Chapter 4

238 25 2
                                    

Wacece Ni?

Part 3/4

****************

Bayan farfadowan Inna da Yan mintuna, aka yi mata bayanin komai ita dasauran matan... .babu abinda suke Fadi sai MashaAllah Lallai wannan al'amarin da abin mamaki yake....... Lokaci kankani jama'an anguwa suka fara taruwa jin cewa Boddo ta dawo kuma da iyayanta tazo......gida ya cika ana ta Shiga da fice ana ganin Boddo da iyayan ta.....kowa yana tofa albarkacin bakinsa.

Inna dake zaune waje guda ta takure kanta babu abinda take yi sai kuka da dana sani acikin rayuwar da tayi da Boddo tana neman gafara awajena, wai na yafe mata, Idan mutane suka shigo kuwa babu abinda suke sai zaginta suna cewa tayi abubuwa marasa dadin ji ta Fadi muna nan abubuwa akan Boddo..,....haka dai har su Baffah da Daddy suka shigo sun maimaita abinda su Hayatee suka fadi wa matan gidan....daga karshe dai Daddy ya musu kyauta mai tarin yawa yace su ciyar da kansu da Kuma iyalansu.........nikam na nemi da a tafi da Inna Abuja ko hankalinta zai kwanta kuma ko ta samu lafiya, Amma Hayatee tace ba yanzu ba tukunna.

Da yamma mukai masu sallama muka bar anguwan bayan Daddy yayi rabon kudi sosai wa makwafta da Duk wanda ya nuna yasan ni......nayi mamakin yanda Daddy yake ta fitar da kudi baya ko kirgawa, ko a jikinsa.......Ni dai nasan Daddy da Baffah suna son talakawa Kuma ayau na Kara gasgata hakan.....Hakika suna matukar girmama rayuwar talaka.

Inna har kofar gida ta rako mu bata bar kukan ba......sai faman godiya takeyiwa su Hayatee saboda duk cikin rabon kudin da akayi nata yafi na kowa yawa don Daddy yace ita ce ta raini abin sonshi.......sannan ya sanar da ita cewa zanyi aure kuma kada ta damu idan lokacin bikin ya matso har gida za'a zo a tafi da ita.

Bayan mun koma masaukin mu ne......kowa ya nufi dakin barcin sa nikam Ina makale da Hayatee....ina yi mata shagwaban wai na gaji a jikinta zanyi barci, Ummie na cewa Adda wannan diyar taki da rigima take wlhy.....dubi yanda take wa hajiyata saita gajiyar min da ita.

Adda ta kalle ni tana murmushi Mai kayatarwa sannan ta dubi Hayatee tace wai haka Hajiyarmu  dagaske jikar taki zata gajiyar dake?

Hayatee da ya'yan nata biyu sun sata a tsakiya wa zata bi acikin su.... murmushi tayi tace Ina Bayan Ummie Amma nidai Jikata bazata gajiyar dani ba.......Adda tace ahhhh Hajiyarmu wannan wayooo ne kika yima.

Hayatee uhmmm nidai kunga tafiyata taho jikata muje Koh.
Na bi Bayan Hayatee muna dariya nida ita.

********

The Next day muka koma Abuja..... after 2days da komawarmu Ina kwance a dakin mama, muna hira da Goggo da dije.....mama nata gyaran wasu tsohon kayanta, tana cewa rabon dana duba kayannan tun bayan zuwana gidana nan......Goggo na cewa Lallai sunsha ajiya Kam,......Nikam muna hira da dije Ina taya ta  murna daya daga cikin driver's din gidan Baffah wanda ya tuka motar su sanda zamu kaduna Yana sonta da aure, Dije Kam sai kunya takeji bayan su Mama sun saka baki amaganar, daga karshe tabar dakin gaba daya...mama na cewa mudai zamu sha biki, muna ta dariya.

Mama ta Ciro wasu hotuna tana cewa Allah sarki hotunan mu lokacin muna aiki a gidan gwamna......nikam na tashi Ina cewa Mama mugani Ina son kallon hotunan tarihi wlhy

Ina ta kallon hotunan 1 after the other har nazo kan wani hoto Wanda naga Kaman nasan mutun biyu na cikin hoton.......nace Mama nikam kaman nasan wa dinnan na cikin hoton nan,

Mama tace Kai Boddo kinsan lokacin da akayi foton nan ko haifan ki ba'ayi ba.

Aa Mama bawai nace alokacin na sansu ba, Ina nufin kaman na taba ganin su Amma na kasa tuna inda na gansu.

Mama tace shin muga foton nikam kin dame ni......mama takai hannu ta anshi hoton tana dubawa gabanta yayi mummunan fadi, hankalinta ya tashi, ita tarasa meyasa take zargin wani abu game da matan nan, ta rasa meyasa duk sanda ta tuna su sai gaban ta ya Fadi,.....ta daure tace Boddo baki san su ba, wannan Rahane ce ta kusa dani, ta gefenta kuma yar uwar ta ce Maman Aamir Allah sarki rayuwa.

