Chapter 2

253 24 1
                                    

Wacece Ni?

Part 3/2

******************

Da sallama muka shiga gidan.....fili ne atsakar gidan sai dakuna biyu Wanda suke kallon bakin kofa da baranda akofar dakin sai wani Dan lungu da aka kewaye shi da falange, tsakiyar gidan kuma murhu ne aka kunna  aka daura tukunya sai turmi a gefen wata yarinya mai shekaru Goma sha biyar take ta faman daka.......gefe daya kuma na gidan wata matace zaune kasa dirshen ta shimfida buhu akasa tana ta tankade surfen gero........na share zufan Daya keto min a fuska sakamakon wahala da gajiyar da mukasha na kalli Yaya Nabil wanda ya kwanta a kafada na cikin wani mayuyacin hali, wata sallaman na kuma dokawa don da alama basuji sallaman danayi ba.

Assalamualaikum

Dukkansu suka waigo da Jin muryar da sunsan bata yan kyauyan bace, don da kallon dasuke min na gane hakan, matar  da na kura wa idanu, Hakika kamannin fuskanta ya min kaman na taba ganin ta, but I can't  recall anything tace bayin Allah lafiya wa kuke nema ne?

Kawar dazancen nayi hade dayin
Murmushi nace babu taimako zakuyi mana don Allah,
Matar mai akalla shekara Arba'in da wani Abu ta tashi ahankali hade da dogara wata sanda data  aje a gefenta tana tafiya tana dingisawa dayar kafar ashanye take.....Ashe gurguwa ce..... tana cewa  maraban ku to ku shigo mana ta shimfida mana tabarma a barandar dakin tace bisimillah ku shigo ku zauna.

Muka zauna na kwantar da Yaya Nabil kansa na saman cinya na saboda ganin halin dayake ciki,

Matar ta kawo mana ruwa tana cewa bayin Allah lafiya kuwa....shin daga Ina kuke ?

Na Kuma kallan matar Ina mamakin yadda take duk wani harkokinta bazaka taba cewa gurguwa bace, nayi kokarin kakalo murmushi take  kuma na zayyana mata labarin abinda ya faru damu, ta tausaya mana matuka tace akwai likita dayake zuwa garinnan daga kaduna Yana da clinic a cen sama dasu kadan...Munyi sa'a yauce ranar zuwanshi don haka bari ta aika a kirawo mana shi ya duba dan uwan nawa.godiya naita Mata.

Yar'ta mai suna sadiya ta aika......tsahon minti Arba'in muna zaune saiga likita ya shigo, nutsattsan mutun Mai Shiga cikin kamala dauke yake da first-Aid box dinsa dakuma briefcase dinsa....ya zo har inda muke, muka gaisa sannan na nuna masa mara lafiyan.....duba Yaya Nabil yasoma yi.

Daga bisani yace babu abinda ya sameshi kanshi ne ya bugu Wanda shi yayi causing stress dake damunshi...yace zai rubuta Mana magani mu siya.....nace doctor why not mu baka kudin ka siyo mana, mu baki ne bamu San ko Ina ba.

Matar tace abawa sadiya taje babban chemist ta siyo,haka na Mika mata kudi wanda na dauka cikin aljihun wandon Yaya Nabil, doctor Kuma ya jira, Jim kadan minti Ashirin kacal saiga sadiya ta dawo,

Cikin kankanin lokaci likita ya fara aikinsa, wanda Bai tafi ba, har saida Yaya Nabil ya fara dawo wa cikin hayyacinsa...na biyasa kudinsa yai mana sallama sannan  na koma jinyar Yaya Nabil na bashi abinci abaki kadan ya iya ci......Yaya Nabil babu abinda yakeyi sai kallo na, baya kalon kowa sai Ni....   Haka har karfe biyu da wani abu. Nayi sallah matar ta kawo mana abinci......Nai Mata godiya dukda ba ci zamuyi ba, don dasauran abincinmu a cooler.

..........................

Zuwa karfe biyar Yaya ya dawo cikin hayyacinsa, sosai yakejin karfi da kuzari ajikinsa.yace min mutafi basai mun kwana ba, don matar ta kafe akan mu kwana....  Tace ba'a samun mota Kuma akwai yan kidnappers......amma inmuka Bari gobe yayi mota har kofar gidanta za'azo daukanmu.

Haka muka bari sai washe gari.
Awannan daran Nabil Yana kofar gida shida mijin matar, sai Ni Kuma muna zaune a kofar dakin matar tana tambayana daga I muke ne?

Haka na zauna na Fadi Mata daga inda muka taho, tace ayyahhhh Abuja wani unguwa kuke don nima nayi zaman Abuja .

Nace mata Maitama.......tare da fadin direct sunan Baffah Don a Maitama babu wanda baisanshiba.....nidai da shegen surutu.

WACECE NI ✔Where stories live. Discover now