chapter 26

206 34 3
                                    

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)
🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤
👩🏻KAMA DA WANE......
BATA WANE👩🏻‍🦱
💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

*Na*
*UMMU NAJMA*
marubuciyar *HAR ABADA*

*DEDICATED TO*
*AMMYN KHAIRAT(golden girl)*
*AND RUKAYYA IKRA(ummu sultan)*

Special gift to *Muhammad Karim*
*And Fenarh matar Soja*

26👯
Cike da mamaki take qare ma Salee kallo tun daga fuskarta har Kan cikin ta dake shafe kamar babu komai a ciki zuciyar ta Yana bugawa da qarfi, yanzu 'yar uwarta cikin wannan mayaudarin Sa'eed din take dauke dashi? Kafin tayi wani magana taji muryan bello Wanda tasa yayi Mata gadi Yana fadin

"Aunty Haleesa ga Mai gidan dawowa"

Cikin hanzari tace "Zaki bini ne ko ba Zaki bini ba"

"I'm sorry Leesa Amman gaskiya bazan iya barin Sa'eed ba ki tsaya yazo ayi komai a gaban shi ya qare ya kaimu wurin iyay....."

Bata Bari ta qarasa magana ba ta fisge hannunta ta fita da gudu, Yanda Salee tayi qoqarin binta sai faduwa tayi Akan cikin ta lokaci daya ta saki wani azababben qara da gudu Zarah Tayo kanta dai_dai lokacin Sa'eed da baba alhaji suka shigo,

Leesa tana fita ta Shiga wani lungu dake Bayan gidan ta buya, har suka fito da Salee Sa'eed ya dauko ruwa_ruwa suka qarasa jikin motar baba alhaji dake farkon layin suka sakata a saba'in driver yaja motan suka wuce asibiti,

Leesa na ganin haka ta fito tace ma bello yayi sauri ya bisu a baya yaga wurin da zasu kaita gaba daya hankalin ta a tashe yake,

**********

Da murmushi dauke a fuskar shi ya shiga dakin, ganin shi yasa ta daddafa da hannuwanta ta tashi ta zauna itama tana murmushi,

Qarasawa kusa da ita yayi Yana fitar da dariya Mai sauti, ya matso daff da ita sannan yace
"He is gone cariño, Garba TK ya tafi na kashe shi"

Cikin zafin nama ta dauke shi da Mari tana fitar da huci Mai zafi da qyar ta iya furta "shame on you"

Ta cukumo wuyan rigan shi ta tura shi gefe, da yatsan ta tayi mishi nuni ya fita, a firgice ya dago Yana kallon ta kwata_kwata baiyi tsammanin haka daga gareta ba, ya dauka zatayi murna sosai idan tasan ya kashe maqiyin su Amman sai akasin haka yake gani,

Qara matsowa kusa da ita yayi Yana qoqarin riqe hannun ta,
"Cariño we should celebrate, na riga na karba Mana hakkin mu Bai Kamata ace kin ci gaba da fushi dani ba,"

A tsawace tace " ka fita nace" sai Kuma ta hau tari ba qaqqautawa duk da haka bata bar ture Sa'ood daga jikin ta ba sai dafe qirjin ta takeyi tana Jin Yanda yake mata ciwo,

Da sauri Sa'ood ya fita Kira doctor daga wurin Kuma ya wuce gida don yasan ko ya koma ba sauraron shi zatayi ba, Daman daga tasha wurin ta yazo ya shaida Mata wannan labarin Mai dadi kafin yaje gida,

Ranshi a bace ya bankade qofar parlorn ya Shiga, yafi 4 minutes sai zagaye yake yi hannun shi riqe da kanshi Yanzu Bai San ta wani hanya zai bullo ma mamanmu ba, bayi son duk wani abun da zai 'bata Mata rai har ya 'daga Mata ciwon ta,

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now