Boddo da taji batun Mama tace Yes Ni nasan na taba ganin su...nasani wlhy Mama nasan Maman Aamir....

Mama tace a Ina Boddo, Wai Anya kanki daya kuwa?

Kaina Daya mama, maman Aamir ba tana da bille ba kuma tana da haske kadan....sannan danta Aamir fari ne.

Mama ta girgiza Kai tana gasgata abinda Boddo tace daga bisani tace kwarai tana da bille a kumatu ita da kanwar ta Rahane.....don akan kirasu da masu bille idan bazan manta ba...Toh amma ke a Ina kika san maman Aamir?

Take na baiwa Mama labarin abinda ya wakana lokacin da naje Niger State......Duk yanda mukayi da Maman Aamir sai da na zayyana Mata..... Mama ba karamin tashin Hankali ta Shiga ba....da Kuma yadda na hadu da dayar matar a wannan kyauyan lokacin da mukayi hatsarin mota, na Kuma tabbatar Mata da cewa akwai abind matar tasani game da gidan.....amma Bata Fadi  min komai ba.......dama ita tasan dole akwai abinda zaisa su bar gidan amma har yanzu ba'asan taka maimai dalilinsu nayin hakan ba ........Mama tashiga zurfin tunani mai karfi, bawai ta yadda da cewa su din bane Amma dole ta sanar da Hayatee....  ...daga karshe ta samu Hayatee ta labarta Mata komai, Hayatee tace Mama bamuga ta zama ba, ai dole aje a nemo Maman Aamir, if possible harda dayar matar....  ..bari zan sanar da Baffah zamu San Yan da za'ayi.......

Da daddare misalin karfe takwas Hayatee ta tari Ummie da Baffah akan maganan sosai suma sukayi mamakin yanda acikin labarin reaction din Maman Aamir ya canja wanda hakan na nufin akwai wani boyayyan sirri wanda dole sai an nemo ta kafin za'ayi sani....da wannan ne Baffah ya yanke shawaran zai sa atura har Niger State ataho dasu amma sai sun shirya yanda Maman Aamir bazata gane su suka sa ataho da ita ba.....ahaka suka rufe maganar.

**********

Few days later

Alhamdulillah ayau ne na kammala karatuna....kuma Ina Daya daga cikin masu first class dukda batareda da mate dina nayi graduating ba Amma naji dadin hakan at least na fita da grade mai kyau, ayanzu na zama cikakkiyar pharmacist.......Daddy ya hada min gagarumin walima wanda har sai da Yaya Hamid yazo yai kwana biyu kafin ya koma,
Daddy yace min Ina son na cigaba da karatu ko hakan ya ishe ni.

Nace Ina bukata Daddy Amma ka Bari sai nayi aure sai na cigaba a gidan mijina.....yace min to hakan ba damuwa bane ya amince.

*****

Kwanaki nata tafiya....haka zalika  shirye shiryen bikina akeyi sosai kowa yana murna Banda Ni😣 ko miye dalili ohooooo nikam bansani ba......na kasa kwantar da hankali na Kuma kasa sanya Yaya Hamid araina, ko nayi attempting saka shi araina baya yuwa.

Ana saura kwana goma biki na ango Hamid ya iso, an dauko Inna, haka zalika gidan ya fara cika da bakin su Hayatee, Friends din Hamid  suma dai shirye shirye sukeyi dukda Nabil baya bada full attention dinshi a lamarin auran....... Awannan lokacin ne aka kawo lefe na....Kuma MashaAllah lefe yai matukar kyau

Nabil shikam a yan kwanakinnan yana cikin damuwa ne,domin wanda yasa yai masa bincike a kaduna ya sanar dashi cewa yasamu kadan daga cikin labarin yarinyar dayake nema.....gashi Kuma Baffah ya matsa Masa a yan kwanakinnan akan auren diyar abokinsa, Yana son zuwa kaduna kafin bikin Amma Ina Baffah ya hana shi, Infact ko nisa da Baffah baya yi.

****************
Legislative quarters
Wednesday
9:00am

Ranar laraba itace ranar da ake samin lalle....Ina wani daki daga bangarena ana min dilka wanda yau rana ta hudu kenan da aka fara min Amma jikina ya canja sosai...ga wani sihirtaccen kamshi danakeyi ko da yaushe, Mamie bata barina nafita iyakaci na dakina sai dakinta ko falo Bata bari naje acewar ta Amarya Bata yawo.

Ina zaune ina tunanin Yaya Nabil, naji Ina bukatar ganinshi ko ta halin Yaya ne,
Bayan an gama min dilka ne misalin karfe biyu na rana, dogon hijab na zumbula na dau key din mota......sai da na fakaici idon kowa nasan babu wanda ya ganni kafin na fice daga part din Kai tsaye na nufi motor park na Shiga mota na bar gidan.

*******************

Vote!Vote!!Vote!!!
Please

WACECE NI ✔Where stories live. Discover now