Chapter 14

266 28 0
                                    

Wacece Ni?
Story written by
DielaIbrahim ✍️

Part 1/14

________________________Abuja
Maitama _________________5:30am

Boddo acikin sabuwar rayuwa
Muje xuwa Readers
😉😉😉


Washegari

Shekaru Sha bakawai kenan kullin sai an tada Ni da ruwan sanyi
Ammaa sai gashi yau da kaina  na tashi cikin ikon Allah Kuma na gabatar da sallah asubahi a tsanake batareda nayi ta cikin sauri ba sabanin da a titi nakeyi idan naje diban ruwa.....

Mama ce ta katse min tunani na da cewa karfe Takwas aikin zai fara alokacin Hajiya take gama komai nata take fita karyawa da danta zuwa part dinsa
Karfe 10 take shigowa lokacin sun gama ya fita kenan
Ke Kuma xuwa wannan lokacin ki tabbatar kin gama komai sanann ki xauna a parlon domin jiran dawowarta

Toh na bita dashi kawai
Ina mamakin wannan doka dukda aikin bawani aiki bane Amma Yana bukatar natsuwa da Kuma tunani

Tashi nayi na gyara dakin da muka kwana na wanke bayi nayi wanka
Lokacin agogon dakin ya nuna karfe Takwas saura
Don Haka na figi yakunanne hijab Dina na fita xuwa Dakin Hajiya
Kamar yadda Mama ta nunamin  jiya
Dakin naje nayi knocking
Ji nayi ance yes come in

I was imagining dat whose voice was dat......saboda jin siririyar muryar,   murda kofar nayi na Shiga Masha Allah na fada a cikin
Zuciyata wannan dakin kaman ba'a Nigerian ba
Anya a Nigeria nake kuwa
Na tambayi kaina
Saboda tsarin dakin ba yanda gidajen Nigeria yake akayi ba
MashaAllah

Come closer young lady

Nabi inda naji voice din
Sai da na sauka ta wani steps siriri nayi doguwar tafiya kafin na iso wajan set din gadon nata Mai Kama da gadon sarauta
Tsaye na hangeta sanye cikin doguwar Riga na lace
Ta yafa gyale colorn kayan asaman Kai ta yafaWanda gashinta kawai ta Kama da band Bata daura Dan kwali ba

Hannunta sanye cikin warwaro da agogo dakuma zobe
Kafar ta flat din takalmi nee color Daya da gyalenta

Saurin tsugunnawa nayi
Nace Mata Ina kwana
Sanin wacece ita agidan
Dakuma yin aikina yadda yadda yadda dace

Ta juyo tace min Ina kwana yarinya Mama  ta Fadi min yau xaki fara aikinki
Na ce Mata eh inshallah

To Miye sunanki
Boddo na Bata amsa

Asalin sunan ki fa
Nakuma cemata Boddo
Boddo Abubakar
Sunana kenan

Toh Masha Allah yanxu xan fita wajan dana acen xanci abinci so ba sai kin shirya komai na abinci ba ki gyara min dakin kawai naji Yana Dan tsami tsami nee
Saboda
Dukda dai jiyaan gyara Amma gyaran Bai min ba
Ki gama saboda idan na dawo muyi Hira ko Boddo, tai min murmushi Wanda yasa Jikina yayi sanyi sosai

Nace Mata to saboda ta kashe min jiki da taushin kalamanta izuwa gareni
Tunda nake a rayuwata Banda Baba da goggo
Babu macen da ta taba yimin magana cikin taushin murya
Lallai wannan matar  akwai mutunta mutane
Hawaye nee suka Dan diga a idanuwa na kadan
Na daga Ido naga har tabar dakin
Kallon dakin na somayi
Hakika babu abinda ya samu dakin Kal Kal yake kamar yanxu aka gama gyarawa
Ga wani kamshin turaren wuta da yake tashi da Kuma kamshin turaren Arabs gaskia Ni Kam a waje na banji wani tsami tsami da dakin yakeyi ba
Kawai dai don ta qasance Mai tsabta nee shiyasa nabawa kaina amsa Ina kokarin cire hijab Dina
Domin na fara aikina

Ina ta faman aiki zuwa karfe Tara da Rabi na ida komai na koma dakinmu na ci abinci
Wanda Mama ta kawo min
Lafiyayyan breakfast
Kadan naci saboda bancika cin abinci dayawa ba
Karfe goma daidai na tashi na nufi dakin Hajiya
Abakin kofa mukaci karo da ita ta dawo, murmushi tamin
Sannan ta Shiga ciki
Nikuma na biyota abaya

Zama tayi a daya daga cikin
L -Shape din kujerun da suke bangare guda na dakin kafin ka sauqa ta step din dazai kaika wajan gado

Kasa na zauna saman carpet
Tace tashi Boddo
Zauna kusa da Ni mana
Ahhhah Ranki shi Dade bankai wannan matsayin ba
Murmushi tayi tace kamar jika na daukeki
Kinga jikokina Basu cika xuwa wajena yimin Hira ba Sai idan hidimar gabansu ce ta kawo su
Mutun Daya nee nakejin sa ajiki na Kuma nake daukan sa jika na Mai kula da Duk wani ci nawa da Sha na matukar Yana  gari babban jika na na cikin gidannan

Allah sarki mi grandson Ina missing dinshi

Niko bance komai ba ayayin da na qasa kunne Ina sauraronta

Tace Boddo kin iya labari?
Ina son labari shiyasa nace a samomin Yar aiki
Duk wa'inda ake kawo min
Sata sukeyi min
Shiyasa nake koransu

Ke Kuma tunda na ganki naji zuciyata ta yadda dake nasan baxaki cutar Dani ba

Nace Inshallah Ranki shi Dade
Dariya tayi tace canja min suna Boddo
Na kalleta da mamaki na
Wai na canja mata suna
Ina matsayin Yar aiki
Nace AA Hajiya bankai matsayin hakan ba

Tace Ni mabaki izini ai

Nayi murmushi sannan na furta
Hayatee

Kallona tayi tace
Wannan sunan
Meyasa kika zabi sunannan

Nace saboda tunda nake arayuwata ban taba haduwa da matar data Shiga Raina ba irin ki
Na Dade Banga mace Mai irin halayenki ba

Hajiya Tai murmushi lallai yarinyar tana da hankali
Hakika ba kamar sauran Yan aikin da ake kawowa ba
Su da ko Hira basuyi Mata
tace Ni har wani Hali gareni
Boddo kinsan babu kyau wulakanta Dan Adam
To Akan me xanyi wulakanci saboda Allah ya bawa Dana kudi
Kuma muna cikin daula
Ahah Boddo musulmi Dan uwan musulmi nee
Don Haka kema Ina umartarki da karki wulakanta na qasa dake
Kinji Koh

Toh nagode Hajiya au🤭 Hayatee 😁

Hajiya Tai murmushi
Sunan ya tuna Mata da jikanta
Sunan dayake kiranta dashi kenan.

Haka sukai ta hira da Boddo
Abin gwanin burgewa

...................

DielaIbrahim ✍️
Vote/Share please

WACECE NI ✔Where stories live. Discover now