Chapter 14

220 29 2
                                    

Wacece Ni?

Part 3/14

______________________Maitama

9:00am

Kowa ya hallara a falon Baffah, Baffah ya aika Kiran Mummy Amma ba'a sameta ba.... murmushi yayi don plan dinshi na tafiya yanda yakamata, shikadai yasan abinda yake planning akanta.

Bayan Rahane ta zayyana ma kowa abinda tayi Kuma ta shaida cewa Mummy ne ta Sanya ta, saboda tana so Daddy ya aura kanwar ta, acewar ta idan yaga  baya da ya'ya bukatar Ya'ya ya taso Masa dole suyi anfani da wannan damar su sashi ya auri kanwarta. Shiyasa ta daura Rahane akan aikin batareda sanin Maman Aamir ba....ta karashe maganar tacewa, nasan dole daga karshe Mama za'a lakaba mawa laifin batar Nihila shiyasa na zake na aikata babban laifi ku yafe min.

Baffah yayi gyaran murya yace shin Ina kika kai yarinyar dakika sace ta?

Rahane ta cigaba kuka tana cewa, Bayan na dauketa mota na hau na nufi hanyar kaduna, Amma motar ta lalace kafin mu Isa kaduna ganin mutanen zasu iya kamani hakan yasa na soma gudu acikin daji, har dare yayi da safe na iso wani rafi wanda bansan ta Ina yayi ba anan na Sanya yarinyar ruwa ya tafi da ita, Nima alokcin ruwa ya tafi dani ya shanya ni  bakin titi, Bayan na farfadone bansan inda kaina yake ba, ban ankara ba kafin na tashi wani mota yazo da gudu ya banke ni, sai dai dayake bamai tsoron Allah bane shima, kodayaga ya jimin rauni sosai jini nata zuba akafa na, sai ya gudu yabarni awajan. 

Sai da nayi kwana Daya awajan Ina Shan azaba nikadai  kafin Allah ya turo mani wani bawan Allah Wanda shine mijina har yanzu, shi ya taimaka ya kaini asibiti. Ta goge hawayen ta, ta cigaba da cewa amma ko da muka Isa asibitin likitan suka ce kafar tawa ta rube sai dai a yanke.

Ina ji Ina gani aka yanke mani kafa, Hakika na Shiga halin tsaka mai wuya, na gwamaci mutuwa da wannan wahalalliyar rayuwar, shekara na daya Ina jinyar kafa tun muna asibiti har muka koma jinyar gida. Har dai Allah yasa kafar ta warke na fara dogarawa da sanda.

Ahaka mukayi aure da mutumin, har Allah ya azurtani da samun diya mace gatanan....ta karashe tana kuka tana sunkuyar da kanta.

Kowa na falon ya tausaya mata...

Baffah yace Lallai labarinki akwai tausayi aciki sosai, sai dai kisani Abinda Kika aikata ne Allah ya nuna maki ishara tun kina duniya, ki gode wa Allah, Daya sa kikayi rai, yanzu kina da damar dazaki nemi gafarar mutanen da Kika zalinta.....uwa uba kuma jaririyar da kika rabata da iyayenta karfi da yaji.
Yakai dubanshi ga Maman Aamir yace ke  Kuma Maman Aamir muna zaune dake lafiya kwatsam muka wayi gari bakyanan.ko lafiya?

Maman Aamir da tunda Rahane ta fara magana kanta ke kasa, tace Ranka shi Dade...kunsani Ina bangaren Hajiya Mummy ne, toh Kuma da nasan gaskiyar abinda Rahane tayi sai naji hakan baimin dadi ba, naso nazo na fada maka abinda ke faruwa Amma Hajiya mummy ta gargadeni akan idan na saki na tona mata asiri zata kashe Ni ta kashe yarona,

Ranka shi dade ku gafarceni amma Hakika inason rayuwar Dana saboda mahaifinsa yabar min amanarsa, dalilin dayasa na amince da shawaranta Amma nace Mata bazan iya zama a gidan ba.

Dukda abinda na fadawa mummy Bata yadda ba Bayan tafiyanmu saida tasa aka bimu don akashe mu, Amma Wanda ta tura yaji tausayi na ya hakura yabarmu da ranmu, na koma Niger State da zama.

Sai gashi watarana Allah ya kawo Boddo gidana, ranka shi Dade nasan ta fadi maku komai.

Baffah yayi shuru yana nazari, ya kalli Daddy yace kace wani abu Mana Daddy

Daddy ya girgiza Kai sannan yace Baffah Hakika sun zalince mu Amma bamu suka cutar ba, ita wacce sukayi wa laifin Ina so su nemi gafara awajan ta, idan ta yafe shikenan magana ta wuce idan Kuma bata yafe ba toh dole mu Mika su ga kotu.

Baffah yace kundaiji Koh, to ku nemi gafararta.

Rahane tayi mamaki taji cewa ashe Boddo ce yarinyar data cutar, tayi kuka sosai ta tafi wajan Boddo tana rokon ta Allah da annabi , haka Maman Aamir

Nace kada ku damu Hakika kudin kun taimaka min, na kalli Daddy nace Daddy Maman Aamir ta taimake ni da wajan kwana lokacin danaje  garin nemanku, Haka zalika Rahane maman sadiya ta taimake mu nida Yaya Nabil loakcin da mukayi accident, zaman danayi dasu tabbas halayensu ya canja, Kuma sun koyi darasi acikin rayuwarsu.

Daddy ka kyalesu suje kawai ni na yafe masu.

Gaba dayansu suka rungumeni suna murna, suna godiya.

Baffah yace toh su kin yafe masu Amma akwai wacce tai maki laifi, Ina sauraron dawowarta, sannan ban yarda kisa Baki acikin wannan part din ba...Ni zan yanke hukunci dakaina.

Na gyada Masa Kai nace toh Baffah.

********************

Vote! Vote!! Vote!!!
Please

WACECE NI ✔Where stories live. Discover now