chapter 27

209 37 5
                                    

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)
🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤
👩🏻KAMA DA WANE......
BATA WANE👩🏻‍🦱
💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

*Na*
*UMMU NAJMA*
marubuciyar *HAR ABADA*

*DEDICATED TO*
*AMMYN KHAIRAT(golden girl)*
*AND RUKAYYA IKRA(ummu sultan)*

27👯
4:34pm
A main parlor na gidan Idris suka taru kowa na zaune a qasa suna facing baba alhaji dake make a kujera zai musu shari'a, Sa'ood shi kadai sai banbami yakeyi ranshi ba qaramin baci yayi ba da aka Hana shi kashe Sa'eed,

Salee kuwa ta maqale a jikin Sa'eed dan gaba daya kallon baqi take musu Zarah tana kallon su a haka amman babu Yanda ta iya yanzu Sa'eed ya fara yi mata nisa Nan gaba tasan sai ta kamu da ciwon zuciya dan wasu abubuwan ba iya jurewa zatayi ba,

Gyaran murya baba alhaji yayi Yana kallon Leesa da ta tsaya qyam ta harder hannuwan ta a qirji tana binsu da wani wulaqantaccen kallo yace
"Amarya ta Dan Allah yi haquri ki zauna magana zamuyi da ku"

Turo Baki gaba tayi ta juya ta bashi qeya tana qunquni, Saida Nabeela ta taso ta lallabata sannan ta zauna a hakan ma tana musu warning idan suka Bata Mata lokaci tafiya zatayi abunta,

"Alhamdulillah Daman ance komai yayi farko zaiyi qarshe, gaba dayanmu min Shiga damuwa kuka min jigata da rashin Sarwa Amman gashi Bayan shekaru masu yawa har Mun fara cire tsammani Allah ya dawo Mana da su lafiya,

Abinda nake so daku yanzu tunda duk wasu qadarori namu zasu dawo hannun mu ku sasanta tsakanin ku, na yarda Sa'eed yayi laifi da ya samu Sarwa Kuma ya boye Mana Amman Allah ya riga ya tsara hakan zata faru tun farko, yanzu sai mu rungumi qaddara a dauki Haleesa a kaita wurin mahaifiyar ta, ita Kuma matar Sa'eed ta ci gaba da zama a dakin ta Allah ya sauqe ta lafiya"

Wuff Sa'ood ya miqe yace " wallahi ban yarda ba, dole a raba tsakanin Sa'eed da Salee ita ba matar shi bace, kowa shaida ne Akan tun tana jaririya aka bani ita na raini abuna saboda idan ta girma na aureta Amman tun ba'aje ko Ina ba Sa'eed yazo ya raba ni da ita yanzu Kuma yazo ya aureta, me yasa ko yaushe baku son yi min adalci ne?"

" Zauna Sa'ood wannan ba abun da za'ayi tashin hankali a kai bane ba ga 'yar uwarta ta ba sai ka aura tunda komi nasu iri daya Kuma anyi maka alqawari"

Nuna Haleesa yayi da yatsa yana yamutsa fuska yace
"Wannan Mai dogon goshi wawiyar 'yar fari me zanyi da ita? Ya zamo dole Sa'eed ya saki Saleeha ni ban damu da cikin jikinta ba idan ta aihu sai a bashi danshi Amman babu Wanda ya Isa ya canza alqawarin da mamanmu tayi min wahalar da nayi ba zai tashi a banza ba"

Jan dogon tsaki Leesa tayi tana faman harare_harare "Kai ance maka son naka akeyi me zanyi da 'dan fashi 'dan ta'adda? Bari ma kuji daga Nan gaba zan qara I'm not interested in staying with you, na riga na saba rayuwata ni kadai Ina dogaro da kaina wannan lokacin ma bani buqatar kowa Amman tunda ita Salee ta zabi zama daku shikkenan ni kunga tafiya ta" ta juya zata tafi da sauri Idris ya taro ta sai faman qwacewa take yi.

"Dan Allah Haleesa mahaifiyar mu, ki tausaya Mata Baki San cikin wani Hali take yanzu ba, dauki shekaru masu yawa a cikin mummunan yanayi ki taimaka kiyi haquri ki dawo gareta ba don mu ba please"

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now