Chapter 10

252 23 2
                                    

Wacece Ni?

Part 3/10

_______________________Abuja____
Hospital

Allah cikin ikonsa kuwa Nabil ya fara samun sauki don yakan ci abinci kadan kadan, kuma Yana magana da Ummie da Hayatee ...Amma basu kara tambayan shi Hamid ba saboda sun lura duk randa suka masa maganan Hamid, hankalinshi Yana tashi sosai kuma wani zubin har ciwon ya dawo.

Baffah yayi kiran  Abba mahaifin Hamid yazo, kuma ya zo shida kaninsa.
Anan Baffah da Daddy suka basu takardar suma suka karanta, bakaramin mamaki hakan ya basu ba taya jininsu zai aikata wannan laifi, tuni suka soma ba wasu Baffah da Daddy hakuri,

Baffah yace kada ku damu, jira mukeyi Nabil ya samu sauki yasanar damu inda Hamid yake.anan magana ta tsaya cak, sai aka koma kula da Nabil Kuma   su kuma su Abba da kaninsa  suka koma gida amma sai da Baffah yai masu kashe di da karsu sanar da kowa abinda ya faru.

****************

MashaAllah acikin sati biyu Nabil ya warware har yan wajan aikinsu suka zo gaishe shi,anan Ogan su yake sanar dasu Baffah rashin Hamid da akayi... .sun dauka sun sani ne.

Kut😮hankalin su Hayatee bakaramin tashi yayi ba, ana nufin ace Hamid ya rasu nanfa kowa ya koma zaman taguma da kallon kallo, damuwansu ya kara yawa.

Hakanan bayan tafiyan sojojin Nabil ya samu Baffah da maganar yace Baffah kuyi hakuri  nakasa sanar daku abinda ya samu Dan uwa na, Baffah Ina matukar kewan shi Kuma Ni har yanzu ban yadda Hamid ya mutu ba shiyasa na kasa fadi maku. Gashi mun nemi gawarsa mun rasa bamuda wani evidence da zamuce he passed away, kuyi hakuri Baffah.

Baffah Kam sun gane Nabil sambatu yakeyi hakika son dayakewa Hamid ne yasa yake fadin maganganun nan, bugu da kari kuma bai karanta abinda ke cikin letter dinnan ba.

Cikin dauriya Baffah ya sanar da iyalan Hamid abinda ya sameshi.
Sun matukar girgiza dajin wannan mummunan labari.

Nidai Ina zaune a gidana nida kannensa as usual....bamusan meke faruwa ba, tsahon kwanaki uku kafin mahaifin Hamid ya aiko kirana haka muka tafi nida yaran.

Ko da muka Isa gidan kuwa alamu ya nuna akwai damuwa a tattare da mutanen gidan.....dakin Dada muka shiga anan take shaidamin cewa na samu Abba wato mahaifin Hamid a falonshi, hakanan naje na sameshi Jikina asanyaye.
Abba ya kalle ni cikin tausayi yace ya'ta kiyi hakuri da yadda rayuwa tazo maki, Duk abinda zakiji agaba to haka Allah ya tsara wa rayuwarki, kuma babu wanda ya Isa ya canja maki, ya Dan dakata kadan..... Kana ya cigaba da cewa yanzu zakije ki  shirya gobe za ki koma  Abuja Daddynki ya turo da kudin jirgi har an Miki booking, so ki zama cikin shiri karfe tara zaku tashi.

Nayi wani sakakau babu ko motsi, fata na Allah yasa dai lafiya, hankali na kuma yana so ya tashi saboda Ina mamakin yadda lokaci daya za'a ce min naje Abuja kuma sai ina ganin kaman akwai wata matsala ce, nakoma dakin Dada, abinda na lura dashi shine Dada na cikin damuwa kuma bata son mu hada ido da ita don inda nake ma Bata kallo......araina nace hala saboda tsananin kunya ce irin tasu ta fulanin usul....na koma gida maimakon inyi zurfin tunani akan wannan al'amarin a'a saima Jin dadi Dana farayi zanje naga su Daddy da Mamie da kowa ma, washe gari da sassafe na Gama shiri Abba ya turo aka dauke ni amota aka kaini airport bamuyi ko sallama dasu Dada ba don har kannensa ma dama su kam  a gida na barsu.

Bayan mun Isa Abuja lafiya, tuni Daddy ya turo mota aka zo aka dauke ni. Ina Shiga part din Mamie na nufa Ina murnar ganinta...... Believe you me, I was very surprised danaga wani damuwa cike a fuskar Mamie sai dai tayi kokarin boye min, babu yanda banyi ba ta sanar dani damuwarta Amma taki, hakura nayi kuma na barta muka tafi ahaka.

Kwana na biyu agidan, atunani babu wanda yasan na dawo nace wa Mamie zanje nagaida su Hayatee....Amma Mamie ta hana Wai na kara hutawa.

Haka na hakura har tsahon sati  daga dakina sai falon Daddy sai dakin mamie, sometimes nakan zagaya na tafi garden tun safe sai yamma nake dawowa....Rayuwa ta canja min kwata kwata na dena Jin dadin zama dasu, na kuma rasa dalili, ko dan yawan damuwan dànake gani a fuskokinsu shiyasa nima na Shiga damuwar, sai dai Kuma duk ranar Sunday suna fita  su barni sai suce ba jumawa zasuyi ba yanzu zasu dawo, hakanan nake hakura wani zubin Kuma nayi ta masu bori harsai Daddy ya dauke ni mun fita shopping idan ya dawo dani Kuma sai su Kara fita, Ni anawa tunanin wai Ina so na dawo da murmushin su da fara'arsu kamar yanda suke ada.

WACECE NI ✔Where stories live. Discover now