Chapter 7

293 30 0
                                    

Wacece Ni?
Story written by
DielaIbrahim ✍️

Part 1/ 7

******************

Karfe Shida agogon cikin dakin da take ya nuna don Haka ta fita da niyan yin sallah
Amma sai ta gudu Bayan ta harhada kayanta
Don tun cikin dare ta tambayi wata Nurse Ina kayanta suke
Nurse ta taimaka ta dauko Mata komai

Tun da tafita take ta uban sauri
Tama manta akwai kudi acikin Jakarta....sauri take tayi da kafanta ta taka har express by pass daganan tadau hanyar bakin ruwa
Agalabaice ta Isa wajan ta samu waje ta zauna don hutawa
Takai minti Talatin tana zaune a wajan kafin takara samun kuzarin tashi ta cigaba da tafiya

Ba ita takai kofar gidansu ba sai karfe Takwas

Tana Shiga ta iske Baba da Inna suna tayi yana Mata fada akan yawan Tallan da take dauramin
Ita Kuma tace Bai Isa ba,,, bazatayi raino a banzaba
Dole in Mata Talla ko mutuncinta xan xubar ita ba damuwanta bane

Daidai lokacin na kutsa Kai na Shiga ...Baba na ganina ya nufo ni Yana  Boddo Wanda har tuntube yayi
Boddo lafia Ina kika Shiga
Hawaye nee suka sauka a idanu na Ina tunanin irin qaunar da Baba yake min
Bansamu dama. Ansa mashi ba
Naji Inna tace

Yohh Ina xata Banda yawon karuwanci......Baba yaji xafin maganar da tayi Amma sai ya dake
Ya sake maida kallon sa ga Boddo yace Zo muje ya jata har kofar dakinshi suka zauna
Yace Boddo fada min meyasa meki Naga bandeji a goshinki
Ki kwantar da hankalinki ki min bayanin komai

Nan take Boddo ta bude Baki tafara you Masa bayani ahankali har dawowanta

Allah sarki Boddo
Boddo ki yafe min kinji
Ke amanace Allah ya bani Amma matukar na cutar dake Allah bazai barni ba
Ina matukar takaicin tasowarki a wannan gida Wanda muatanen gidan Basu sonki ko kadan
Kiyi hakuri Boddo Ni naja maki

Da sauri na katse Baba nace Baba Kai mahaifina nee
Ko wacce irin rayuwa na tsinci kaina dole in godema Allah

Baba kada ka damu komai Mai wuce wa nee kaji

Kadena kuka saboda Ni Baba
Inshallah watarana zakai farinciki Dani
Inshallah xaka ga sakayyah Baba
Kasan ance mahakurci mawadaci

Nagode ma Allah Daya bani ke Boddo amatsayin yata Ina alfahari dake Allah yai maki Albarka

Ameen Baba

Tashi muje wajan Mai shayi Kisha shayi kidanji dama dama ko Yar baba

To Baba

Suka fita suka bar Inna tana cije yatsa zaku dawo ki same Ni wlhy
Tayi kwafa ta Harare sauran matan da suke zaune a barander dakinsu ta galla masu harara sannan Tai shigewarta daki

Sai da Baba ya tabbatar da Boddo ta koshi kafin suka koma gida yace Boddo na
Na kawo maki kifi na baiwa kowa nashi kema ga naki
A Ina Zaki dafa

Tai saurin cewa a gidan Goggo
To gashi yabata wani roba
Kifin suna ta wusul wusul
Kifin tarwada nee Wanda aikin babane xuwa Rafi kullin Yana
Sa'narshi me Wanda dashi yake ciyar da iyalanshi
Gashi je ki dafo
Toh Baba na gode

Da sallama ta Shiga gidan ta samu goggo ta gaishe ta sannan tace Mata Goggo baba ya bani kifi Ina so na dafa
Toh Boddo Naga bandage a kanki meyasameki
Boddo ta Fadi Mata komai

Tace Ayyahhh sannu Koh

Kawo kifin kije ciki Yar uwarki tana ciki
Bari na daura maki

To goggo nagode

Ta Shiga dakin ta Sami Dije saman gado kwance
Take Dije ya jikin ki
Da sauki Boddo Ina kika je jiya nee ana ta nemanki
Nan itama ta Bata labari

Dije tace to yanxu kinji sauki nee
Eh da dama jikin Amma Ina bukatar kwantawa saboda magungunan da aka dirka min Basu sake Ni ba

To kixo ki kwanta Koh

Ai tana kwantawa ko minti goma batayi ba bacci ya dauke ta

Goggo ta shigo taganta tayi bacci take Allah sarki Boddo
Wlhy tausayi take bani
Dije tace Nima Goggo kullin cikin tashin hankali take

Allah ya kawo Mata karshen wahalan Nan
Ameen Goggo


***************

DielaIbrahim ✍️
Vote and Share
Pls 🙏

WACECE NI ✔Where stories live. Discover now