Chapter 11

222 32 11
                                    

Wacece Ni?

Part 3/11

*****************************

"Assalamualaikum
Bayan gaisuwa mai tarin yawa izuwa gareki masoyiyata,
Boddo kiyi hakuri da yanda abubuwa suka kasance acikin rayuwarki.....am so sorry , Boddo dalilin rubuta wannan sako shine don na sanar dake cewa amatsayina na mijinki na sawwake maki aurena
Idan kin samu miji kiyi aure.
Bissalam"

Hawaye ne ya keta sauka a idanuna, lokaci daya kuma maganganun Lailah suka fado min arai....dukda ban dauki abinda tace da muhimmanci ba Amma ga dukkan alamu tayi nasara akaina........tunani barkatai babu wanda banyi ba, na mayar wa Daddy da letter batareda na ce mashi komai ba, haka Mamie ma.....sun tausaya min sosai.

*****************
Wata ranar juma'a, ranar yakama 28/12/2018.(wannan itace ranar da bazan taba mantawa ba acikin rayuwata, ranar data zo min abazata, ranar da banyi tsammanin zuwan taba ba.

Yau kimanin wata daya da rabi da dawowa ta gida....Kuma ayau Familyn Hamid, Abba, Dada, kanin Abba, da wansa sai matayensu da kannen Hamid guda biyu wanda na Saba dasu sosai.....sukai mana ziyarar bazata gidan Baffah.

Ina daki na babu abinda nakeyi Mamie ta shigo tace nashirya zamu gidan Baffah anyi baki daga Adamawa.

Natashi na shirya, sannan muka tafi, Hakika sunyi farin cikin ganina, kuma sun tausaya min matuka bansan mesu Baffah da Daddy da sauran mazan  suke tattaunawa ba, nidai Hayatee ta janyoni muka nufi sashinta kaya tabani na sanya na alfarma lace mai tsada sannan aka yafa min lifaya wanda yasha kanshin turaren wuta sandal, sai wata mai kunshi data zo tayi min kunshi mai bala in kyau kaman na amarya kuma tayi masu dije da kannen Hamid.

Nidai na saki baki ina ta kallon ikon Allah su Hayatee babu abinda suke sai murna da shagali.....Haka zalika su Dada, abin ya daure min kai na samu. Mamie na don nasan itakaidaice zata saurareni nace Mamie hidiman me ake tayi ne haka? Dubeni fah na dawo kaman wata Amarya.

Mamie tayi murmushi tace yau ranar farin ciki ce Boddo, Daddynki ne zai kara aure....

Na kalleta da sauri tana daga min gira, nace what Mamie aure fah kikace, shiko Daddy mezaisa ya kara aure a shekarunnan dukda ba tsufah yayi ba.

Mamie ta harare ni, kaji Yar bakin ciki baki so ne akawo min abokiyar zama ko nagane ki, to aniyar ki ta biki.

Na zare idanu, Baki bude Ina kallon Mamie nace aa Mamie Allah ya huci zuciyar ki, ai bansan haka kike son kishiya ba.

Mamie ta hadiye wani yawu Daya tokare Mata a makoshi sannan ta Kuma daure wa tace... Toh nama fi haka.

Nayi murmushi nace Mamie Allah ya Sanya Alkhairi Amma babu ruwana....tace ehh babu komai, tana yi tana min dariya.

Na kura wa fuskarta kallo Ina tunanin kaman ba gaskiya take fadamin ba.....daga bisani na Dena kallon ta don ta fara tsarguwa.

Ranar dai Mamie bata koma gida Dani ba, Wai tunda bani son kishiyar Ni nayi zamana agidan Baffah, kafin idan sun Saba sai na dawo........ murmushi kawai nayi nace toh Mamie shikenan.

Washegari kuwa gagarumin walima aka hada a cen filin gidan  dayake baya, fili ne babba .

Aka shirya ni cikin shiga ta alfarma, wanda kowa Fadi yake nayi kyau, wasu ma har cewa sukeyi nafi kyau akan ranar bikina da Yaya Hamid, niko Boddo Ina mamakin yadda mutane suke yawan fadin cewa Ina da kyau,Kuma wasu sukance naci sunan Boddo wanda ni bana ganin kyan ko kadan......na zauna a gaban dressing mirror Ina karewa halittata kallo,

Tohh Nidai zan iya cewa doguwar mace ce ni chocolate color ce, kuma Ina da doguwar fuska da siririn hanci, babu abinda yafi birge mutane ajiki na sai shape din Jikina don Ina da correct figure 8 shape.
Na girgiza kai ina Kara kallon yadda gown din danasa tazauna ajikina kaman an gwadani.

