Chapter 8

230 31 6
                                    

Wacece Ni

Part 3/8

*****************************

Washegari da sassafe ogan su Nabil ya Kira su a office Shida Hamid kuma suka shirya suka je.

Meeting akayi da sauran sojojin sannan daga karshe aka turasu
Wani bangare na qasar sudan.zasu hadu da sojojin qasar tare kuma zasuyi aikin, ayanzu saura masu kwana biyu su tafi tafiyar Kuma da Basu san ranar dawowarsu ba sai Allah yayi.

Bayan sun dawo gida nee kansu yayi matukar zafi gaba dayansu sun shiga damuwa barin ma Hamid da shi ya damu yaje yaga Amaryar sa.

Nabil ya sanar dasu Baffah halin dasuke ciki, basuji dadi ba Amma yasuka iya, haka Allah ya tsara don babu yadda Nabil baiyi ba amatsayinshi na babba da adakatar da Hamid acikin masu tafiya Amma Ina sunki amincewa acewar su shima ba karamin jarumi bane bazaiyu acire sa ba.

Kiran waya kawai Hamid yayi ya sanar da iyayansa abinda ke faruwa, sunso ya kokarta yaje ko da ma bai kwana ba...Amma Yana yin aikinsu bazai iya zuwa ba don haka dole suka hakura....haka kwana biyun yayi suka tafi suna yi wa su Hayatee ban kwana.

Abangare na kuma,Ranar dànake expecting zuwan su Yaya Hamid ranar muna zaune muna hira da kannensa a falon baki....mukaji sallaman mahaifiyar Hamid wacce naji suna Kira da Dada, ba ita kadai bace ita da wasu Mata guda biyu.

Nai masu iso da falon suka zauna sannan na gaida su cikin girmamawa.

Daga bisani Dada ta soma magana tana mai bani hakuri akan yanda abubuwa suka zomin.....tun kafin naji dalilin hakurin nata, naketa faman cewa  babu komai ai.

Kaman daga sama naji sun furta cewa an tura su Hamid da Nabil wani aiki a sudan,inyi hakuri ba jumawa zasuyi ba. Sosai maganan ta daga min hankali dukda bawai na damu Hamid din yazo bane Amma da ko so dayane na gansu shida Yaya Nabil ko zuciyata satai sanyi.

Haka dai su Dada suka tafi suka barni cikin tunani, tunda daga lokacin na soma yiwa mijina addu'a sosai, kuma na kwantar da hankali na....Yan uwan Yaya Hamid suna debe min kewa sosai don suna kulawa dani yadda yakamata.

*******************

Kwanaki nata tafiya, haka kuma kwanakin suka shude kaman kiftawar ido tun ana girga kawanaki yadawo mako daga bisani yadawo wata yanzu ana maganan wata shidda kenan da tafiyan su Yaya Nabil, abin mamaki da ana waya dasu jifa jifa ana jin lafiyar su amma yanzu ko wayar tasu in aka Kira bata shiga Kuma su basa kira......bangaren Ummie kuwa ta Shiga damuwa sosai dason sanin halin da yaran suke ciki.

Haka Adda damuwan ya zame Mata guda biyu domin ta damu da yar'ta datake cen wani gari tana zaman kadaici, secondly babu labarin su Nabil ko kadan.

*************Adamawa (Yola).

Anan bangaren mu zan iya cewa mun fi Shiga damuwa akan su Hayatee dalili kuwa shine

Hamid tunda akayi aure baizo yaga Amaryar sa ba, gashi kuma daga waje mai nisa aka dauko ta....dukda sunsan ba laifinsa bane yanayi ne na aikin sa....Amma ya zasuyi da hakkin Yar mutane da ansan hakane da ba'ayi auran ba har sai sun dawo.

Haka dai kowa yake ta damuwa Ni kuwa ban isa na nuna damuwata a fili ba kullin Ina cikin boye damuwata bana taba nuna komai a fuska ta....sai ma kokarin kwantar wa Dada da hankali nakeyi saboda yanayin rayuwa.

Haka dai zaman namu ya cigaba babu wani canji kullin Ina zaune a waje daya dukda babu abinda na rasa na daga kudi da kayan abinci, kudi dai Daddynah Yana tura min akai akai kayan abinci kuwa mahaifin Hamid ke kawowa duk wata.

*************************

________________Sudan____________

Tsakiyan sahara suke inda ko digon ruwa babu, guzurin ruwan da sukayi kuma ya soma karewa saboda wahala, daga kafar sa dayan da zaiyi sai jin tashin wani bomb din sukayi wanda akusa kusa dasu ya tashi.

Dagewa yayi ya riko hannun dan uwan nasa ogan su sojan sudan bature ne shike masu jagora agaba su kuma suna baya,....ya sake kai dubansa ga sojojin dasuka rage a filin yakin Wanda kwata kwata basukai hamsin ba.....ya girgiza kai yana mai son zubar da kwalla ya tuna sojoji dari suka taho daga Nigeria...na Sudan kuma dari biyu amma yanzu duk babu su, gashi basu gama cimma nasara akan aikin da aka turosu ba ya dafe kanshi yana jin zafi da wanne zaiji da rashin lafiyar dan uwan nasa kokoh da wannan tashin hankalin dasuka shiga.......ji yayi an katse shi dacewa Ruwa ya waiga Dan uwansa ne ke magana cikin karfin hali ya kalli sojan dake gefen shi yace water please....take ya zuba ruwa ya mika masa, shi Kuma ya bawa Dan uwan nasa Yana Sha ahankali Yana masa sannu............Awannan halin ne suka isa inda suke tunanin mafi yawan mugayen mutanen anan suke rayuwa sai dai Basu ga Alamar komai ba awajan....fili ne kawai.

Tsayawa sukayi don yin shawara...Ogansu yace dasu map dinmu ya nuna mana cewa muna dai dai wajan Daya kamata Amma Kuma azahiri babu komai anan.

Gyaran murya mara lafiyan yayi yace suna kasa ahankali ya Kuma cewa inda suke zaune kenan Kuma zata iya yuwuwa ma anan suka boye mutanen....tari yayi ahankali.....Are you sure of what you are saying Major?

Yes sir am very sure, you can all check but please be careful, the place might be dangerous.

************************

Vote! Vote!! Vote !!!
Please




WACECE NI ✔Where stories live. Discover now