Chapter 6

252 22 0
                                    

Wacece Ni?

Part 2/6

________________Kaduna State____
________tsakiyar garin kaduna
________ poly road______10:20am

A titin poly road daidai second gate na Yusuf Dan Tsoho Memorial Hospital hold Up nee a wajan kasancewar kodayaushe xaka ga wajan a tunkushe
Saboda makarantar dake opposite hospital din,kowa dai harkar gaban sa yake.........

Awannan lokacinne yake tafe acikin motar sa yana danjin sautin kida na wakar Veer-Zaara
Wakar India Mai matukar Shiga rai...........Motocin kwata kwata basa moving saboda ana sauke Yan makaranta ga Kuma masu tsallakawa
Ta gefe guda cen tsallaken titin ya hango wata yarinya Mai kimanin shekara 13 xuwa 14
Tana kokarin tsallaka titin Amma da alamu tsoron titin take Kuma harda Lodin bokitin dake saman kanta.......yakai dubansa gare ta

Sanye take da atamfah Riga da Zani atamfar ta Dan tsufa kadan Amma daka ganta kasan a tsabtace take saboda komai nata neat yake.........har ya juya sun fara tafiya ya waiga sai yaga still yarinyar bata tsallaka ba..........gefen titi ya koma yayi parking ya fito cikin sauri ya Isa gare ta..........,........

Tana tsaye taji mutun yakama hannunta ta daga Kai ta kalle shi
Sai taga bature fari Sol tai saurin kauda kanta gefe acewar ta Wai kila aljanine saboda kyansa ya wuce misali........Yana tsallakar da ita ya juya ya wuce abinsa Bata bi bayansa da kallo ba itama ta cigaba da tafiyarta.............

Abangaren shi kuwa Bayan ya Kama hannunta nee yaji wani irin Shock......yakai dubanshi ga hannun inda yayi tozali da zoben dayayi wa kyakkyawan yatsunta kyau....har ya tsallakar da ita hannunta yake kallo.........Bayan ya koma motane ya cigaba da tunanin yarinyar har ya Shiga office ..........karfe biyu ya tashi daga aiki Yana fita kuwa ya hange ta zaune tana ta faman dauraye plate tana sasu cikin farin bokitin dayaganshi cike da abinci da safe Amma yanxu Kam harta siyar...........ya wuce don shi Kam baisan dalilin kallon nata ba.................

...........the next day dayaxo ma haka yaganta sai Daya kwashe kwanaki Yana haduwa da ita Amma Bai taba yi Mata magana ba........

_________________wata rana da karfe 2:30pm

Nabil ya gama aiki xai tafi gida
Yana Hawa motar yayi key taki kunnuwa ya rasa mece ce matsalar sai ya fita don duba masu gyara kodaya dawo Bai samu mai gyaran ba Yana tsaye wasu nurses suka rogo wajansa suna neman dauki
Likitan Daya kamata ya xo Bai iso ba ga Kuma wa'insu sun fara labour ............

Da har zaice kujirasu man su karaso sai ya tausaya masu yashiga.......Ranar bashi ya fito ba sai karfe (7)bakwai already dare yayi ya nufi ta baya Yana so yayi alwala yai salla kafin ya wuce
Mai gyara ya fara Nemo wa yana gyara Mai shikuma Yana sallah agefe...............Yana idar wa maigyaran yace oga sai ansa ruwa yace ohk Bari na zagaya tabaya akwai ruwa

Yadau gora ya kulle motar ya nufi wajan, ya gama diban ruwanne  ya juya zai tafi yaji motsi.......Amma Koda ya waiga baiga kowa ba sai yayi tafiyarsa.........    Ya tafi yakaiwa Mai gyaran ruwan tuni ya xuba successfully motar ta tashi......

