chapter 15

238 42 4
                                    

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)
🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤
👩🏻KAMA DA WANE......
BATA WANE👩🏻‍🦱
💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

*Na*
*UMMU NAJMA*
marubuciyar *HAR ABADA*

*DEDICATED TO*
*AMMYN KHAIRAT(golden girl)*
*AND RUKAYYA IKRA(ummu sultan)*

Wannan shafin naku ne aunties dina masu cin tuwo da alqalami😜 dearest

* Aisha Alto*
And *Real smasher*
Ina Muku son so fisabilillahi💓💞

15👯
Har dare mutanen alhaji Basu Sami Leesa ba suka koma suka sanar dashi, a cikin Daren ya tada ma madam hankali a ta nuna musu inda ta samo ta,

Bilkisu da sauran'yan dakin su Leesa kuwa kuka kawai sukeyi Dan babu shakka sun tabbatar Leesa ta Shiga cikin bala'i da masifa Dan abinda zai hana su raba ta da rayuwar ta saidai idan basu same ta ba,

Sun bincika cikin Jakarta ko zasu samu wani Abu da zai nuna musu inda take ko ta fito Amman babu komai Bayan kudi da Kaya (masu karatu kaman Kun manta ta bar takardan da aka tsince su da ita a wurin Salee sarqanta kawai ta dauka),

A cikin Daren aka tafi gidan hajiya me Kai yara aikatau ta nuna musu gidan su Ameerah, suna Isa suka balla qofar gidan suka Shiga sannan wasu daga cikin su suka shiga har daki suka tunkudo qeyar maman Ameerah harda babanta da baisan komai ba da Ameerah da qannen ta duka aka tarasu a tsakar gida ga bindigogi ta ko Ina an saitashi a kawunan su sannan aka fara musu tambayan inda Leesa take,

Ranar sunga tashin hankali Dan Saida sukayi fata_fata da komai na gidan sannan suka dauki Ameerah suka tafi da ita sai sun fito da Leesa kafin a sake ta Dan harga Allah Ameeerah Bata San gidan su ba a jigawa, iyakan qawancen su makaranta don kowa tsoron zuwa gidan su Leesa yake yi shiyasa ma Basu sani ba,

**********
Har 12:30 idon Leesa biyu ta kasa rintsawa tana tsoron kada tayi bacci wannan mugun ya harbeta, cikin baqaqen Kaya da baqin gloves ga baqin facing cap da baqin mask Sa'ood ya fito da jaka Mai dauke da kayan aikin su ya zauna a kujeran gefen Leesa Yana saka bullet a bindigan hannun shi don a tunanin shi barci takeyi Yanda ta qudundune cikin blanket,

Numfashin ta ne kawai be dauke ba ita tasan yau kwanan ta yazo qarshe Dan tabbas wannan bindigar ita za'a kashe da shi, tashi tayi ta zauna tana kuka kaman Allah ne ya aikota Sa'ood kuwa kallon ta kawai yakeyi ya rasa wani cuta ne yake damun qwaqwalwar yarinyar Nan,

Cikin sheshsheqar kuka tace "kawu Dan girman Allah ka rufa min asiri ka tausaya ma qanwata wallahi ni kadai na rage Mata ba Dan ni ba Dan Allah kada ka kasheni wallahi ko menene kakeso zanyi maka"

Tsaki kawai Sa'ood yaja ya rataya jakarshi yayi ficewar sa tana ganin haka ta sauqe ajiyar zuciya ta ci gaba da kasa kunne ko zataji fitar motan su ta samu Daman tserewa Amman shiru,

Kafin su qarasa inda zasuyi aikin Saida Sa'ood yasan Yanda yayi ya saka ma KB sedative a wine yasha sannan suka tafi, Basu dade da Kai farmakin ba sedative din ya fara aiki idon KB ya fara rufuwa ga wani nannuyan barcin da yake ji ya zube a qasa hakan yasa hankalin yaran shi ya koma wurin shi,

Da qyar Sa'ood suka Sha a hannun opponent dinsu saidai ya gode ma Allah da basuyi nasaran cutar da mutanen da basuji ba Basu gani ba, can wuraren asuba Bayan komai ya lafa, su Sa'ood suka tallafo KB zasu tafi dashi babu zato ba tsammani suka ji ruwan alburusai a sama haka suka sake KB a qasa suka fara musanyar wuta a garin haka aka harbi Sa'ood a kafada, Saida sukayi da gaske suka samu barin wurin,

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now