chapter 11

235 34 0
                                    

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)
🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤
👩🏻KAMA DA WANE......
BATA WANE👩🏻‍🦱
💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

*Na*
*UMMU NAJMA*
marubuciyar *HAR ABADA*

*DEDICATED TO*
*AMMYN KHAIRAT(golden girl)*
*AND RUKAYYA IKRA(ummu sultan)*

*Happy confusion clique*🗣️🗣️🗣️

Your attention is needed here🤣🤣🤣

Haleesa=Leesa=eldest=Mai bindiga
Saleeha=Salee=youngest=burin Sa'ood Kuma matar Sa'eed
NO MORE CONFUSION PLEASE 🙏🏼😅

Wannan shafin naku ne
*Sis bahijja*
*Farida magaji*
*Fatima*
*Hauwa baba tunde*
*Maryam milo*
And finally my little sis *khadeejah Muhammad (mmn jawad) love you all😘

11👯
8:02pm

Da motan Nabeela da na Idris akayi Kai amarya irin mutanen da ta gani tare da amaryan ya Bata mamaki, ya Sa'eed a wani irin gida ne ya nemi aure haka? Taso ta fada ma Idris abubuwan da ta gani Amman ba zataso wani Abu ya sake samun Sa'eed ba, tasan mijinta qiris yake jira ya tada rigima.

Tunda aka daura aure Zarah ta qule a cikin daki tana risgan kuka gashi Sa'eed bayi Nan Islam Kuma tana wurin Nabeela, al'amin kawai aka Bari da aikin rarrashi,

Bata taba tsammanin zata tsaya takara da wata mace a zuciyar Sa'eed ba ko lokacin da yake da arziqi Amman saboda wulaqanci shine Sa'eed zai Mata kishiya a cikin talauci, Daman rayuwar Yaya aka qare manage suke yi yanzu tsiya zai qaru a Kan na baya,

har qawayen amarya suka Gama Shan zaman su suka watse babu ango babu abokan shi, tun Salee na baza idanuwa har barci ya dauke ta tana zaune tana faman tsiyayar hawaye, Allah yasa Sa'eed ba wani abu bane ya samu Sa'eed din gashi Bata da waya ballantana taji ko Yana lafiya,

Zarah na labe a jikin window tana jiran taga wucewar Sa'eed dakin amarya Amman shiru har qarfe 1 idonta biyu ta kasa samun nutsuwar barci, tana so ta tabbatar ma kanta yaufa Sa'eed ya zamo ba nata ita kadai ba, yau idan Sa'eed ya shigo gida dakin wata zai kwana ba dakin ta ba,

Ganin shirun yayi yawa yasa ta dauki waya ta Kira shi, kaman jira take bugu daya ya dauka, rasa me zata fada mishi tayi shima sai ya tsinci kanshi da Jin nauyin ta yasan rashin dawowar shi gida ne yasa ta Kira shi,

Tattaro Dan qarfin guiwar ta tayi tana qoqarin yakice kishin sa daga cikin ranta, murya a sanyaye tace
"Ya Sa'eed Yaya har yanzu baka dawo gida ba? Ka San amarya tana jiran ka ko?"

Cikin wani irin murya yace "I'm sorry mi Alma uzuri ne ya taso min ki Bata haquri please sai gobe da safe zan dawo"

" Ina dai lafiya ko?"
"Kada ki damu Lafiya qlau"

Sauqe numfashi tayi tace " to Allah ya kaimu goben, bye"

" bye, love you"

"Uhm_hmm" kawai tace ta katse Kiran, tana Jin tausayin Salee cikin ranta, ta San da ciwo ace ango baizo wurin amarya a Daren auren su ba, ta rufe qofarta ta kwanta, da qyar ta samu barci yayi awon gaba da ita.

**********
Nabeela ce tsaye a jikin mirror sanye da kayan barci tana tace gashin kanta, Idris na zaune ya jingina kanshi da gado Yana kallon bayanta,

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now