chapter 3

361 42 0
                                    

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)
🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤
👩🏻KAMA DA WANE......
BATA WANE👩🏻‍🦱
💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

*Na*
*UMMU NAJMA*
marubuciyar *HAR ABADA*

*DEDICATED TO*
*AMMYN KHAIRAT(golden girl)*
*AND RUKAYYA IKRA(ummu sultan)*

Special gift to *Muhammad Karim*
*And Fenarh matar Soja*

*Wannan shafin naki ne qawata Kuma qanwata HALEESATOU Yar mutan nijar da Kuma SALEEHATOU Yar mutan Nigeria 🤣🤣🤣kuyi yadda kukaso dashi❤*

03👯

Dagowa Leesa tayi ta kalli Yanda take faman murmushi tace
"Wato bazaki bar maganan Sa'eed din nan ba ko? Duk abinda nake fada Miki bakiji kinzo kina ta cikamun kunne shi baima San kinayi ba"

" Kai Leesa nifa ba wani Abu nace ba illa matarshi da yaranshi sunada kyau shikkenan Nan fah Amman kin hauni da fada saikace wata uwata"

" Ai uwarkin ne, don wa'ican iyayen namu basuda amfani, inaso ki saka a ranki Salee duk duniya Bayan Allah ni kadaice gatan ki, nice Wanda duk duniya bazan yarda ke ba saidai idan kece Kika yakice ni daga jikin ki"

Bata fuska Salee tayi tace
" haba Leesa ta Yaya zan yakice ki daga jiki na Bayan nasan ke kadaice jini na, kece asalina, ke kadai nake gani naji dadi"

" Ta hanyar yarda da wani namiji ko a mafarki banison naji ko Naga kin amince da wani da namiji"

" Shikkenan mu haka rayuwar mu zata qare a tagayyare ba zamuyi aure ko saurayi ba? Haka kikeson muci gaba da amsa sunan kilakai?"

Murmushi Mai sauti Leesa tayi tace
" Yanzu ke Salee a tunanin ki akwai wani namiji Wanda akwai Allah a zuciyar shi ne? Ai duk halinsu daya yake idan kikaga namiji ya dage Akan soyayyar mace har ya aure ta, to sai tana da asali tana da masu tsaya Mata Wanda idan yayi Mata ba daidai ba zasu hukunta shi, amman mu waye zai Mana haka? All we have is that paper Wanda bazai mana amfani ba harsai ranar da na mallaki bindiga, ranar da zanje na dauki fansar lalata rayuwar mu da akayi wallahi bazan haqura ba"

Shiruu Salee tayi tana sauraron ta tasan ko sau miliyan zata bawa Leesa haquri ta bar zancen daukan ran iyayen su ba fasawa zatayi ba, itadai tanaso idan suna da rabo Allah ya hada fuskokin su.

Suna Gama assignment din suka fito da qur'anin su suka shigar da hadda sannan suka shiga dakinsu da nufin yin barci don Basu dogon Hira saboda tarin ayyukan da sukeyi da safe musamman a weekend.

Ta ciki suka saka kwado suka rufe qofa Leesa ta Kade musu katifar su ta sake gyara bedsheet kafin ta dauko throw pillow taje can quryan katifar ta kwanta dan ita already ta canza kayan ta zuwa shirt da wando da suke barci dashi.

Bude akwatin su Salee tayi ta Ciro nata kayan a garin haka wani paper Mai shegen kyau ya Fado jiki harda stamp da sunan asibiti, ta dauka tana karantawa kamar yau ta fara gani.

Saida ta karantashi yafi sau 10 kafin ta ajiye tana wani irin kuka ta linke shi ta mayar cikin akwatin ta rufe sannan ta raba gefen Leesa ta kwanta tana qoqarin danne kukanta Kar ya fito, Leesa ta hanata bibiyar takardan but she can't help it cikar burinkan ta kawai take fata.

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now