chapter 16

224 33 2
                                    

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)
🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤
👩🏻KAMA DA WANE......
BATA WANE👩🏻‍🦱
💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

*Na*
*UMMU NAJMA*
marubuciyar *HAR ABADA*

*DEDICATED TO*
*AMMYN KHAIRAT(golden girl)*
*AND RUKAYYA IKRA(ummu sultan)*

Special gift to *Muhammad Karim*
*And Fenarh matar Soja*

16👯
Rungumo ta jikin shi yayi Yana patting bayanta a hankali,

"Ki kwantar da hankalin ki please insha Allah babu abinda ya samu Leesa Hala Bata samu kudin bane shiyasa bakiga saqon ta ba, tun jiya kike daga hankalin ki for no reason ki qara haquri kadan zakiji daga gare ta"

Girgiza kanta tayi tace "no ya Sa'eed nasan halin Leesa fiye da kowa a duniyar Nan tafi damuwa dani a Kan rayuwar ta, tasan idan naji shiru Dole na Shiga damuwa so Ina da tabbacin ko bata samu kudin ba indai tana cikin qoshin lafiya zata turomin letter Dan Allah ka taimaka min na nimo ta na roqe ka"

"Ok shikkenan zansan abinda zanyi but please cool your mind kada ki qara ma kanki rashin lafiya insha Allah zan samo Miki ita kinji?"

Gyada Kai tayi ya Kai Mata peck a goshi sannan ya fita daga gidan, duk abinda sukeyi a kan idon Zarah, daga jiya kadai da Salee ta Shiga tashin hankali gaba Daya weathern gidan ya canza kowa bayi cikin walwala harda Islam ma,

Komawa dakin ta tayi ta cigaba da kwanciya tana Jin gaba daya jikin ta na Mata tsami, Zarah ta shigo ta zauna a gefenta tana qare Mata kallo,

sosai taji tausayin ta ko babu komai Salee ta damu da ita Kuma tana girmama ta tana Mata hidima batasan lokacin da ta samu matsuguni a cikin zuciyar ta ba, Koda Sa'eed zai sota ba zata dauke ta a matsayin kishiya ba saidai qanwa don yanzu matsayin ta ya wuce haka a wurin ta,

Cikin muryar tausayawa tace "auntyn yara me kike so a kawo Miki ki ci?"

Girgiza Kai tayi ba tare da ta motsa ba a hankali tace "babu komai momyn al'amin bani Jin yunwa"

" toh" kawai tace ta fita daga dakin, tana zuwa zata Shiga dakinta saiga Islam da al'amin sun shigo da gudu kowa da uniform din makarantar boko a jikin shi,

Murmushi Zarah tayi ta bude musu hannuwan ta suzo tasan yanzu suna buqatar ta tunda Salee bata da lafiya Amman kaman ma Basu lura da rayuwar ta a wurin ba suka wuce dakin Salee da gudu suka dale jikin ta suna Mata sannu da jiki,

Sandarewa Zarah tayi a wurin very shocked she can't believe that her own children ignored her for another woman, ko mafarki takeyi ne? Yau yaranta sun Sami damar da suka Dade suna tsumaye daga gareta Amman sun watsar saboda matar ubansu? Wani irin spell ne Salee tayi casting musu har ta samu ikon karkatar da zuqatan su cikin qanqanin lokaci haka?

**********

Tunda Sa'eed ya koma kasuwa ya kasa samun sukuni gaba Daya matsalan sani ya addabi zuciyar shi, tsoro da fargaban abinda zaije ya dawo idan Idris da Sa'ood suka Sami labarin ya auri Salee har Allah ya tsaga rabo a tsakanin su,

Duk matsalan da salee take fuskanta a rayuwar ta shine sanadi tun daga na farko har na qarshe, badan shi ba da basuyi nesa da gida da kuma iyayen su ba, saboda shi sukayi hannun riga ita da 'yar uwarta har yau bata dawo ba kuma basu san a wani hali take ciki ba,

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now