Chapter 22

251 28 1
                                    

Wacece Ni?

Part 2/22

_____________________Maitama
Abuja,

*************

Hayatee ta dago kai arazane tana kallona hakan yayi daidai da shigowan Mama dasu Goggo da dije.

Hawaye naji yana neman fitowa a idanuwa na, ga Kuma wani matsanancin ciwan kai daya kamani lokaci guda.......  Cigaba da kallon Goggo nayi, daga bisani Kuma jiri ya fara dauka na

Na fadi ne adaidai sanda Nabil da Hamid suke shigo wa dakin Hayatee..........atare suka furta Subhanallah.

Maimakon ayi rushing akaini asibiti no, Hayatee ta dakatar dasu...Nabil please call our Family doctor, there's no need to take her to the hospital.......... hurry up

Nabil ya Kira Doctor yamasa bayani Jim kadan Doctor Hasan  ya shigo ya iske duk sunyi jugum jugum a falon Hayatee....ya nemi da a ragu a falon don Haka kowa ya fita saura Hayatee kawai.....   Yayi dube dubenshi sannan ya baiwa Nabil list na medicines din daza'a siya......cikin sauri Nabil yaje pharmacy ya siya sannan ya dawo aka fara Mata treatment.

Minti Ashirin ya dauke shi yana aikinsa kafin yagama ya musu bayani, sallama ya tafi

***************

Acikin Nabil da Hamid bazan iya cewa ga wanda ya fi damuwa da suman danayi ba, kowa adame yake burunsu kawai na farka Kuma na samu lafiya.

Few hours later
2pm to 7pm

Na farka Hayatee na fara sanyawa a idanuna sai Nabil Wanda yake zaune a dayan gefen gadon shida Ummie suna magana.... Alhamdulillah she's awake fadan Hayatee

Kafin hankalin sauran ya dawo kaina  sannu ake tamin Ina gyada kaina da kyar na iya  tashi nayi alwala nayi sallah na sallame kenan Ina addu'a mukaji sallaman Adda cike da doki da murna, kafin mukaji na Alhj. Othman shi ma dai ba'abarsa abayaba wajan zakwadin.....jikin su na rawa suka rungume ni, Wanda ni kawai ji nayi an kankame ni........sosai su biyun suke murna da kukan farinciki......batareda sun yi magana da kowa ba.

Hayatee ce ta katse su da muryar ta awannan karon muryar da fada take magana......... Kafin suka juyo da hankulan su gare.

Alhj.Othman ya tashi da sauri yana nuna wa Hayatee takaddar results tsabagen murnar dayake ciki ma ba'a Jin magananshi saboda da sauri yake furta zancen nashi......mutumin da yake da murya mai sauti kuma da dadin sauraro aduk sanda zaiyi magana Koda kuwa da fada zaiyi ta.

Hayatee ta ce......Haba Othman calm down please and talk to me,

Alhj.Othman yace Hajiyarmu jikan ki ce wlhy results ya fito Hajiya gashi....ya'tace Boddo jini na ne....she my blood....ya karashe yana hawaye

Hakika lamarin tsoro yake bani
Kuma lamarin dauremin kai yake yi....Ni Boddo yar wadinnan hamshakan masu kudi Kuma jika awajan Hayatee.....yanzu suna nufin suce su ne iyayena and .....and Adda ita ta ta dauki cikina na tsahon wata tara sannan ta tsugunna ta haifeni.....I can't believe this....Adda is my mom, "my blood mother"
"Huh😣am totally confused about this issue....  Taya zan fara yadda Nooooooooo nafada da karfi ban yadda kune iyaye na ba naja da baya Ina hawaye masu zafi da kuma kona zuciya..........Na tsugunna a wajan Ina kuka, sumbatu na farayi Ina cewa....Amatsayin yar aiki nazo gidannan kun bani dukkan abinda yà take bukata awajan mahaifanta , Hakika ina zama dakune ba don kudin ku ba, meya sa zaku tsiro da cewa ni yar' ku ce.....me kuke so mutane su dauke ni? So kuke ace na asirce ku.......ku dena don Allah bana so wlhy.

Adda ta bude Baki zatai magana Hayatee ta dakatar da ita da sauri please don't ....Bata da lafiya yanzu ta farka and karku kara mata wani confusion....ta tsagaita kafin ta cigaba

WACECE NI ✔Where stories live. Discover now