Chapter 13

252 27 9
                                    

Wacece Ni?

Part 2/13

_______________________
Kidnappers area

Arazane na dago kaina dukda ba iya ganin su nake ba......zuciyata ta karaya matuka na Kuma durkushewa Ina tunanin to wa zasu kashe tsakanin ni da Aamir

Shakka babu mutanen da gaske suke zasu iya kashe mu, su ba damuwansu bane saboda Duk sanda zasuyi kisan mutane da akwai wani waje cen cikin daji dasu ke kwasarmu sukai mu anan suke kashe Duk Wanda zasu kashe.....a iya tunani na rami ne awajan babba Wanda da zarar sunyi kisan atake suke tura mutum ya fada, wani ma da ranshi za'a turashi daga nan asake masa harsashi..........jiri naji Yana Kama ni atake na kuma durkushe awajan kai na kuma akatsa tsahon minti biyar kafin na dago cikin dauriya da jajircewa na furta, Ku kashe ni,kumin duk abinda zakuyi min Amma don Allah ku sake shi ya tafi na karasa ina hada tafukan hannaye na biyu hade da hawaye dukda ruwan ba fitowa yake ba sakamakon kullin da idon yasha na tsahon kwana Shida,

Umarni naji yana bayarwa
Akwashe su atafi dasu........daga nan Kuma yayi Shuru

Inajinsa Kuma Yana waya yana requesting kudi masu yawa ahannun wasu mutane.....idan suna son Dan su araye.......sosai na tausaya ma duk wanda mutanen nan sukayi nasaran kamawa.......kamar yadda aka umarce mu da mu tashi. Na lura kaman muna da yawa saboda yanda nakejin karar jan kafa na mutane daban daban

Bayan ankaini dakin da zan iya cewa masauki na kenan.......kukan zuciya na cigaba dayi Ina dana sanin saka kaina cikin wannan Hali.......Ohh Allah ka kubutar da mu.

______________Nabil_______________

Da yamma ne misalin karfe biyar da rabi 5:30pm
Bakajin motsin komai a cikin jejin Kuma baka iya hangen mutum Koda kuwa Yana kusa dakai ne saboda yawan manya manyan bishiyoyi dasuke cikin jejin....,Nabil ne kwance a kasa fuskanshi kuwa an shafe da bakin color Wanda sojoji suke shafawa  ayayin da suke kan aikinsu..... baka iya gane su ma Nabil ya na hangen cen wani waje Mai nisa tare yake da sauran colleague dinsu wanda Suma Duk sun kwankwanta ba'a ganinsu.....Bayan mintuna ashirin,
sai suka sakko suka hadu waje daya.....magana Nabil ya farayi masu yana musu bayanin yanda zasu afkawa mutanen dukda haryanxu basu Gama gano ainihin wato inda kidnappers din suke ba.........suka rarraba kansu kafin suka fara aiki......

Tsahon awa biyu suka dauka awannan jejin Amma Basu gano komai ba, sai Kara lulukawa ciki sukeyi.....Allah cikin ikon sa Nabil da course mate dinshi suka hango hayaki da nisa kadan dasu.....da alama wuta aka kunna
Ba shiri suka hada sauran mutanen sukayi hanyan da hayakin ke fitowa,Bayan tafiya Mai tsayi dasukayi suka iso wajan da hayakin ke fita  katon rami ne wanda suna haskawa da touch dinsu sukaci karo da gawawwakin mutane wajan inbanda wari babu abinda yakeyi........Nabil ya fara tunani aranshi shakka babu suna dab da Isa wajan kidnappers din sai dai dole suyi taka tsantsan saboda kar hanyan ta bace masu.......ya kalli sauran yai masu bayani tayanda zasu gane yace kowa ya shirya da kyau....cigaba da tafiya sukayi wanda akalla saida sukayi tafiyan kilometer 20 da kafa kafin Suka iso wajan Alhamdulillah Daya daga cikin sojojin ya fada bayan ya hango mutanen da abin hangen nesa
Ya juyo da saurin sa yace
Na hangosu, mun iso wajan..... Nabil yai saurin ansan abin ya hanga tabbas yana iya hango bukka da gini mai rufi sai wuta da aka kunna da alama inda suke dafa abinci ne.....Allah yasa suna iya hangowa saboda hasken farin wata daya haska ko ina na wajan

Ya ajiye abin sannan ya koma gefe suna ta shawara yanda zasu afka masu bayan minti goma duka suka fara rarrabuwa into 4 part, sun Isa wajan Amma ba Kai tsaye ba....Daya Bayan Daya Kuma cikin dabara ahankali suka fara attacking dinsu, Allah cikin ikonsa sunyi attacking din na waje sun gama dasu dukka....toh fah daganan wasu set din mutanen masu Dan Karan yawa suka fito, Nan take fada ya kaure
Ba sojojin ba ba Kuma kidnappers ba kowa kashe shi ake
Nabil da Course mate dinshi Hudu suka nufi hanyan da zai kaisu cikin wajan sai dai arashin sani aka fara harbi but, ba'asamu kowa daga cikin su ba Nan take Suma suka soma harbe mutanen ciki da waje........... successfully suka kashe su, suka Shiga ciki ba tareda Bata lokaci ba suka ci Karo da mutanen da aka Kama da yawa akalla zasu Kai Talatin ko Arba'in Nan suka fara fito dasu ahankali bayan sun kunce ma ko wannen su hannu da kafa da ido sai dai abin tausayi wasu dakyar suke iya gani,haka sukai ta daddagewa suna tafiya .......Wani Dan saurayi ne yai saurin rike hannun Nabil yace yallabai ku taimakamin Yar uwata sun kaita wani wàje bansan ina ne ba........Nabil ya Kira daya daga cikin CourseMate dinshi yace ya tafi dashi su Nemo inda Yar uwarshi take

