Chapter 20

381 25 10
                                    

Wacece Ni
Part 3/20
Last Chapter
Last Update

______________________________________
ABUJA

Hamid yaji shawaran abokin sa, ya samu Dije yai mata magana cikin fahimta....da fari taso taki amincewa da hakan, Amma daga baya kowa ya daura ta akan hanya, tuni ta saduda ta amince da auran Hamid.

Cikin sauki suka fara shimfida soyayyar su har takai ga suka sako manya cikin maganar, sannan aka sha shagalin biki, Itama sai da aka kaita Adamawa kafin daga baya suka dawo Abuja, gidanta Yana kusa da namu babu wani nisa a tsakanin mu, Twins da Junior ma har sun Saba tare da Nabil suke takawa suje gidan.

Hakika zumunci ne mai karfi ya Kara kulluwa atsakaninmu, ga kuma aiki da muka farayi a hospital din Nabil wanda nice in charge of everything a hospital din.

*****************

Bada jumawa ba Dije ta fara laulayi, ana haka Nima nabi bayanta tare mukayi laulayin cikin mu har yakai ga watan haihuwa, Allah cikin ikonsa duk maza muka haifa....Nabil ya rada wa baby na sunan Hamid muna kiransa da Ayman, shi Kuma Hamid yayi wa Abbansa takwara.

Haka Allah ya canja min rayuwa ta, nakoma kullin cikin farin ciki, Duk inda na waiga masoya nake gani, Hayatee, Ummie, Mama, Goggo da Kuma Inna
Sai Babban su wacce ta raine ni tsahon wata tara a cikinta wato Mamie nah
Hakika babu abinda zance sai godiya Mai tarin yawa ga Allah madaukakin sarki.

Su Goggo babu abinda suke cewa sai Allah yayimin Albarka nice silan canjawar rayuwar su, kullin godemin sukeyi barinma Inna da ayanzu garau takejinta.

A dalili na kuwa Family din yakara yin suna, ga jama'a,  Baffah da gidan Daddy kuwa ako dayaushe Albarka suke sakamin, so da dama sukance nice Hasken Family dinsu.

************
Bangaren su Lailah kuwa
Mummy ta rasu, Lailah Kuma tana da yara biyu, Abuddarr ma haka, Suma ayanzu mun kara sabawa dasu saboda sosai suke kawo mana ziyara tare da ya'yan su.

*****************

Yau ranar Sunday ranar weekend, muna gida nida Nabil, Yara Kuma tun ran Friday daga school ya kaisu wajan Mamie.

Ina kitchen Ina kokarin daura lunch naji anyi hugging dina tabaya, murmushi nayi saboda nasan oga na ne,

"Nace Nur kana so ka razana ni"

Kyakkyawan murmushi yayi sannan  yace taya zan razana farin cikin rayuwata,ahankali ya dinga manna fuskar shi da tawa yana wani goga min hancin sa a fuska, zamewa nayi ahankali na gudu da wayau Ina cewa Nur bazaka barni nayi aiki ba, I have to hide gaskiya......kafin na rufe baki tuni ya janyo ni na dawo jikinsa na kwanta a faffadan kirjin sa, Yana cewa ofcus kamar yadda Kika fadi gaskiya I won't allow you to continue with your house chores, fita zamuyi yanzunnan.

AhAh Nur dina Ina zamu Kuma?

Uhmm yau weekend fah, Kuma kinsan yau ranar hutu ce so zamu fita yawan shakatawa.......

Tsura masa idanuwa nayi, Nabil komai nasa daban ne, magana yakeyi Amma kai mai sauraronshi sai ka shagala wajan kallon yanda yake magana,at the end ka kasa fahimtar komai.

Nace dashi, how about this close your eyes and stay in one place...Bayan yayi dariya ya kulle ido sannan Ni kuma nace cikin muryan shagwaba Yaya na, shikuma Yana amsawa cikin sigar jan hankalin wanda akai mawa,  Ina yi Ina ja baya, na kuma cewa Nur dina, har dai nakai bakin kofa daga bisani nace time out na gudu nabarshi a tsaye.

Ya bude ido yaga batanan murmushi yayi kawai shima yabi bayanta.

Yawo muka dingayi cikin garin Abuja,Munyi annashuwa sosai wanda ya samar mana da farinciki....bamu koma gida ba sai karfe shidda na yamma.

Ni diela mai rubutu na nemi waje na zauna tare da bude wani page Ina shirin cigaba da rubutun Wacece Ni?..  Amma ko dana daga kaina sai Naga Nabil ya dauki matar sa cak yayi dakinsa da ita suna ta faman kallon soyayyah ma junansu. Ji nayi Nabil ya rufo kofa da karfi...ya barni da sakakken baki Ina mamaki, cen naji kuma anbude kofar....ba kowa bane illah Boddo kyafta😉 min idanuwa tayi hade dayimin gwalo 😛 sannan tace dani.....yakamata mai tubutu ta tafi gida taje ta huta saboda da alama alkalami da littafi sun gaji da long journey, don idan suka biye ta labarin Wacece Ni?toh watakil nan gaba sai mai rubutu ta nemi ta bude company wallafa littatafai, domin Labarin Wacece Ni bazai taba karewa ba harsai idan characters din ciki sun koma ga mahallincinsu...... Bissalam

Boddo taja kofa ta rufe gam, Nikuma DielaIbrahim ✍️ na tashi na nufi hanyar fita zan koma garinmu  domin journey dina yazo karshe,har nakai wajan mota ta ina Shirin budewa , sai na hangi Hayatee,Baffah,Daddy, Ummie, Adda,Mama,Goggo,Inna,Dije,
Hamid,Lailah, Abuddarr,Twins, Junior and d rest suna daga min Hannu 
Suna min bankwana, Nima dai daga masu hannu nayi sannan nashige motana na bar gidan.

Sannan na bude littafi na, narubuta
Tammat - bihamdulullah!!!!!!!!!!

********************

Toh masu karatu nan dai na kawo karshen littafin WACECE NI?
Mallakin DielaIbrahim ✍️.
Mai sharhi,korafi, da Kuma masu bukatar complete document kune me ni ta What'sApp Number na :
07031086858

Sai kuma mun hadu a sabon littafi na mai taken Baqar Mace masoya na ku cigaba da bibiyata inshallah zan kayatar daku da Labarai masu dadi,nishadi, kayatarwa da kuma ma'ana.

Baqar Mace Labari ne wanda zai zo maku da salo daban daban na rayuwar da wata (Baqar Mace) take fuskanta. Idan kuna bukatar Jin labarin ku saurare ni yana nan tafe da yardar Allah.
***************

Check out my novels please
~UMMI ƘWARAS~
~RAYUWAR JIDDAH~
~NAJMAH~
~AL'ADARMU~
DielaIbrahim ✍️
07031086858
Bissalam

WACECE NI ✔Where stories live. Discover now