chapter 42

186 33 3
                                    

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)
🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤
👩🏻KAMA DA WANE......
BATA WANE👩🏻‍🦱
💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

*Na*
*UMMU NAJMA*
marubuciyar *HAR ABADA*

*DEDICATED TO*
*AMMYN KHAIRAT(golden girl)*
*AND RUKAYYA IKRA(ummu sultan)*

*Wannan shafin taki ce ke kadai Momyn twins AKA Mrs zanna💖 kiyi yanda kika ga dama dashi🤩*

42👯
Shi abin tausayawa ne abin tallafawa Amman wasu mutane sukan dauke shi kaman bayi da muhimmanci su cuce shi, su hantare shi, basu san zasu iya rasa rahamar Allah saboda hakan ba? Meyasa mutane ba zasu zauna suyi tunani idan Suma suka mutu 'ya'yan su zasu iya Shiga irin wannan halin ba?

Ka ko kin taba tunani idan ka mutu akwai Wanda zai kula da naka ko naki yaran? Kuma wani irin riqo za'ayi musu? Tabbas duk abinda kayi shi za'ayi maka ko baka so ba, ba sai ka hada ya Kai dubu 'dari ba, ba sai ka Tara Kaya sunkai kala hamsin ba, ba sai abincin da zaka bayar ya Kai buhu goma ba, ko cikin Wanda suke zuwa makarantar gwamnati ka biya was kudin P.T.A Allah zai biya ka, idan ka Sami Mai Jin yunwa ka bashi abinda zai wadatar da cikin shi Allah zai biya ka, Wanda yake zaune bayi da aikin komai ko zare da alluran dinkin takalmi ka siya mishi ya fara bi gida_gida Yana samun halaliya Allah zai biya ka kuma ya Buda maka taskar arziqin ka,

Cikin suratul baqara Aya ta 215 Allah yace
بسم الله الرحمن الرحيم
و يسألونك ماذا ينفقون قل ما انفقتم من خير فالوالدي ولاء قربين واليتاما والمساكين

Suna tambayar ka me zasu ciyar kace duk abinda Zaku ciyar na alkhairi to kuciyar da iyaye, makusantar ku dangi, sa'annan *marayu* da miskinai,

Sa'annan cikin suratul baqara Aya ta 220 Allah yace
و يسألونك عن الائتمان قل اصلاح لهم خير

Suna tambayar ka Akan al'amarin marayu kace kyautata musu alkhairi ne, ku Sanya arziqin ku cikin kasuwancin da bayi da faduwa, ku nemi yardar Allah ta hanyar kyautata ma maraya, shuwagabanni kuji tsoron Allah alumman ku kiwo ne Allah ya Baku Kuma abin tambaya a kanku ranar alqiyama, 'ya'yayen ku suna Hawa manya manyan motoci, sun saka tufafi na alfarma marayu Kuma suna barci da yunwa, ruwa, Rana da iska duk a kansu yake qarewa, ku rage ko kashi Daya ne daga cikin nasu ku tallafa Mana dashi tabbas Allah zai biya ku"

Share guntun hawayen dake idon shi yayi cikin nutsuwa ya ninke takardan hannun shi sannan ya sauqa daga Kan stage din aka saka qabbara, sautin Allahu Akbar ke tashi ta ko wani kusurwa har sai da babban malamin da aka gayyata zaiyi fashin baqi ya hawo Kan stage kafin aka sarara,

Shima sallama yayi ya gabatar musu da kanshi sannan ya fara da " daga Abu huraira Allah ya qara masa yarda yace manzon Allah s.a.w yace (me daukan nauyin maraya nasa ko na waninsa no da shi kamar haka ne a cikin aljannah, wato kamar yatsar tahiya da babba)

An riga an bashi guarantee na Shiga aljannah Kenan, na San duk cikin mu a nan Babu Wanda bayi son Shiga aljannah to ga dama ta same mu dama Mai matuqar sauqi dukda akwai dawainiya a cikin ta Amman duk Wanda zai iya ciyar da iyalansa ciyar da Mara guda Daya tol ba zai gagare shi ba, idan Kuma mutane kuka watsar da wannan damar kuka aikata zalunci ma maraya to fa Allah ba zai barku ba tabbas Zaku Shiga ciki uquba da tsananin azaba ranar qiyama,

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now