Course mate din yace Major Nabil da mun tafi tare saboda ta iya yuwuwa cen ma mutanen yawa garesu.....Nabil yadanyi Shuru daga bisani yace okay muje ya umarci sauran dasu hadu da sauran mutanen su a waje su yanka cikin jejin su zasu taho daga baya,

Suka Kama hanya Dan Saurayin yace dakata yalla bai bari inyi wani Analysis....aduk sanda zasu kaini wajan muna fita daga nan Hagu mukeyi, Nan suka bi hagu
Yaron ya cigaba dacewa yauwa mukanyi tafiya Mai tsayi sai muyi dama Nan take suka ga wata hanya Kuma datayanki dama suka bi....daganan Kuma sai mu shiga wata kofa danake tunanin gabas take kallo, Nan ma Kuma suka haska sukaga kofar tabbas direction din gabas yake kallo.....cikin sauri don Basu da time suka nufi kofar suka fara bugawa da karfi,

********

Ina kwance cikin wani mayuyacin hali mai wuyan fassarawa.....Babu abinda bakina yake ambato sai sunayen Allah masu rahama tun Bayan sallan isha'i wanda da taimakon Mai tsaro na nake sanin lokutan sallah haka wani zubin nake sallah batareda Alwala ba........Ina nan dai kwance mukaji harbe harben bingida nida Mai tsarona

Ya tsorata sosai yazo ya kwance ni Amma Bai bude min idanuwa ba muka cigaba da tsayuwa batareda mun leka don ganin abin da ke faruwa ba,

Muna haka ne kwatsam mukaji ana bubbuga kofar mu kaman za'a fasa.....Ina nan take na Kuma riki cewa tsoro ya Kuma Shiga jikina....mutumin ya dubeni yace
Alhamdulillah Ki godewa Allah nayi niyan kubutar dake Amma da alama sojoji ne sukayi attacking dinmu.......zan so na mutu don na huta da wannan rayuwa ki tashi ki bude kofar saboda idan sun shigo su harbe ni, Kinga wata kila Allah zai dube Ni da idon rahama ranar gobe kiyama.............ya tsagaita adaidai lokacin da aka fasa kofar mukaji shigowan sojojin.........

Haskomu sukayi da touch light dinsu Mai mugum haske

Aamir ya karaso ya kwance min idanu saidai bana iya budesu saboda nauyin danaji sunayi yace dani ahankali
Boddo tashi sojoji ne suka zo cecen mu....

Ahankali nace Yaya Aamir idanuwana bazan iya budesu ba
Sunmin nauyi yace daure Boddo

Tsawa mukaji ana cewa kutashi mutafi kunsan bamuda lokaci

Aamir ya taimakamin na tashi har mun fara tafiya na tuna da mai tsarona

Na koma wajan da sauri nace idan kana tunanin ka koma ga Allah Kuma ka cigaba da zama anan cikin mutanen nan toh Allah bazai yafe maka tuban dakayi ba .......saboda haka don Allah ka tashi mu tafi tare saboda kai ma ka tsira daga hannun mutanen Kuma ka tsira daga fushin ubangiji..........bai min musu ba ya tashi muka fita tare Kai tsaye hanyan daji muka nufa Ina Jin Daya daga cikin sojojin na waya da alama kwatancen hanyan da zamu bi ake mashi cikin sauri muke tafiyan sunayi suna waigawa baya. don su tabbatar ko we are still safe.........bamuyi aune ba mukaji karar harbin bindiga wanda ya rikita mu.

Batareda bata lokaci ba sojojin suka fara harbi suma bayan sun kawar da mutanen dasukayi Harbin ne....sai suka fara dubawa suga wa aka harba acikin su..........ana Haka ne sukaci karo da Aamir kwance cikin jini an harbe shi, Nabil ne ya gane shi take ya kallo inda nake dukda duhu ya mamaye wajan Amma yana iya hangoni sabanin Ni da nake tsugunne a waje daya idanuwa na akulle saboda bana iya gani har yanzu, kafin faruwar abin Ina rike da hannun Aamir ne Amma ana yin Harbin na nemi hannun nasa na rasa.........wani sojan ne ya zo dab inda nake ya kama hannu na yakaini inda Aamir yake.....

Ina shafa jikin rigar zuciyata ta tabbatar min da Aamir ne
Inna lillahi wa'inna illaihi raji'un

Hannu na daura akai ina fadin yaya Aamir don Allah ka tashi ka cika Alkawarin daka daukar wa Mama..........saidai Kuma me take naji wani jiri na diba na kaina ya fara wani matsanancin ciwo Mai wuyar fassarawa........na Fadi kasa warwas...........

***************
Vote!Vote!!Vote!!!
Please

WACECE NI ✔Where stories live. Discover now