Chapter 16

266 28 0
                                    

Wacece Ni?
Story written by
DielaIbrahim ✍️

Part 1/16

___________________________________
Abuja

Kamar kullin yauma na gama Duk aikin Daya Dace.......Nayi ma
Hayatee sai da safe kasancewar
Karfe goma lokacin
Don ita har tayi Shirin kwanciya
Na rufo Mata kofa
Taku biyu na qara Domin xuwa dakinmu

Amma sai ji nayi an damki hannuna an janyo ni zuwa wani corridor din hade da toshe min bakida hannu
Dukda dare yayi, An kashe wutar corridor din
Amma Ina iya gani fuskanshi saboda hasken farin wata Daya haska wajan  daga tsakiyar corridor din wajan a bude yake
Shi Kuma Yana kokarin fadin
Shhishhhhii 🤫
Alamar karnayi ihu

Tsayawa yayi sannan yace ki nutsu magana kawai xamuyi

Sosai abin yaban mamaki
Meke Shirin faruwa Kuma Dani
Ina cikin zaman zamana
Hankali na kwance......

Katse min tunani yayi da cewa
Miye sunanki

Banyi niyan tanka mashi ba
Amma ahankali na furta
BODDO

wow wat a nice name
Amma dai ke ba Yar aiki bace
Don dagani bakiyi Kama da masu aiki ba

Nidai tsoron sa nakeji
Jikina na kyarma muryata na rawa da kyar na samu nace dashi
Bawan Allah me kake nema nee
awaje na

Shhishhhhii 🤫 ya qara cewa nai Shuru
Cen Kuma yace kawai kin burge nine Ina Jin kaman San ki nake

Kije kiyi tunani Kinji ko young lady kiyi tunani ko xaki iya aure na gobe xamu hadu sai mu qarasa

Toh nace mashi da sauri don ni gaskiaya na qosa na bar wajan kada wani ya ganni

Da gudu na koma daki
Ina haki
Mama ta lura da hakan tace
Boddo yarinya ta me ya sameki ne?

Amma saina tsinci kaina da boye Mata saboda bansan me xatayi tunani akan hakan ba
Ohhh Allah you keep on testing me all the time
Allah ka bani ikon cin jarabawar ka kodame taxo min

Afili Kuma nace Mama
Babu komai naji tsoro nee saboda nikadai nee a corridor din gashi dare yayi

Mama Tai dariya kadan tace
Ki rage tsoro Boddo
Yooo me xai ciki a corridor din
Babu fa Wanda xai shigo

Ni Zo ki zauna In qara samaki labarinki kin ishe ni kullin
Da na karasa maki

Nikam jinayi bani son Jin wani labari yanxu saboda a zahiri gaskia tsoro nakeji wannan mutumin me yake nufi
Kaman akwai personal abinda ya kawo shi ba soyayyar asali bane
Amma dasannu xan bishi ahankali inshallah Allah baxai bashi ikon cutar Dani ba
Saurin kawar da xancen nayi kada mama ta gane abinda ke zuciyata

Guri na samu kusa da Mama nace Mama na kosa naji
Afara please

Hmm Mama tayi murmushi
Tace kamar yadda nake fada maki Boddo
Alhji. Mata biyu yake dashi
Babbar matar sa tana zaune a wani gari nee daban it da danta
Wannan flat din da kika gani a kulle to natane
Danta Daya Kuma shine Babba agidan gaba daya
Kafin shi ta haihu har sau biyu du Maza Amma Allah Bai bar Mata ba sai ana uku nee  Allah SWT yabar mata  Wanda haryanxu karatu yakeyi Bai gama ba

Sai matar sa ta biyu itace mummy qarama
Ita yaranta biyu
Abuldarr da Kuma Laila

Duk fadin gidan Nan iyakan yaran da Allah yabawa Alhaji kenan
Kuma ko wani mutun Yana da flat dinsa kamaryadda kika gani
Gobe in Allah ya kaimu xan xagaya dake gidan gaba daya don na nuna maki komai sai dai xamu gaji fah saboda gidan ba kadan ba wajan girma

Murmushi nayi nace Mata ba komai Mama
Nikam ma na Saba da aiki baxan gaji ba inshallah
Mama ke ma Baki da Yara nee
Ina zuri'ar ki?
Mama Tai murmushi tace
Boddo yarinya ta guda Mai kimanin shekara Ashirin da dori kadan ya rage ta Shiga Talatin
Ita kadai Allah ya mallaka min
Tai Shuru for a while

Mama ya kikayi Shuru Kuma
Ko ta mutu ne and Ina mahaifin ta

Boddo kenan kina da son Jin labari....mahaifin yata Allah yai Masa Rasuwa shekaru Ashirin kenan, diyata Mai suna Halima Kuma tana gidan mijin ta ayanxu Haka tana da 'ya'ya Hudu jikokina kenan
Sukanxo ai xaki gansu wata tana

Toh Mama Allah ya kaimu lakacin da xasu xo
Ameen
Mama tayi murmushi kin gaji da yawa xo ki kwanta ki huta ko

Toh Mama na fada Ina Hamma
Na kwanta kenan na fara tunanin halin da Baba yake ciki
Allah sarki baba ko yayi Daya dawo ya tadda bananan
Allah ya qara Masa lafiya
Ya Kuma bani ikon daukan dawainiyan shi nan gaba
Na Dade  Ina tunanin Baba har bacci mai nayi yai awan gaba Dani

...........

Washegari
10am
Nagama abinda nakeyi
Na fita daga cikin dakin Hajiya don batanan tana wajan Alhaji
Na fita don na wanke mopper da towel a waje saboda bana Jin dadin wankewa a bayi, ba jimawa na gama na dan zagaya tabaya kadan inda nake shanyawa wajan wasu fulawoyi na gama shanyawa
Na juya kenan xan wuce
Naga mutun agabana

Gira ya daga min
Hade da min turanci
How far?

Saukar da kaina nayi kasa na gitta ahankali xan wuce
Amma Kuma Kash hannuna yaso kamawa ya sabule yaji ya rike hijab

Kallona yayi cikin mamaki

Sai ya wayence kamar babu komai yace kada Kiyi gigin Fadi ma wani wannan maganar
Tsakanin mu ne
It's a secret
Har ya tafi Sai Kuma ya dawo
Na manta ku masu aiki Baku fiye Jin turanci ba
Ina nufin  wannan maganar sirri nee tsakanina dake
Sannan ya wuce

Sosai hankali na ya tashi narasa Ina xansa kaina sabon Al'amari na Shirin faruwa Dani

..............,....

DielaIbrahim ✍️
Vote/Share please


WACECE NI ✔Where stories live. Discover now