Chapter 9

290 25 0
                                    

Wacece Ni?
Story written by
DielaIbrahim ✍️

Part 1/9

******************

Tunda Boddo ta shige gidansu Dije Bata fito ba tana ta kuka tasan dole abinda suka fada shi xai faru da ita
Amma ya xatayi gwanda ma tayi nesa da Innah ko hankalinta xai kwanta
To ya xatayi da Baba xatayi kewanshi Allah sarki baba

Dole tasan yadda xatayi ta Hana kudirinsu na cutar da Baba

Karfe Takwas na dare ta tashi ta tafi gida abinta Dije ta rakota har gidansu
.

.....

Few days later Boddo tayi wani saurayi
Al'ameen
ahanyanta ta komawa gida
Ya rage Mata hanya Akan mashin dinsa
Al'ameen
Ba Mai kudi bane Amma Yana da rufin asiri
Yana saman layinsu nee shida iyayensa

Baba yaga Alamar dagaske Al'ameen yakeyi saiyasashi ya turo iyayenshi  Dan su San da maganan
Magana ya kankama Al'ameen har kudin gaisuwa ya kawo gidan su Boddo
Tohhhh fah
Da Inna Taji maganar cewa za'ai wa Boddo aure Baba har ya ansa kudin gaisuwa yanxu Rana kawai xa'asaka Kuma abinda ya Bata Mata Rai batasan komai akan maganr ba

Tafara safa da marwa ta shiga ta fita naganin ta Hana wannan al'amari faruwa

Amma ta kasa samun nasara
Kullin ma mutumin sai yaxo wa Boddo da Kaya da kayan kwalliya
Yakan siya Mata Duk abinda yaga Yan Mata na anfani dashi na yau da kullin

Ana saura sati daya  iyayen Al'ameen suzo ai masu baiko
Kwatsam

Wata Ranar Lahadi misalin  karfe biyu xuwa uku
Boddo ta dawo daga talla kasancewar yau ba sch

Tana Shiga gidan taga wayam babu kowa har Inna ma Bata Nan
Don Haka ta Shiga dakin Tai bincike ta Nemo maganin
Sannan ta musanya da wani garin magani na gargajiya
Bayan ta fito nee ta nufi
Dakin Baba don canja kayanta da wuri  sakamakon Al'adan ta daya riske ta tun tana wajan Talla
Bata so agane ta Shiga dakin Inna shiyasa ta Shiga dakin baba

Dubawan da xatayi taga ai zaninta ya rigada ya baci da jini saboda ita ranar farko rushing yakeyi kaman Yaya

Tana kokarin cire kayanne taji an tura kofa saurin waigawa tayi
Zare idanu tayi ganin idi ne Dan Inna da Kuma wani na biye dashi
Kuma ga dukkan alamu ba'a haiyyacinsu suke ba yayi shaye shayen shi Daya Saba

Ihu ta tsala tana neman hanyan guduwa Amma Ina tuni dayan ya buga ta da bango Nan da Nan ta fara Jin jiri da taimakon ubangiji ta tashi ta Kara tsala wani ihun neman taimako
Xagaye suka fara yi adakin har shima ya fara gajiya Idi Kuma ya tafi waje don dauko maganin da xasu Shaka Mata
Sun manta Basu shigo da maganin ba
Boddo tace kuji tsoron Allah
Meyasa xakuyi min wannan abin
Shiko dariya yake Yana Kuma surfafa Mata zagi kasantuwar ba'a haiyaccinshi yake ba

Yasamu sa'an kamata yai saurin toshe bakinta saboda ihun da take zabgawa
Yace cikin fada Idi kayi sauri ka kawo mana
ya kwantar da ita a kasa Yana kiciniyar danne Mata hanci
Tare da son cire Mata zani
don yasamu yayi abinda yakawo su
Boddo babu abinda takeyi sai kiron sunan Allah da Kuma kuka

Cikin ikon Allah wasu suka shigo turo kofar dakin akayi suna salati sukai saurin  daga shi akanta

Suka fidda shi cikin gida Wanda ihun yasa mutane sukaji kasancewar unguwan akwai yawan mutane
Cikin gidan ya fara cika da mutane Kam

Zuwa wasu muntuna su Maman Rabi da Maman Safiyah sun dawo

Jin abinda yafaru nee yasa sukayi Shuru Basu tofa albarkacin bakinsu ba
Minti Ashirin da faruwar wannan Al'amari Inna ta dawo

Itama haka ta samu labarin abinda Dan ta da abokinsa  suka  aikata
Boddo na dakin Baba tana kuka taji mutane nata maimaita sun Mata
fyade Allah sarki wannan wani irin abin kunya nee Kiri Kiri acikin gidan ubanta Kuma da Rana tsaka

Agigice Boddo ta fito daga dakin ta kalli illahirin mutanen gidan tace  kuyi hakuri Amma babu abinda ya faru dani
Wlhy baimin komai ba
Ta cigaba da kuka Mai tsananin
Ciwo dakuma zafi
Rabi da take Bayan Boddo tace
Lahh wlhy jama'a ga sheda jini
a zanin ta

Nan mutanen da  suka rage suka fara
Magana kasa kasa

Wasu sabbin hawaye nee suka sauko Mata zazzafa
Takara bude Baki tace
Bashi bane Jinin Al'ada ne
Ku fahimce Ni
Ta nufi mutumin da aka Kama za'akai shi police station
Tace ka fidda Ni taga cikin wannan tarkon ,kasani wlhy baka aikatamin komai ba
Ka wanke ni don Allah Kai ma ka wanke kanka

Shiko gogan idanuwanshi sunyi jajir xuciyarshi ta mashi Baki
Bai samu abinda yake so ba
Kuma gashi Matukar Wanda tasasu aikin ta tabbatar ba'ai ma yarinyar komai ba
To baxata cika masu sauran kudin su ba
Gyaran murya yayi yace
Malama kina so na Kara aikata wani zunubinne wato karya Bayan wannan zunubin Dana aikata akanki
Nan ya fakaici idanuwan mutane da hankulansu yaga basa tare dashi
Nan take ya juya ya gudu

Basu samu nasaran kamashi ba

Ita Kuma Boddo tana Nan zaune tana kuka tana maimaita baimin komai ba wlhy karya yakeyi

Inna ta wuce daki batareda tace komai ba.....Suma sauran daki suka wuce aka barta ita kadai tana sunbatu

Atakaice dai ranar a gidan su Dije ta kwana saboda babu Mai tanka ta agidan nasu Kuma Baba bai dawo ba sai washe gari

.............

The next day

Dije wlhy baimin komai ba na rantse maku da sarkin da ya halliceni

Dije tace na yadda Amma jinin da Rabi tagani fah

Wannan jinin al'ada nee kinsan yau karshen wata Kuma wannan lokacinne nake al'ada

Goggo tace na yadda da batunki Boddo Amma wannan mutumin tsinanne ya rigada ya Bata maki suna tunda ya shaida wa mutane cewa ya Miki fyade Kuma gashi ya gudu Kinga xasu dauka da gaske nee

Boddo ta fara Sabin hawaye
Tana rokon inama Allah ya dauki ranta

*********************

DielaIbrahim ✍️
Vote and Share
Pls 🙏


WACECE NI ✔Where stories live. Discover now