Nabil ya Shiga mota yafita sai yaga ana masara tacen gaba Kuma Ummie tana son masara gasassa.........tsayawa yayi  sai matar tace Masa xai Dan jira akwai layi...........ta wani bench ya zauna Yana jira
Kwatsam sai ya tsinkayi hiran da wasu samarika sukeyi su biyu suna zaune kusa dashi

Dayan yace abokina
Ina gaya maka anjima akwai Mai zafi fah

Abokin yace Haba mutumina
Yace wlhy Ina gaya maka

Ina wata yarinya xaka ganta Bata magana cikin masu tallan Nan

Abokin yace nagane ta wacce muke Hari dinnan
Yace yauwa Ashe kagane to ita
Ina gaya maka

Sai yayi kasa kasa da murya yace tana Bayan asibitinnan
Ni kadai nasan inda take
Tunda Rana Rabi tai min hanya na kamata sannan na rufe mata baki
Yanxu jira nake  anjima yayi nee
Kasan lokacin komai yayi tsit
Kai mutumina ku dinfa kun iya wlhy gaskiya xan Shiga tsahu anjimannan saboda yunwarta nakeyi Yasin
To ba komai dama nikadai nee

Tana Ina nee ?
Saurin me kake kabari xamuje
Tana ta Bayan asibitinnan
Wajan ciyayi babu Wanda xai it ganinta

Nabil na tsaye ana Sanya Masa masara ............har zai wuce sai ya saurara yayi kaman Yana waya yadinga Jin maganganu
Har ya dago zancen su wato wata yarinya suka Kama xasuyi wa fyade.........  Lallai yau baxa shi gida ba sai ya taimaki koma wacece..........  Abin ya matukar bashi mamaki kana nan Yara amma suna wannan harka
Allah ya shirya su.........................
Baibar wajan ba  saida ya Kira police station yai masu kwatancen inda xasu tsaya a boye......sannan ya ji dayan nacewa

Abokina Bai kamata mu aje ta a wajan ba kamata yayi muje mu dauke ta saboda Idan akaje yin fitsari ana iya ganin ta

Yace Kuma fa hakane tashi muje
Amma Ina kake ganin zamu kaita ?

Mukaita dakina tunda Yana kusa nee

Toh shikenan

Suka tashi secretly suka tafi Nabil na binsu abaya har suka Isa wajan Yan sandan ya Kira suka biyo shi abaya suka boye ta inda yaran baxasu gansu ba

Saida ya Shiga ya dauko yarinyar
Tare da taimakon abokin wajan babu kowa sai Motoci dake wucewa kadan kadan.........suna fitowa sukayi kasa da gudu suna sauri......ita Kam sai wutsul wutsul takeyi tana so tayi ihu Amma an rufe Mata baki

Basu Ankara ba suka ga mutane agabansu......ba shiri suka saketa ta Fadi kasa suna Shirin rugawa Amma Ina tuni Nabil ya Kama su ya sharara masu Mari biyu biyu sannan aka kamasu

Yarinyar yaje ya bude wa baki ...ya kwance Mata hannu
Duhu yayi baya ganin fuskanta dakyau Kuma ba abin ya dauko wayar sa ya haska ba
Yansanda sun so tafiya da ita
Amma Nabil ya lura kuka takeyi
Da Kuma tsoro atare da ita

Yace su tafi dasu kawai ita abarta taje gida
Tuni ta ruga xata bar wajan
Amma sai ta tsaya taimashi  godiya .tana hawaye sannan ta bar wajan da saurinta.......

Nabil na tsaye yaso ya kaita gida Amma yaga Alamar atsorace take
Ya girgiza Kai yace Allah sarki
Ko ya iyayenta zasuji............igiyar da ya kunce Mata hannu ya jefar sai yaji wani abu ya rike mashi wando a jikin rope din

Dubawa yayi sai yaga zobe (ring)
Heeee this ring look's familiar
Harya koma gida Yana tunanin inda ya taba ganin ring din

Sai washe gari Bayan yaxo asibiti ya tuna ring din yarinyar Nan dai Daya tsallakar titi.......kenan it ya taimaka mawa jiya da daddare........... hmmmmmmm

..................
DielaIbrahim ✍️
Vote pls 🙏

WACECE NI ✔Where stories live. Discover now