chapter 22

237 34 0
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)
  🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤
👩🏻KAMA DA WANE......
                          BATA WANE👩🏻‍🦱
   💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         *Na*
        *UMMU NAJMA*
marubuciyar *HAR ABADA*

*DEDICATED TO*
*AMMYN KHAIRAT(golden girl)*
*AND RUKAYYA IKRA(ummu sultan)*

_wannan shafin taki ce sis *fatima M.Y* she always says *aunty Aisha salon ki na daban ne Ina sonki sosai* Nima Ina sonki sisi nah😍😘 irin over dinnan💘 Allah ya barmin ke dear_❤️

22👯
Qofar toilet din yaje Yana knocking cikin daga murya yace "fito matsoraciyar banza kawai, kizo ki gyara wurin da Kika 'bata kada ki saka carpet dina wari don ba da kudin ki na saya ba"

Bude qofar Leesa tayi a hankali ta leqo da kanta Nan ta sake arangama da bindigar hannun shi da sauri ta koma ciki ta rufe qofar tana sauqe numfashi,

"Mtsww idan Baki fito kinyi abun da na saka ki ba sai na fasa Miki Kai ta cikin qofar Nan, kinsan zan iya ko?"

Leesa najin zancen fasa Kai babu shiri ta fito tana zazzare idanu
"To ka ajiye bindigar nan dan Allah kada ka harbe ni baka sani ba"

Bai sake cewa komai ba yayi Mata nuni da wurin da ta zubar da abinci da hannun shi, babu musu taje ta dauko tsintsiya ta share sannan ta goge ruwan da ya zuba Tass, tazo wucewa zata maida kayan aikin ya Kira sunan ta for the first time,

"Haleesa! Indai da gaske kina son koyan bindiga ki shirya neman kariya daga mutanen da ke Shirin zama Miki matsala da Kuma daukar fansar wulaqanci kaman Yanda Kika fada dole ki cire tsoron shi daga ranki, you have to focus on your goals ki jajirce ta haka ne kawai Zaki iya samun biyan buqata,

Nima a lokacin baya bani son hulda dashi, badon Ina tsoron shi irin naki ba no! Sai dan Ina qyamatar shi saboda Yanda ake amfani dashi wurin daukan ran bayin Allah, ya zamo dole ma duk wani babban magajin Mailafiya family ya zamo ya mallaki bindiga saboda tsaro, Amman a lokacin bani dashi sai gashi yanzu qaddara ta saka sun zamo abokan rayuwa ta, so it's left to you ki xaba tsakanin tsoron ki da Kuma burin ki"

Ya miqa Mata qaramar pistol "ga wannan ki ajiye a wurin ki, Kar kiji tsoro babu bullet a ciki, idan kin samu dama kiyi rehearsing training din da mukayi ni zan fita daman shi ya tsayar dani"

Karba tayi ta Masa godiya duk gabobin jikin ta sun mutu, Bai Bata lokaci ba ya fito cikin shigar shi all in black as always ya fita daga gidan tayi mishi rakiyar idanu zuciyar ta Yana kokwanto,

Anya kuwa abinda nake Shirin yi dai_dai ne? Idan na cutar da Sa'ood nayi abin da ya dace ko kuwa? Shi ba kamar Sa'eed bane beyi kalar mugaye ba ko dayake ance mugu bayi da Kama Amman a duk zaman da mukayi tare Bai taba qoqarin cutar da ni ba dukda kuwa baisan ni waye ba, Amman Anya Sa'eed Bai fada mishi mu 'yan uwan shi bane shiyasa yayi saurin bani labarin kanshi saboda na fallasa mishi ni wacece? Anya ma kuwa labarin da ya bani gaskiya ce ko kuma zama kawai yayi ya tsara labarin saboda wani quduri nashi? Yaya akayi Sa'eed ya kasance mugun Sa'ood Kuma mutumin kirki Bayan kamar su daya? Tabbas KAMA DA WANE BATA WANE but something is definitely wrong here,

**********

Zarah ta Gama share tsakar gidan ta sunkuya zata kwashe dattin taji muryan Salee a saman ta,
"Momyn al'amin Ina kwana"

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now