chapter 49

229 38 7
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)
  🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤
👩🏻KAMA DA WANE......
                          BATA WANE👩🏻‍🦱
   💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         *Na*
        *UMMU NAJMA*
marubuciyar *HAR ABADA*

*DEDICATED TO*
*AMMYN KHAIRAT(golden girl)*
*AND RUKAYYA IKRA(ummu sultan)*

Special gift to *Muhammad Karim*
       *And Fenarh matar Soja*

49👯
Da dingishi take takawa zuwa inda Salee ke kwance Amman saboda nisan wurin kafin ta qarasa wani yaje ya Kira Sa'eed da gudu yayi kanta bai tsaya wata_wata ba ya ciccibeta yayi bedroom dinshi da ita, Yanda take juyi a jikin shi tana kuka ga jini dake ta kwalala yayi matuqar daga mishi hankali,

Suna Shiga yasa qafarshi ta baya ya rufe qofar sannan ya kwantar da ita a Kan bed dinshi ya cire Mata kayan jikin ta ya tattaro kayan aikin shi ya fara Bata taimakon gaggawa,

sunfi 1 hour a ciki babu labarin Salee Babu duriyan Sa'eed mutane sunyi jingum_jingum ana jiran tsammani wa'inda abin ya faru a gaban su sai kuka sukeyi, Babu kaman Zarah da mamanmu da suka shaida irin wahalan laulayin da Salee take sha da Kuma tashin hankalin da ta Shiga a first miscarriage dinta,

**********

Zame 'dan kwalin kanta yayi, ya zaro kadan daga cikin gashin kanta da yasha gyara, ya nannade shi a yatsar shi manuniya Yana wasa dashi,
"Baki bani amsa ta ba novio, yaushe zasu kaimin ke ne?"

"nifa ban sani ba ya Sa'ood wallahi nasan yanzu Haka mama tana ta nema na idan na koma bansan Ina zance Mata naje ba"

Dan kawar da kanshi yayi ya furzar da iska sannan ya maido da duban shi gareta yace
"Na riga na fada Miki duk Wanda ya tambaye ki daga Ina kike kice wuri na Kika zo, ni mijinki ne kowa ya shaida hakan to menene abun damuwa Dan mun kasance tare?"

" Ya Sa'ood ma maman kake so nacewa wurin ka nazo? Baka Jin kunyar ta ne? Kaifa a matsayin 'danta kake"

" Ai itama tasan tun da ta bani 'yarta na aura dole ne mu kasance tare ko a gaban idonta ko a Bayan idonta, so menene a ciki Dan kin fada Mata daga wuri na kike? And one more thing, a gaskiya ni na gaji da ya Sa'ood dinnan kina Kiran sunana kaman kina hamma, please find a sweet and lovely name for me"

Haleesa ta bude Baki zatayi magana sukaji qaran doorbell, ta juya zata je budewa yayi saurin jawota Yana galla Mata harara,
"A haka ne Zaki je bude qofa ko Dan kwali Babu a kanki ga kafadan rigan ki duk ya sauqa qasa? Ko kina so tun yanzu ayi tunanin wani abu ne?"

Sunkuyar da kanta Haleesa tayi cike da kunya, yayi Dan murmushi da yaga haka lokaci daya Kuma Yana Jan tsaki baisan wani dan rainin hankalin bane yake so ya katse mishi Jin dadi, kafin ya qarasa qofar aka sake ringing doorbell ya sake fusata ya bude qofar fiskar shi a daure Yana so yaji menene take damun shi a Kai,

Ganin Ummi tsaye fuskar ta dauke da damuwa yasa in a concerned voice yace "Yaya ne Ummi? Wani Abu ne ya faru?"

"Ya Sa'ood Salee ne ta Fado daga stairs, yanzu haka she is in critical condition Dan tunda ya Sa'eed ya Shiga da ita ciki zai duba ta har yanzu Bai fito yace Mana komai ba"

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now