Chapter 15

233 28 2
                                    

Wacece Ni?

Part 3/15

______________________Maitama

Misalin karfe shidda na yamma Mummy ta dawo Kai tsaye sashinta ta nufa cikin tashin Hankali take ta faman dialing wani number wanda har yanzu ake ce mata not reachable, cike da takaici ta kuma dialing number sai a lokacin tayi sa'a ya shiga bugu uku aka daga.

Haba Hajiya Ina ta faman kiranki layinki baya shiga tun dazu,

Cikin wayar akace Yi hakuri Mummy wlhy na shiga inda babu network ne, Ina fatan dai lafiya Koh?

Inafah Ina Nan hankali atashe naje wajan malam ne, na kaimashi matsala ta.

Okay tih Ina fatan ya biya maki matsalar taki?

Ya biya Hajiya Amma fah sharuddan daya kidaya min ne suke tsorata Ni,

Wani irin sharudda?

Kinaji kawata yabani maganin mallake gidan ne gaba daya....Birnewa zanyi amma adakin Baffah, Kuma yace karna saki wani ya ganni,idan na bari wani ya ganni to hauka ko mutuwa zai tabbata akaina.....sannan yace ballallai bane abinda zanyi yayi aiki idan na birne.Shine fah kika ga hankali na ya tashi na rasa wanne zanyi.

Tohhhh ai kawai ki aiwatar da aikin Mummy Amma ki tabbatar babu wanda ya ganki.

Kina ganin hakan shine solution Ni nasan babu Wanda zai ganni dama kawai dai na tsorata ne.

Toh ki aiwatar inyaso gobe sai ki kira ni ki sanar dani.

Toh Nagode Hajiya.

Tana gamawa, ta tashi ta dau maganin saidai waugawan da zatayi ne ta ci karo da Baffah da Kuma wasu mata guda biyu Wanda idanuwanta sun kasa gano Mata ko su waye.

Wayen cewa tayi tana cewa Ohhh
Alhaji na ya kk tana sosa kai.

Baffah yasha mur yace biyoni part dina, ko dayake dama cen Zaki koh dauko maganin kizo mube toh.

Hankalin mummy ya tashi Bata da choice haka ta bishi, tana yi kaman wata munafuka, Koda suka Shiga ganin mutane tayi dayawa afalon ciki harda su Adda  da Daddy ga Kuma yar'ta Lailah ko yaushe tazo oho...

Baffah yace karaso Mana ku ku zauna anan ke kuma mummy kin gane su,

Mummy ta dubi matan da ake cewa kota gane su.....babu Shakka ta gane su kuwa Rahane nee da Maman Aamir ta hannun daman ta.

Amma saita girgiza Kai tace Bata ganesu ba....Baffah yace kalle su day kyau ki kura masu Ido Zaki gane su.

Haka Tai ta kallon su, daga karshe Kuma ta koma hararar su tana turo baki, Baffah yace munji dukkan wani abu da kika aikata, gashi Kuma yanzu kina Shirin aikata wani adakina....Ga hanya Zaki iya Shiga ki birne duk abinda zaki birne babu mai Shiga ya ganki inshallah.

Mummy tana tsaye kunya ya kamata, tafara soshe soshe tana cewa wlhy Allah nine silan faruwan komi, da fari kuka tafarayi Amma daga karshe sai ta Kama dariya tana soshe soshen jiki, Lailah tayo kanta da gudu tana cewa Mummy miye haka, Mummy dama ke kikayi sanadin bacewar Boddo......mummy meyasa Kika aikata wannan laifi haka.

Baffah yace bama wannan ba, Abuddar ya salwantar min da kudade na ya lalata min company dina na Sudan Kuma still kin goyi bayansa Kuna so ku cutar damu.....Halima ke wacce irin macece mara tunani, Baki da hangen nesa ko kadan.

Mummy tafara kuka tana cewa Alhaji ku yafemin bani da niyar cutar daku, sharrin shaidan ne.

Baffah yace Hajiya Ina so kibani izini na aiwatar da hukunci.

Hajiya tace na baka dana...ka aiwatar da ko wani hukunci na amince.

Baffah yace kije na sawwake maki aurena Halima, na sake ki.

Ihu tayi wanda idan kana kusa da ita dole ka firgita,Lailah ganin Halin da uwarta tashiga ta janyeta afalon ta nufi sashinsu tana kuka Amma mummy sai fisgewa takeyi, da kyar ta iya kaita dakinta ta tura ta ciki sannan ta kulle dakin. Nan ta zauna tana zubar da hawaye....ji tayi an dafa ta waigawan da zatayi taga Boddo da mijin ta a gefe....wani sabon hawaye tasomayi masu matukar zafi.

Na tsugguna na dafa ta nace kiyi hakuri ki tashi kibi mijin ki kuje gida.... don't worry she will be fine inshallah.

Lailah ta rungume ni tana cewa ki yafe min Boddo na musguna maki na nuna maki tsana don Allah ki yafemin.

Nace kada ki damu Lailah Ni komai kikaga ya faru dani to daga ubangiji ne, ban rike ki azuciya ba kinji....na kalli mijin nata nace mashi ka dauke ta ku tafi.

Ya gyada kai lallabata yayi suka bar gidan ...Nima Kuma nabi nawa mijin muka koma gida.

Tohh mummy dai rashin lafiya ta kamu dashi mai tsanani, Baffah yasa aka dauketa aka kaita gidansu acen suka cigaba da jinyar ta.

Su Maman Aamir kuma Baffah ya sallame su tare da yi masu kyauta suka koma gidajen auransu Amma fah sai da suka hada Sadiya da Aamir aure.

*******************

Vote!Vote!! Vote!!!
Please

WACECE NI ✔Where stories live. Discover now