Dije tace Boddo Allah yayi maki baiwa dayawa, ki gode masa sosai, nace Dije nifah haryanzu bansan wani irin baiwa Allah yayi min ba.

Dije tace kada ki damu da sannu zaki sani inshallah.

Takama hannu na muka fita harabar gidan kowa kallona yakeyi yana yaba irin kyan danayi, bayan na zauna akujera ne Hayatee tazo inda nake tana murna ta zauna kusa dani, ta dafa ni sannan tace jikata kinyi kyau sosai.

Nace Nagode Hayatee, Amma meyasa ake wannan hidiman Hayatee nakasa fahimtar komai dubi yanda akayimin  kwalliya da kunshi kaman wata Amarya...... Hayatee tayi murmushi sannan tace Boddo na, yakamata kisani yanzu kam , Boddo jiya aka daura maki aure Kuma yau za'a tafi dake gidan mijinki da yardar Alkah, Ina so ki kwantar da hankalinki Kuma ki nutsu kiyi biyayya ga mijinki,kada ki damu dasanin ko waye Kika aura wannan zabin mu maukai maki shi, kuma inshallah bazakiyi nadamar kasancewa mata awajansa ba,tayi shuru.

Mamaki da fargaba ya hanani magana, Aure Ina zaune kalau, meyasa bazasu tambayeni ba suji ko inaso na kara kasance wa da wani acikin rayuwata, meyasa bazasu tuntubeni suji ko Ina da nawa ra'ayin ba......hawaye ne suka soma zuba Daya bayan Daya Hayatee na gogemin tana cew lah kada ki fara, Boddo kiyi hakuri zabin da mukamiki bawai zai cutar dake bane kinji.

Nan tabarni cikin damuwa, Ni duk tunani na waye kuma wannan wanda aka daura min aure dashi?

Haka akaita shagali nikam bana farin ciki kwata kwata, na shiga halin damuwa, Bayan Mamie ta iso ne naje wajanta nayi kuka sosai lallashina take tayi tana kwantar min da hankali har aka dauke ni Dani da sauran mutan gidan da bakin Adamawa aka kaini gidan da suke cewa shine gidana acikin garin Abuja.

Da shigan mu gidan ban iya kallon gidan ba, sai dai na lura gidan Babba nee saboda yanayin tafiyan da mukayi kafin muka iso  flat din.

Koda muka shiga inaji anata Koda gidan, Dije ta matso daidai kunne na ta rada min cewa Boddo gidanki kaman aljannan duniya..wlhy tunda nake irin wannan gidan da kayan gidan a T.V nake gani Kuma sai akasar waje, Boddo wlhy gidan yafi Wanda mukaje a Adamawa ke bazama ahada ba.....ban ko kula taba har tagama surutunta.

Daki akawuce Dani aka zaunar dani, ana min hoto, wasu Kuma nacen suna zagaye gida suna Sanya albarka, awa Daya sukayi misalin karfe shidda da rabi duka sukai min sallama suka bar gidan, aka barni ni kadai Ina ta faman sharban kukana, nagaji nabude kaina, Ina Kare was dakin kallo, Lallai ankashe naira adakin jeren daki kaman a kasar waje, nashiga ban daki don yin alwala namma dai wata dukiyar nagani anzuba bayan gidan Mai girma.

Nayi alwala nazo na gabatar da sallan magrib na zauna har saida akayi isha'i sannan na gabatar,na tashi na koma saman gado na cigaba da kukana kaman wata yarinya karama.

Banji motsin taba kofa ba, haka zalika banji motsin tafiya ba, muryar shi naji kawai Yana cewa
Ke karamar yarinya ce, dazaki ta cika wa mutane kunne da kuka.

Arazane na dago kai na kafe idanunshi da kallo,Kuma shima kallona yakeyi ido cikin ido.

******************

Toh masu karatu..... Aganin ku wa kuke tunanin shine mijin Boddo?

Please comment are always welcome....and Vote!

DielaIbrahim ✍️ and please kuyi comment idan kuna jin dadin labarin, along side with silent readers, those that always read without comment and vote, now I need your comment pls for more update.

Silent readers please Vote and Comment 😊

WACECE NI ✔Where stories live. Discover now