chapter 6

256 35 0
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)
  🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤
👩🏻KAMA DA WANE......
                          BATA WANE👩🏻‍🦱
   💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         *Na*
        *UMMU NAJMA*
marubuciyar *HAR ABADA*

*DEDICATED TO*
*AMMYN KHAIRAT(golden girl)*
*AND RUKAYYA IKRA(ummu sultan)*

Special gift to *Muhammad Karim*
       *And Fenarh matar Soja*

06👯
Da azama ya qarasa wurin ta Yana faman riqo ta Amman sai qwace wa takeyi
"Sa'eed haka zamuyi dakai? Duk Sona da kake fada kanayi Ashe na qarya ne irin tozarci da cin mutuncin da zakayi min Kenan?

Sa'eed karuwa fah, yaushe ka fara bin karuwai ba tare da sanina ba har ka mallaki Daya tana kawo maka abinci gida? Duk abinda zai shiga tsakanin mu bani tauye maka hakkin ka ko?"

"Zarah Mai kike nufi ne?"

"Ai bazaka San Mai nake nufi ba Sa'eed, tunda ka riga ka cuceni ka Gama tambada ni a gari dole kace baka san Mai nake nufi ba, yanzu haka makwaftar mu matar Mai shago ne ta Kira ni naje Naga zahiri ita tazo ta ajiye Kai Kuma kaje ka dauka duk Akan idon na kuma Dan rashin mutunci aci a gidana a mayar Mata da kwano daga baya a zaga a lalube ta"

"Zargi na kike yi kenan z..."

"Wallahi wannan yafi qarfin zargi tunda ganau nake ba jiyau ba nidai Allah ya Isa min bazan yafe ba"

"Haba Zarah nasan na nemi Mata a baya Amman kafin nayi aure ne idanma ci gaba zanyi na rasa wa zan Nima sai Salee wannan kwailar?"

" To wa ya sani? Wa ya San maka, sunan ta Kenan Salee ko? Ubanta zanci wallahi sai ta fadamin dalilin da yasa ta rabi mijina" ta qarasa tana share hawaye Bata bi ta kanshi ba ta yi hanyar dakin ta da sauri ya ajiye food plask din hannun shi ya Sha gabanta.

"Please mi Alma don't add to my problems, na fada Miki babu abinda ke tsakani na da Salee Bayan abincin da take bani nake shigowa naci a Kan idon ki Dan kada kice na shiga hakkin ki wlh babu komai a tsakanin mu, shima bani na saka ta kawowa ba ra'ayin kanta ne"

"Nima ai bance Kai kake saka ta ba, Amman cin Amana ta ne anayi baka da wani evidence din da zaka wanke kanka dashi, ka cuceni Sa'eed Allah sai ya sakamin"

Bai sake ce komai ba ya fita daga gidan sannan ya dauki hanyar gidan su Salee for the first time in his life, yasha mamakin nisan tafiyar da yayi dan Kwatancen gidan akayi mishi Amman haka yarinyar Nan take jigila a wurin har sau biyu Rana.

Yana Isa qofar gidan ya fara cin Karo da 'yammata da samari suna aikata badaqalar su da ranan Allah babu kunya babu tsoron Allah, qyamar Salee da qyamar gidan da abincin su da yaci ne ya taso Masa Yana ji kaman ya amayar da hanjin cikin sa,  da yasan daga irin wannan gidan abinda take ci yake fitowa da baici ba.

Haka ya daure ya tura ayi mishi sallama da ita, da yaro yashiga gidan yace ana sallama da Salee Saida kowa ya Sha mamaki dan basu taba ji ko ganin irin haka ba koma waye zurmowa ciki kawai yake yi ya gama abun da ya kawo shi ya fita.

Jin abin da yaron ya fada yasa Leesa dake dake tsince shinkafa a qofar dakin su tayi saurin dagowa tana tambayar inji wayene.

"Wai inji Sa'eed"

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now