ya kammalu, Kuma ahalin yanzu ni ce zan bude asibitin idan aka zo yin walima.

Nace dije kema kinga zaki fara aiki a hospital din sannan so kije ki fara shiri. Sannan ya maganan aure

Uhmmm Boddo kinsan me bawai bani son auren bane Amma Duk samarin dasuke zuwa guna, wlhy basuyi min ba, infada maki kowa da irin tasa matsalar Kuma sai suyita nunamin suna da kudi, suna zaton zan sosu saboda kudin su ne.....Ni kuma ba haka nake ba wlhy.

Toh nidai shawaran dazan Baki yakamata kizauna kiyi tunani, you have to get married again.

Inshallah zanyi tunanin nagode.

Muka fito zan raka ta mota don ayanzu dije tana da motar kanta wanda da kudin datake sana'a ta siya....bayan ta tafi ne Hamid ma ya fito zai tafi shima junior kwata kwata yanzu ya dena kukan zai bishi tunda yasaba da twins, mukai mashi sallama sannan muka koma ciki.

Da daddare muna dinning room muna having dinner, Nabil yake cemin Yana da wata shawara why not a hada Dije da Hamid aure, don kaman hakan shi ne best solution for both of them.

Nace kwarai Kuma fah ya kawo shawara amma ya fara tuntuban Hamid in yaso sai yaje yayi campaign da kansa, don idan nasa baki ba Lallai dije ta amince ba.

Nabil yace kuma hakan ma yayi Bari I will talk to him tomorrow at the office inshallah.

Allah ya kaimu kawai nace , sannan muka sauya hira har muka gama cin abinci muka koma falo.
Washe gari kuwa Nabil ya tunkari Hamid da maganar... Hamid yaji abin kaman almara amma daga karshe yace wa Nabil alright zanyi shawara da zuciya ta .

Anan suka bar maganan.

Koda Hamid ya koma gida babu abinda yake tunani sai shawaran da Nabil ya bashi......daga karshe ya amince da shawaran abokin nasa.

***************

Vote!Vote!Vote
Please

 

WACECE NI ✔Where stories live. Discover now