Chapter 15

302 27 0
                                    

Wacece Ni?
Story written by
DielaIbrahim ✍️

Part 1/15

___________________________________
After 2days
11:40

Ina zaune a qasan carpet
Dakin Hajiya
Naji anyi sallama
Na daga Kai don Naga ko waye
Wata yarinya nagani
Daga gani bazata wuce shekaru na ba

Ta gama kalle kallen a dakin Hajiya,Ta juya xata fita kenan
Sai Kuma ta fasa tayo inda nake

Kece sabuwar Yar aikin daka kawo wa Hajiya

Kai na gyada mata Alamar eh
To kixo mummy nason ganinki

Ba musu na tashi na bita
Ban tsaya jiran Hajiyar ta fitoba daga bathroom

Tafiya mukayi wanda na dauka wannan parlon da muka taba Shiga Nan zamu
Sai Kuma Naga mun canja hanya mun cigaba da tafiya dukda Ina hango flat din dànake xaton nan xamu
Akuwa muna xuwa wajan Kuma Naga Tasha kwana ta Bayan flat din Naga wasu manya manyan flat guda biyu ginin kamar upstairs  dayan na gefe Naga munshiga
MashaAllah na furta acikin Raina

Babban parlor ne tace zauna anan ki jira fitowarta
Har ta tafi sai Kuma ta dawo
Miye sunanki
Ahankali nace Mata Boddo

Tace ohk sannan ta wuce abinta

Jim kadan
Naji shigowar wani
Waigawa nayi da sauri don ganin ko waye
Wani dogon saurayi ne
Wanda shima dai kallona yakeyi

Saurin dauke idanuwa na nayi daga kanshi na cigaba da wasa da yatsun hannuna

Ya gittani ya wuce ciki

Ina Nan zaune dai sai ga mummy ta fito
Na Kara durkushewa a wajan Ina Kai gaisuwa

Ta amsa ciki ciki
Sannan tafara magana ahankali

Da alamu Hajiya na Jin dadin taraiya dake yau kusan kwananki uku kenan Amma banji wani matsala ta wajan Hajiya ba

Shuru nai Mata don bansan me zan ce Mata ba

Tadaura da cewa
To Ina fatan an fadi maki aikinki
Koh

Na amsa da eh an fadamin
To ki kiyaye

Nace inshallah ranki shi Dade
Batareda na kalli fuskanta ba

Zaki iya tafiya
Toh nagode

Na tashi na fita Ina tafiyan Ina ta kalle kallen gidajan wajan
Lallai gidan Nan a tsare yake
Ba shakka babban gida nee
Amma Kuma da àlama mutanen gidan basuda yawa

Na koma dakin Hajiya abina
Nabarwa kaina tambayana na don Mama tace ahankali xata sanar Dani komai

Dashiga na daki na iske Hajiya zaune ita kadai ta Sanya tabarau
Tana karatun jarida
Azuciyata Kuma mamakin tsohuwar nakeji
Tsohuwa Yar Boko
Zama nayi akasa kusa da kafafunta  nace sannu da hutawa Hayatee

Ahah Ina kika shigane na fito banganki ba
Hayatee Amin afuwa don Allah Mummy ce ta Aiko kirana
Ohhhhhh yayi kyau

Na zauna kenan tacemin Boddo
Kina karatun jarida kuwa
Na girgiza Kai
Tace meyasa?
Nace babu komai

Murmushi tayi tace watarana ke xanba mawa ki karanta min duka

Na zare idanu duka wanna jaridar?
Eh tabani amsa atakaice

Nayi smiling nace da ita to Allah ya kaimu
Ameen ta amsa
_

_________________________________
Kaduna,Rigasa.......makera
Bayan tafiyan Boddo da kwana biyu
Baba da Inna

Inna tun muna mu biyu a dakin Nan ki Fadi min inda kikakai Yar mutane.....
Toh ai sai kayi Mallam nidai na Fadi maka tana dawowa tace min xata fita....to dai tunda ta sa kafa ta fita kwana uku kenan ban sake sata a idanuwana ba Kuma na ce da idi ya bincika Kuma yasa ayi bincike

Ka kwantar da hankalinka mallam yarinyar Nan Naga ba karamar yarinya bace tana da wayau Duk inda taje ai xata dawo gida

Baba yai Shuru shiyasan karya Inna takeyi takai Boddo aikatau
Hawaye nee suka Dan zuba a idanuwan Baba lokacin ya na kokarin fita daga dakin
Ya tuna ranar daya samu Boddo

Ya daga hannuwansa sama yace ya Allah gaka zuciyata Banda niyar cutar da yarinyar Nan
Allah katsareta aduk inda take
Allah ka tsare min ita daga mugun ji da mugun gani
Ameen Summa Ameen

Baba yace acikin zucitarshi

Inna Hakika xan barki da halinki idan kinyi Mai kyau
Tabbas xaki gani

___________________________________
______Kaduna_____
Marafa Estate
3:00pm

Ummie na zaune ita Daya a babban gidanta
Wayar ta ta janyo tayi dailing number

Bugu biyu aka daga

Son ya kk
Cen cikin wayar aka amsa da lafiya mi mom

Hope kana lafiya nayi missing dinka tunda ka tafi yau wata uku kenan Nabil
Wai shin baxa'abarku kudan dawo bane
Ni gaskiya Ina son ganin mi son

Dariya Nabil yayi
Yace Ummie nah Nima nayi missing dinki sosai
Ummie being a Force you know it's mi dream so I have to achieve mi goal..

Ovcux mi son I knew dat and am supporting you as you can see tunda har na yadda na barka ka tafi
But kagafah shekara  Hudu
Nabil Shekara Hudu Yamin nisa gaskiya Yamin yawa da nasan hakane da banbari kun min wayau Kai da Baffah ba wlhy

Mom,Mama,Momma,
Ummie nah
Nabila ya Kira Ummie
Wannan dabi'ar shice Duk sanda xai lallashe ta yakan kirata da sunaye kala kala

Uhmmmm
Ummie taja numfashi zaka fara Koh Nabil
This time around am really serious Nabil gaskiya ka dauki hutu ko kwana biyu ne nidai kaxo kamin

To Ummie nah ni kadai
Xan xo inshallah

Ummie kina zaune ke kadai nee shiyasa kike kewana
Ummie why not ki koma gidan Baffah kawai....in Kuma baxaki koma ba sai Sweetheart dina taxo ta Taya ki zama don ita kullin saitayi magiyar dawowarki


Zan yi tunani akai Nabil
Inshallah karka damu kaji

Alright Ummie I'll hang off d phone now

Ohk Nabil Bye till then

...............


DielaIbrahim ✍️
Vote/Share please

WACECE NI ✔Where stories live. Discover now