chapter 44

200 35 12
                                    

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)
🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤
👩🏻KAMA DA WANE......
BATA WANE👩🏻‍🦱
💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

*Na*
*UMMU NAJMA*
marubuciyar *HAR ABADA*

*DEDICATED TO*
*AMMYN KHAIRAT(golden girl)*
*AND RUKAYYA IKRA(ummu sultan)*

Special gift to *Muhammad Karim*
*And Fenarh matar Soja*

*A page din jiya nayi mistake wurin numbering, na saka 42 instead of 43 sorry for the errors*

44👯
"Eh ai ka jini, nace maka akwai wani daban Wanda nake so ba Kai ba"

Dafe qahon zuciyar shi Sa'ood yayi Yana Jin kaman ana cakka mishi mashi a kanta murya can qasa yace "da gaske kina son wani daban Haleesa? Me ya fini dashi?"

Bushewa da dariya tayi Jin Yanda ya marairaice murya kaman yaro Mai kwadayi tace "wasa nake maka ya Sa'ood, ai ni bankai na soyayya ba tukunna tunda kaga ba Nan kusa nake da niyyar aure ba, Babu wani saurayin da nake dashi"

"To meyasa ba Zaki aure ni ba? Nayi Miki alqawarin Zan barki kiyi karatu Mai tsayi har sai ke da kanki kince ya ishe ki, ko PhD Kika ce kina so Zan taimaka Miki kiyi i just can't hide it anymore, I love you so much Haleesa please help me ki zamo tawa I will love and cherish you till forever, please think about it zamu zama kaman Sa'eed da Saleeha shi Yana Kama da ni ke kina Kama da ita and they are in Union, so we should also be in Union please"

Qudunduwa cikin duvet Haleesa tayi tana dariyan Jin Dadi, dalilin da yasa Bata son Sa'ood tun farko saboda Yanda take Abu da izza da gadara a Yanda zuciyar ta take tana buqatar lallami da nutsuwa a yanzu, tasan da ta amince mishi da tuntuni ya Dade da tarwatsa ta, Amman yanzu a shirye take ta bashi wuri a cikin zuciyar ta finally itama zata 'dandana abinda su Salee suke ji a soyayyar Nan,

"Umm? Yaya naji kinyi shiru? Please tell me Zaki bani wuri a cikin zuciyar ki? Even if it's a little"

" To ka Bari sai na tambayi mama tukunna idan tace na kula ko shikkenan"

Qwalalo Ido yayi kaman tana kallon shi yace "ra'ayin zuciyar naki ne sai kin tambayi mama?"

" Eh Mana to Ina da uwa a Raye me zaisa nasha wahala? Idan ta nine bansan amsan da Zan baka ba wahalar da kaina kawai zanyi Amman ita duk abinda tace min shi zanyi,"

" Oh I see, shikkenan sai da safe kiyi mafarki na please"

" Sai na tambayi mama"

Kaste Kiran yayi Yana dariya, wasu halin na Haleesa a jinin ta yake ba zata taba Bari ba har abada, irin Maganganun ta Kai tsayen Nan da wasu shaqqiyanci saidai yayi haquri da su idan har Yana son zaman su ya daure da ita,

Saida ya Gama narkan dariyan shi sannan ya dauki wayar shi ya tura Mata text ya kashe bedside lamp ya kwanta,
Haleesa tana kwance ita kadai sai maimaita Maganganun su takeyi tayi nata tayi nashi sai ta kwashe da dariya, qaran da wayar ta yayi ne yasa tayi saurin tashi ta zauna tana dubawa, hannun ta har Yana rawa ta bude text din da ya turo Mata,

'''with all my heart and soul, I write to you to let you know that you are my life and my true love, since the time you came in...my life has changed for good, there is a feeling and need of being with you every time and that is because I'm most comfortable with your company, with you...i am at ease and I want to share everything with you that's why I want you to be my señora (mrs) good night my heart, good night my soul, good night my love'''

KAMA DA WANE....(Completed)Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang